A Ranar Asabar, 30 ga Watan Disamba na shekarar 2006 aka kashe tsohon Shugaban Ƙasar Iraq Saddam Hussein ta hanyar rataya.
Bayan da aka same shi da laifin cin zarafin Bil’adama, an rataye Saddam da Asuba a Ranar 30 ga Disambar, 2006.
Al-Maliki shi ne Firaministan Iraq daga watan Mayun 2006 zuwa Satumba 2014, kuma shi ne jami’in da ya sanya hannu kan hukuncin kisan Saddam Hussein.
Da misalin ƙarfe shida da minti biyar na Safiyar Ranar 30 ga wata (Agogon Bagadaza), an aiwatar da hukuncin kisa kan Saddam Hussein, tsohon shugaban ƙasar Iraq ta hanyar rataya a birnin Bagadaza.
Yayin da manema labarai suka kai ziyara ga Mowaffaq al-Rubaie, mai ba da shawara kan harkokin tsaron Ƙasar Iraq don jinta bakinsa, sai ya ce, bisa amincewar da aka yi musu, shi da wasu jami’an Ƙasar Iraq da wani lauyan Saddam sun sami damar kallon yadda aka kashe Saddam a wurin da aka aiwatar da hukuncin kisa a kan Saddam. An kuma aiwatar da hukuncin kisa kan Saddam ne ta hanyar rataya yadda ya kamata.
A Ranar biyar ga watan Nuwambar 2006, Babbar Kotun Ƙasar Iraq ta shelanta cewa, ta yanke wa Saddam hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifinsa na cin zarafin ɗan’adam a kisan mutanen ƙauyen Dujail 143.



Bayan haka, Saddam ya ɗaukaka ƙara ga Kotun . A Ranar 26 ga watan nan, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Ƙasar ta shelanta cewa, ba za ta canja hukuncin kisan da aka yanke wa Saddam ta hanyar rataya ba.
Gidan Talabijin na Iraq ya nuna hoton Bidiyo na rataye Saddam, inda aka ga wasu mutane da dama da suka rufe fuskokinsu, sun taho da Saddam cikin Sarƙa zuwa dandalin da aka rataye shi ɗin. daga nan aka ɗaura masa igiya ga Wuya.
An ga alamun kwanciyar hankali a fuskar Saddam, wanda ya ƙi yarda a rufe masa fuska da Ƙyalle, kafin rataye shi.

Saddam Hussaini, lokacin da ake aiwatar da hukuncin kisa domin tabbatar da umarnin Kotu a kansa, ta hanyar rataya.
Daga baya an ga hotunan Bidiyo na gawar Saddam cikin farin likafani a Gidan Talabijin na Iraq. An ga kansa, wanda ba ya rufe a cikin likfanin, a karkace (alamar wuyarsa ta karye).
An kashe Saddam Hussein a wata tsohuwar Hedikwatar Hukumar Leƙen Asirin Soja da ke wata unguwar ƴan mazhabin Shi’a ta Bagadaza mai suna ‘Kazimayah.’
Bayan da aka aiwatar da hukuncin kisa a kan Saddam, Shugaban Ƙasar Amurka Bush ya bayar da sanarwa cewa, aiwatar da hukuncin kisa a kan Saddam wani al’amari ne mai muhimmanci ga hanyar da ake bi wajen aiwatar da Dimokraɗiyya a Ƙasar Iraki. Amma ya yi kashedi cewa, ba za a kawo karshen aikace-aikacen nuna ƙarfin tuwo da ake yi a Ƙasar Iraq ba.
Kasar Birtaniya ita ma ta fitar da sanarwa a kan al’amarin, haka wasu Ƙasashen Duniya.