Turmin Tsakar Gida

Babbar Magana! An Naɗa Akuya a Matsayin Shugaban Gari

Wata al’umma a ƙauyen Nabankaha na Cote d’Ivoire, ta naɗa Akuya a matsayin shugaban garin.

Bugu da ƙari, shi ne sarkin ƙauyen Nabankaha da ke yankin Tshilogo. Wannan Bunsuru ya yi mulki sama da shekaru 15 a wannan ƙauyen.

Mazauna garin sun ce har yanzu su na jin daɗin rayuwa ƙarƙashin ikon wannan Bunsuru da ke a matsayin hakimin garinsu.

Sunan sarautar Sarki bunsurun ‘Bakoroni mai Daraja ta ɗaya,’ kuma wanda ke mulki yanzu ya shekara aƙalla 15 a kan karaga.

Ƙafar yaɗa labarai ta RTI-2 mallakar Gwamnatin Turkiyya, ta ruwaito cewar, al’ummar ƙauyen sun yi matuƙar farin ciki da salon jagorancin Bunsurun.

Har ila yau, wasu mazauna garin sun yi imanin cewa Bunsurun ya na kawo sa’a ga al’ummarsu.

Duk da cewa ba ɗan’Adam ba ne, al’ummar ƙabilar Senoufo da ke kauyen sun ce, su na ɗaukar shugaban nasu a matsayin ɗan’Adam, kuma su na ɗaukarsa da matuƙar daraja.

“Idan da zai rasu, dole mu sake nemo wani daga cikin ƴaƴansa mu naɗa shi a shugabanmu,” kuma babu wani ɗan ƙauyen da ke iya cutar da shi.

Mutanen kauyen sun yi amannar cewa Bunsurun da ke jagorantarsu shi ne mai ba su kariya, da kuma gargajiyarsu, wanda a cewarsu, shi ne amfanin sarkin ƙabila.

Don haka a matsayin shugabansu, babu mai korarsa, ballantana hantararsa, duk abin da zai yi.

Wani ɗan ƙabilar, Emmanuel, Ouattara, ya ce, hasalima, “Muna alfahari da kasancewarsa a cikin wannan al’umma ta Nabahanka.”

Sarkin nasu Bunsuru na yawata tare da watayawa ko’ina a wannan Masarauta ba tare da wani mutum ko wani abu ya cutar da shi ba.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Turmin Tsakar Gida

Musaboni Hosono: Ɗanƙasar Japan Guda Ɗaya Tal da ya Tsira Daga Haɗarin Jirgirn Ruwan Titanic

Wanann shi ne Musaboni Hosono. Ɗan asalin Ƙasar Japan guda ɗaya tal da ya tsira daga haɗarin Jirgirn Ruwan Titanic
Turmin Tsakar Gida

Tarrare: Mutumin Da Ya Kasa Daina Cin Abinci, Saboda Ba Ya Ƙoshi

A ƙarshen shekarun 1700s, akwai wani mutum a ƙasar Faransa wanda ke fama da yunwa marar iyaka kuma ya kasa