Turmin Tsakar Gida

Dr. Rachel Siu: Likitar Dabbobi Wacce ta Gayyaci Macijiya Bikin Aurenta

Rachel Siu, mai shekaru 26, da mijinta Eric, mai shekaru 31, sun gayyaci macizai da sauran Dabbobi zuwa bikin ɗaurin aurensu a Gidan Ajiyar Namun Daji (Zoo).

Ba’amirkiya Rachel da mijinta Eric na sha’awar Dabbobi matuƙa, har ma sun gayyaci wata Mesa mai suna “Lucy,” don ta halarci bikin aurensu.

Ma’auratan masu sha’awar dabbobi sun kasance mazauna Carrollton, Amurka, an kuma ɗaura auren a gidan Zoo na Fort Worth a Jihar Texas.

Rachel, wacce Likitar Dabbobi (Veterinary) ce, ta ce; “Na kasance ina son macizai kuma ina aiki da Dabbobi a kowace Rana a matsayin Likitan Dabbobi.”

Ta ƙara da cewar, “Na yi tunanin zai zama abin farin ciki don kawo Lucy zuwa wurin bikin saboda ta kasance na musamman a gare ni.”

Ta kuma ayyana cewa, “Ina so in nuna cewa, Lucy dabba ce mai kirki da sauƙin mu’amala. Kuma na nunawa mutane cewa, su daina yi wa dabbobi mummunar fahimta ba tare da sun mu’amalance su ba.”

Daga ƙarshe ta bayyana cewar, “Abokaina da dangi sun ƙaunaci hotunan, kuma sun ce ya dace da ni a matsayin Likitar Dabbobi.”

Bugu da ƙari, Dr. Rachel Siu ta na bayar da horaswa a makarantu da cibiyoyin domin nusar da al’umma muhimmanci dabbobi, da kusantarsu domin fahimtar ɗabi’u su domin ta yadda jin ƙai zai kai gare su.

Haka nan, Dr. Rachel Siu, a yanzu haka ta na tare da mijinta (Eric) da kuma ɗansu guda.

📷 Dr. Rachel Siu/News 24

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Turmin Tsakar Gida

Musaboni Hosono: Ɗanƙasar Japan Guda Ɗaya Tal da ya Tsira Daga Haɗarin Jirgirn Ruwan Titanic

Wanann shi ne Musaboni Hosono. Ɗan asalin Ƙasar Japan guda ɗaya tal da ya tsira daga haɗarin Jirgirn Ruwan Titanic
Turmin Tsakar Gida

Babbar Magana! An Naɗa Akuya a Matsayin Shugaban Gari

Wata al’umma a ƙauyen Nabankaha na Cote d’Ivoire, ta naɗa Akuya a matsayin shugaban garin. Bugu da ƙari, shi ne