Tsaunin Obudu, (wadda a da ake kira da Obudu Cattle Ranch), wani kwari ne a rafin Oshie na tsaunukan Sankwala, a jihar Kurus Riba (Cross Riba) da ke Kudu maso gabashin Najeriya.
Kwarin ya kasance a yankin tsaunukan Sankwala da Obudu na Ƙananan Hukumomin Obanliku da Obudu, kusa da kan iyakar Jamhuriyar Kamaru (Cameroon) a yankin Arewa maso gabashin jihar.

Obudu Mountain Resort, Ya kasance ƙarƙashin gwamnatin jihar Kurus Riba, wadda take kula da kuma alkinta shi.
Bugu da ƙari, yankin ya mamaye fili mai faɗin murabba’in mil 40 (kilomita 110), kuma ya kai kusan taku 5,200 (mita 1,584), sama da matakin teku. Har ila yau, tsaunin na da wani babban dutse a bisansa, kuma ƙololuwarsa ya kai tsayin kusan mita 1,716 (taku 5,630) sama da matakin teku.

Har wa yau, yanayin da ke tsaunin Obudu ya kasance na hunturu madaidaici. Saboda haka, yankin ya na fuskantar yanayi mai tsaka-tsaki, tare da yanayin zafi tsakanin 26 ° C (78.8 ° F), da 32 ° C (89.6 ° F), a lokacin rani daga watan Nuwamba zuwa Janairu.

Lokacin damina kuwa, a watan Yuni zuwa Satumba ne, yayin da yanayin sanyi yake kankama na tsawon watanni 3.9, daga Yuni zuwa Oktoba. Watau; Wata mafi sanyi na shekara a Obudu shi ne Disamba, a matsakaicin 67°F, kuma sama da 85°F.
Yankin ya na samun ruwan sama mai yawa a lokacin damina. Akan samu ruwan sama mai ƙarfin milimita 4,200 a tsakanin Afrilu da Nuwamba.

Kamar yadda binciken masana sararin samaniya (Meteorologists) ya bayyana dalilin da ke haifar da ruwan sama mai yawa a tsaunin shi ne; Gajimare da ke gangamowa kudancin Najeriya daga Tekun Atlantika, danshinsu na sauka ne bisa tsaunin Obudu, wadda sakamakon sanyin ruwan sama mai yalwa ke samuwa.

McCaughley, wani makiyayi ɗanƙasar Scotland wadda ya yi sansani a bisa dutsen Oshie ya zauna a tsaunin na tsawon wata guda.
Haka nan, ya fara binciken tsaunin Sankwala a shekara ta 1949, kafin daga bisani ya tafi ya dawo tare da Mr. Hugh Jones, da Crawfeild (wasu makiyaya), a shekarar 1951, inda suka yada zango tare da aiwatar da kiwon dabbobi, wadda hakan ya bada damar haɓakar wurin.

A baya-bayan nan dai, an samu kwararowar masu yawon buɗe ido daga Najeriya da ma na ƙasashen waje saboda bunƙasa wuraren yawon buɗe ido da gwamnatin jihar (Kurus Riba) ta yi, lamarin da ya mayar da tsaunin zama sanannen wurin hutu da wuraren shaƙatawa a Najeriya.



Akwai tashar (airstrip) motocin taƙaita zirga-zirga (Cable Cars) wadda ke tsakanin ƙauyen Obudu da wurin shaƙatawar saboda sadarwa tsakanin zirga-zirga daga sassa zuwa sassa na tsaunin.



Bugu da ƙari, akwai ɓangarori daban-daban wadda ya haɗar da ɗakunan taro, ɗakunan kwana, wajen ciyayya da shaye-shaye, tafkuna linƙaya, farfajiyar noma da kiwo, da sauran ababen ɗebe kewa na ƙawa da nishaɗi.




Jihar Kurus Riba ta na da zaman lafiya da kwanciyar hankali idan aka kwatanta da sauran yankuna a tarayyar Najeriya, wadda hakan ta sa al’umma ke ziyartar tsaunin (Obudu Mountain Resort) daga sassa daban-daban na duniya.



📷 Obudu Mountain Resort