Tsaunin Kajuru, wani katafaren wurin shaƙatawa ne, wadda aka gina a tsakanin shekarun 1981 zuwa 1989, a ƙauyen Kajuru da ke kudancin Jihar Kaduna, Najeriya.



Wani Bajamushe mai suna Gerhard Huebner, wadda ya zauna a Kaduna a shekarun 1980s ya gina shi.
Ginin ya na da tsarin salo na Gidan Sarauta, ya na kuma da tazarar kilomita 45 daga cikin birnin Kaduna, a kan wani Dutse da ke ƙauyen Kajuru (Ajure) a Jihar Kaduna.




An gina shi da Dutse mai kauri na mita ɗaya a cikin kyakkyawan salon zamani na ginin ‘Romanesque.’ An kuma ƙawata shi da Falo mai salo na “Baronial,” akwai ɗakunan kwana wadda ke da ikon ɗaukar mutane 150, a hawa na uku.






Har ila yau, an tsara ginin da Hasumiyai waɗanda suka ƙara fito da kyawun ginin, sannan akwai furanni masu ban sha’awa, daga tsakiyar farfajiyar wurin kuwa, tafki ne aka tanada domin ninƙaya



Yawancin lokaci ana kwatanta ginin a matsayin sigar Afirka ta “Bavarian Castle” a cikin babban salon ginin Romanesque na ƙarni na 19.
Masu Yawon Buɗe Ido daga sassa daban-daban a faɗin Duniya kan ziyarci wurin domin kashe ƙwarƙwatan idanunsu.

