Sarkin Daular Mali, Mansa Musa ya kasance mutum mafi ƙarfin arziki da aka taɓa samu a Duniya, wadatarsa ta ba shi damar bunƙasa Birnin Timbuktu.
Ya Yi Sarauta Tsakanin Shekarar 1313 zuwa 1337
An haifi Mansa Musa a shekara ta 1280 a garin Manden. Kodayake, ana yawan kiran shi da ‘Kankan Musa,’ amma ainihin sunansa ‘Kanku.’ Wannan sunan Mata ne da ya samo asali daga dangin mahaifiyarsa.
Wasu daga cikin manyan ƙabilun wancan lokacin sun fi danganta Yaro da ɓangaren Uwa, don haka, Maza ma suke ɗaukar sunan mahaifiyarsu.
A cikin shekarar 1313, bayan rasuwar yayansa Sarki Abu Bakr II, Musa ya zama Shugaban Daular Mali. A lokacin mulkinsa na tsawon shekaru da dama, ya yaɗa al’adun Musulunci a kewayen Ƙasar Mali, kuma Daular ta zama ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gaba a Duniya.
Mansu Musa, ya fito ne daga Gidan Sarauta na Keita, waɗanda suka yi mulkin Mali tsawon Ƙarni da dama.
Haka nan, ya kasance Sarki mai wadata wanda ya gina Daula mai ƙarfin faɗa-a-ji, kuma wadda ta bunƙasa. Bisa ga bayanan al’adar baka, kakansa Abu Bakr na farko, ƙani ne ga Sunjata Keita wanda ya kafa Daular Mali.
Sarautar Musa ta Haska Daular Mali a Duniya

Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: DW
A zamanin mulkin Musa, wataƙila Ƙasar Mali ce ta kasance mai samar da Zinariya mafi girma a Duniya, kuma ana ɗaukar Musa ɗaya daga mutane mafi arziki a tarihi. Ko dai ya ta kasance, masu sharhi na zamani irin su: Mujallar Time, sun kammala da cewar, babu ingantacciyar hanyar da za ta ƙayyade arzikin Musa. Amma kuma Mujallar Marca ta ce, gabaɗaya, ƙiyasin dukiyar za ta kai kusan Dala Biliyan 400.
A shekarar 1324, Mansa Musa ya tafi aikin Hajji a Makka. Ayarinsa ta ƙunshi mutum Dubu 60 da Bayi Dubu 12 da Dogarai da ke sanye da kayan ƙawa da Sanduna na Zinariya, da kuma masu kula da Dawaki da kayansu.
Wannan ƙasaitaccen rangadin ya sa ya zama sananne, musamman a Yammacin Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya. A cikin kowane Gari da ya yada zango, Musa ya kasance mai karamci sosai kuma ya yi ta ba da kyautar wani ɓangare na dukiyarsa – wanda babu shakka ya yi tasiri ga tattalin arzikin yankin, da kuma labarin mulkinsa.

Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: DW
Sarki Mansa Musa (Musa Keita) ya hau kan ragamar mulki a shekarar 1312 Miladiyya, bayan rasuwar Sarki Abu Bakr na biyu. Hawansa karagar mulki ke da wuya ya faɗaɗa iyakar Masarautarsa wacce ta faro tun daga gaɓar ruwan Gambiya, har yankin ƙasar Sudan, inda ya haɗa yankin Ƙasar Hausa da ke Najeriya da Ƙasar Nijar da Senegal, Burkina Faso, Gambia, Mali, Chad da Mauritania su suka haɗu suka bayar da Daular da Mansa Musa ke mulka.
Babban Birnin Mulki: Timbuktu Wanda ke Ƙasar Mali
Sarki Mansa Musa ya shimfiɗa mulki na ƙasaita, ya kuma faɗaɗa Birnin Timbuktu https://is.gd/ISvez0 ta yadda ya yi gogayya da sauran manyan biranen Duniya na wancan zamani.

Birnin Timbuktu a tsarin ginin Gargajiya, wadda ya samo asali daga ƙwararren magini Ishaq El Teudjin.
A shekarar 1324, Sarki Mansa Musa ya shirya tafiya zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke Farali, tafiyar da ta bar wa Duniya tarihi na ban mamaki.
Lokacin da tawagar Sarki Mansa Musa ta motsa daga Birnin Timbuktu zuwa garin Makka, ya tafi da Sojoji sama da 20,000, haka zalika bayin da za su yi hidima sun haura 500. Ya kuma ɗebi dukiya da zummar yin Hadaya a garuruwa masu tsarki na Makka da Madina, dukiyar da ko Sarakunan Daulolin Larabawa ba su taɓa mallakar irinta ba.
Kamar yadda malaman tarihi suka ambato, sun ce ya tafi da Raƙuma 20,000 da Dawaki 6,000 da manya-manyan mazubai cike da Zinariya da Azurfa, da Tufafi na alfarma da sauran nau’ukan dukiya duk domin bayar da kyauta ga mutanen Makka da Madina.

Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: DW
A lokacin wannan tafiya tasa, ya tafi da wata amaryarsa wacce yake matuƙar ƙauna, wacce aka tanadar mata Bayi da Kuyangi sama da 100 waɗanda aikinsu kawai yi ma ta hidima.
A yayin da tawagarsa ta ratsa Hamadar Arewacin Afirka https://is.gd/1GYvZv bayan tafiyar watanni, sai wannan amaryar tasa ta gaji da tafiya a cikin Sahara, ta yi fatan ina ma ta samu Dausayi mai Danshi da za ta huta. Wannan buƙata da ta nuna ya sa Sarki Mansa Musa ya umarci da a share Saharar a ƙirƙirar ma ta Dausayi (Lambu) da za ta huta.
A tarihin Duniya wannan shi ne lokaci na farko da aka taɓa samar da dausayi a cikin Sahara.
An ce, an yanka sama da Raƙuma 3,000, aka yi amfani da ruwan cikinsu aka samar da wani Dausayi mai tarin ni’ima da shuke-shuke masu ban sha’awa. A wannan Dausayin ne amaryar tasa ta samu damar hutawa har na wasu watanni kafin daga bisani tawagar ta sake motsawa.
Labarin wannan tawaga ta ratsa ko’ina a ƙasashen Yankin Magrib. Sarakuna da dama sun kaɗu sun kuma firgita da ƙarfi da kuma tarin dukiyar da suka gani ta Sarki Mansa Musa.

Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: DW
Lokacin da tawagar ta isa Ƙasar Misra, ya kiɗima Misrawa, domin ba su taɓa ganin mutum mai ƙarfin dukiya kamar Mansa Musa ba, ta yadda har ya kusan mayar da Misirawa bayinsa saboda tarin dukiyar da suka gani.
Labarin isowarsa Misira da irin dukiyar da yake ɗauke da ita ya watsu a kowane lungu da saƙo, wannan dalili ya sa mutane su ka yi ta turereniyar zuwa ganin wannan tawaga.
Malaman tarihi sun ce, Mansa Musa ya yi ta raba Hadaya (Kyauta) ga mabuƙata da Miskinai. Har ila yau, ya hidimtawa Malaman Misira na zamanin, ya bada Dukiya mai yawa wajen sake gina Masallatai da makarantu. Saboda kyautuka da ayyukan alheri da ya yi, ya sa aka samu hauhawar farashin kayayyaki a Ƙasar Misra.
Tawagar Mansa Musa ta tashi daga Misra ta nufi Hijaz (Makka) ta Gaɓar Ruwan Maliya. Tuni labarinsa da irin hidimar da ya yi wa mutanen Misra ta isa gare su. Wannan dalili ya sa ya samu kyakkyawar tarba daga mutanen Makka da Madina.

Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: DW
Wannan tarin Dukiya da ya taho da ita, sai ya tattara ta gaba ɗaya ya bayar da ita Hadaya ga Haramin Makka da na Madina. Haka nan, ya bi manyan gidajen Sharifai da na zuriyar Sahabbai ya yi musu hidima ta ban mamaki. An ce Allah ne kaɗai ya san iya adadin Zinariya da ya rabar.

Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: DW
Dawowarsa Daga Makka
Bayan dawowarsa daga Makka, Mansa Musa ya taho da malamai Larabawa, da ma’aikata da masu gine-gine. Daga cikin waɗanda suka tawo tare da shi har da masanin gine-gine Ishaq El Teudjin, wanda ya ɓullo da dabarun gine-gine ga Ƙasar Mali.
Ya tsara gine-gine masu yawa ga Sarkin Sarakuna, ciki har da; sabuwar Fada mai suna ‘Madagou,’ da Masallacin Gao, birni na biyu mafi girma a Mali, da kuma babban Masallacin Timbuktu, birni mafi girma a Cikin Daular. An sanya wa wannan Masallaci suna Djinguereber.


Shahararren inda El Teudjin ya gina shi ne, ɗakin Sarki a Babban Birnin Mali na Niani.

Yanzu haka, Niani ƙauye ne a Ƙasar Guinea. Ya na cikin Lardin Kankan, a Gabashin Ƙasar. |Hoto: Wikipedia
Sakamakon ɗimbin arzikin da ya mallaka, Kanku Musa ya gina wuraren Addini da na mulki da dama a shekarun 1325s. Daga cikinsu akwai; Masallatai, da Makaranta da kuma Masarauta a garuruwan Timbuktu da Gao.
Masallacin Sankore da ke Timbuktu ya kasance fasaharsa da ta fi fice. Ya ba da damar musayar al’adu tsakanin Ƙasar Mali da ƙasashen Larabawa.
Wasu ɗaliban Mali sun je Misra da Maroko don kammala karatunsu, yayin da wasu malaman Masar da Moroko suka je karatu a Sankore Madrasa. A wancan lokacin ya kasance Cibiyar Yaɗa Kyakkyawan Al’adun Musulinci a Yammacin Afirka.
Mansa Musa, ya rasu a shekara ta 1337 bayan ya yi shekaru 25 bisa Karagar Mulki. Ɗansa Maghan I ne ya gaje shi.
Madogara
Waɗanda suka yi hidima wajen haɗa wannan maƙala sun haɗa da; Muhammad Cisse, da Salahuddeen Muhammad, tallafin Jaridar Blueprint Manhaja, da Mujallar Time, da Marca, da kuma sashen Hausa na DW.