Al'ada

Al’adar Yanke Yatsa na Ƙabilar Dani

Dani, ƙabila ce da ke tsakiyar tsaunukan Yammacin New Guinea a cikin ƙwarin Baliem Valley, Highland Papua, na Ƙasar Indonisiya.

Wani ɗanƙabilar Dani. |Hoto: Pulse

Kusan mutane 100,000 suke zaune a cikin kwarin Baliem, wadda ya ƙunshi wakilan ƙabilun Dani.

Wasu ƴan ƙabilar Dani, a yayin gudanar da bukukuwan al’ada. |Hoto: Pulse

Har ila yau, an san su da al’adu iri daban-daban ciki har da wadda ke da ban mamaki; Al’adar Yanke Yatsa.

Al’ummar ƙabilar Dani, su na shagalin bikin al’ada. |Hoto: Pulse

Yanke Yatsa, al’ada ce da aka saba yi a cikin ƙabilar Dani wadda suke yi don bayyana raɗaɗin baƙin ciki a yayin da aka rasa masoyi ko ɗan’uwa.

Wata Mata ƴar ƙabilar Dani |Hoto: Pulse

Wani daga cikin ahalin wannan dangi dole zai yanke Yatsa sannan a ƙone, ta zama toka don adana ta a wuri na musamman.

Wani hannu wadda aka yanke yatsunsa. |Hoto: Pulse

Bugu da ƙari, su na Yanke ɗaya ko fiye na yatsunsu a matsayin alamar baƙin ciki. Sun yi amannar cewar, yin hakan zai kawar da mugayen ruhohi da taimakawa ran mamaci ya samu sururi a Lahira.

Wata Bazawara wacce ta rasa mijinta, a yayin da ta yanke yatsunta saboda nuna alhini da tsantsar ƙauna. |Hoto: Pulse

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Al'ada

Bikin Guérewol na Ƙabilar Wodaabe a Jamhuriyar Nijar

Bikin Guérewol wata gasa ce ta al’adar neman aure da ake yi a kowace shekara tsakanin al’ummar Wodaabe Fula na
Al'ada

Shin Kayan Lefe Kyakkyawa ko Mummunar Al’ada Ce?

Abdulmutallib A. Abubakar malami a sashen nazarin aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri da ke jihar Barno kuma mai sharhi kan