Akwai wasu kayayyaki da Annabi Muhammadu SAW, ya yi amfani da su a lokacin rayuwarsa da a yanzu haka suke wani Gidan Adana Kayan Tarihi a Ƙasar Turkiyya.
Domin jin yadda waɗannan kayayyaki suke, Turkiyya a yanzu maimakon birnin Madina na ƙasar Saudiyya inda Manzon Allah ya yi rayuwarsa, mun tuntuɓi Sheikh Ibrahim Daurawa, fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya kuma ƙwararre a fannin tarihi don jin yadda hakan ta kasance.
Malamin ya ce, abubuwan da ake jinginawa Manzon Allah waɗanda aka same su a Ƙasar Turkiyya sun samu ne a lokacin Sarki Abdulhamid II, a shekarar 1914.
Daular Usmaniyya ta kafu ne a shekara ta 1299, 27 ga watan Yuli, sannan ta ruguje a 29 ga watan Octoba shekara ta 1923, wato ta kwashe tsawon shekara 600 ke nan ta na gudana.
Wanda ya fara kafa ta kuwa shi ne Uthman na farko, wanda ake kiransa Attagul.
Wani Sarki a lokacin Yaƙin Duniya ya so ya kai farmaki Madina domin ya yi ta’addanci, don haka wannan Sarki ya sa aka tara Sojoji masu yawa aka tura su domin su je su tsare Madina, su kuma kwaso duk wani abu da ke da alaƙa da Manzon Allah domin ka da a maimaita ƙona Alkyabbar Manzon Allah da Mongul suka yi a Bagadaza.
Malamin ya ce, shi ya sa duk wani abu da ake jinginawa Manzon Allah sai aka kwashe su aka mayar da su Turkiyya domin samun kulawa ta musamman, da kuma kare su daga sharrin Kafirai.

Sahun takun Annabi Muhammad ke nan da aka nuna a wani Gidan Adana Kayan Tarihin Musulmai da ke Birnin Santambul na Turkiyya a Ranar 16 ga Nuwamban 2017. Gidan da ke Unguwar Sultanahmet na ƙunshe da kayayyakin tarihi na Turkawa da na Musulunci. Sannan akwai tarin kayan ƙere-ƙere, na Gilashi, da Duwatsu da kayan kwalliya, da kayan Ƙarafa na Yumɓu, da kuma manyan Katifu na Turai, waɗanda kayan tarihi ne da ba safai ake samunsu daga ɓangarorin Duniyar Musulunci ba.

Takubban Annabi Muhammad da kuma gidajensu, da fitattun maƙera na Zinariya na Daular Usmaniyya da suka yi wa wurin sanyawa, wannan hoton an ɗauke shi ne a Ranar 3 ga watan Yulin 2018 a Turkiyya.

Wannan wata Tasa ce, da aka yi imanin cewa Annabi Mohammed ya sha ruwa da ita, ta na ɗaya daga cikin abubuwan da aka bajekolinsu a Fadar Topkapi da ke Santambul.

Hajrul Aswad, ko Baƙin Dutse ke nan, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga Musulmin Duniya, an nuna shi a Fadar Tokpati a Ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018.

Mazubar ruwan rufin Ka’aba ke nan, wadda ita ma Ka’aba kamar yadda aka sani ta na da matuƙar muhimmanci ga al’ummar Musulmin Duniya, an nuna ta ne a Fadar Topkapi a Ranar 3 ga watan Yuli na shekarar 2018.
Gashin gemun Annabi Muhammad, da Hatiminsa da wasiƙunsa, da Takubban Annabi Muhammad da gidajensu, na cikin wasu wuraren ajiya na musamman da maƙeran Daular Usmaniyya suka samar, kuma ana nuna su ga ɗimbin masoya Annabi Muhammad na Duniya da mabiyansa, da kuma wasu sauran kayayyaki da ake alaƙantawa da shi.

Silin gashin gemun Annabi Mohammed ke nan, wanda ke da matuƙar tsarki ga al’ummar musulmi shi ma an nuna shi ne a Fadar Topkapi.