Daga: Muhammad da Nazir Adam Ibrahim
Majalisar Gudanarwar Jami’ar Bayero da ke Kano, ta amince da ɗaga darajar Dr. Maryam Mansur Yola, ta Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, da ke Jami’ar zuwa matsayin Farfesar Magungunan Gargajiya da Al’adu, kamar yadda wata sanarwa da Jami’ar ta fitar a ranar Juma’a 27 ga Disamba, 2024 ta bayyana.
Farfesa Maryam Yola, Ƴar asalin Ƙaramar Hukumar Kano Municipal, ita ce Mace ta farko a tarihi da ta zama Farfesa kan Magungunan Gargajiya da al’adun Hausa, kuma Malama ce da ke koyar da kwasa-kwasan Al’adun Bahaushe da ta koyar da ɗimbin ɗalibai a matakan ilimin daban-daban a ciki da wajen Najeriya.
Baya ga Takardu da Maƙalu masu tarin yawa da ta gabatar kan magungunan Gargajiya a Jami’o’i da makarantu da wuraren tarukan ilimi daban-daban a ciki da wajen Najeriya, ta duba aikin ɗalibai masu tarin yawa a matakin Digiri na ɗaya da na biyu da na uku a Jami’ar Bayero da wasu Jami’o’i a Najeriya.
Farfesa Yola, ta kuma riƙe muƙamai da dama a matakin gwamnatin Tarayya da Jiha da wasu Ƙungiyoyin Siyasa da Jami’a da Ƙungiyoyin ci gaban al’umma.