Yadda aka gudanar da Gasar Pizza na Ƙasa da Ƙasa a Algiers babban birnin ƙasar Aljeriya, inda masu fafatawa 50 ke fafatawa domin fidda zaƙaƙurai guda uku.
Bugu da ƙari, Fiye da mutane 40 masu aiwatar da wannan sana’a ta Pizza daga ƙasashen Aljeriya, Libya, Tunisiya, Italiya, da Faransa suka shiga Gasar don gabatar da fasaharsu da kuma salo iri daban-daban wajen haɗa Pizzar.


A yayin da aka gayyato ƙwararrun alƙalai guda 7 masu lura da Gasar wadda sun kasance fitattu a duniya a ɓangaren dafe-dafe (Chefs).
Akan bai wa ƴan ukun farko da suka yi nasara kyautuka, sannan za su ci gajiyar horon mako guda a wani gidan cin abinci na alfarma a Italiya, baya ga samun damar shiga Gasar a matakin Duniya.


Saboda haka, wannan Gasar ta samu karɓuwa sosai musamman ga ƙwararrun masu dafe-dafe na Duniya. Haka nan, mutane masu haɗa kayayyakin da ake amfani da su wajen yin Pizza su na halarta domin baje-koli.


