Daga: Muhammad Cisse da Salahuddeen Muhammad
Shade Thomas-Fahm, cikakkeken sunanta Victoria Omórọ́níkɛ Àdùkẹ́ Fọlashadé Thomas, ƙwararriyar mai zanen Kayan Ado ce ta Najeriya. Ita ce mace ta farko da ta fara yin kayan kwalliyar zamani a Najeriya. Kuma ita ce ta farko da ta fara buɗe Kantin Sayar da Kayan Kwalliya a Najeriya.
A shekara ta 1960, Shade ta kasance mace ta farko a Najeriya da ta mallaki wani Kantin Sayar da Kaya, ta hanyar amfani da kayan Gargajiya na Afirka tare da ƙirƙiro salo da dama.
Kantin nata, ya kasance abin alfahari ga al’ummar Legas da Najeriya bayan mulkin mallaka.

Shade Thomas, ta na tsaye cikin murmushi, ta dafa wani aikinta da ta kammala.
Yawancin abubuwan da ta ƙirƙiro sun haɗa da: Boubou, da Agbada (Babbar Riga), da Ankara, da Aso-Oke, da Riguna, da Buje na mata, da Takalmi mai ƙwanƙwasa, da Takunkumin rufe Fuska (Face Mask), da sauran sutura da kayan kwalliya.
An haifi Thomas-Fahm, a Ranar 22 ga watan Satumba, a shekara ta 1933, ga dangin Bankole Ayorinde Thomas da Elizabeth Olaniwun Thomas.
Ta halarci Makarantar St. Peter, Faaji, Baptist Girls’ School Araromi, daga baya ta halarci Makarantar Mata ta New Era, duk a Jihar Legas, da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Asali ta tafi zuwa Ingila a cikin 1953 don samun horo a kan Aikin Jinya, Shade Thomas-Fahm ta canja fannin karatu, inda ta yi karatun a ɓangaren Fasaha (Artist) a St Martin’s School of Art (yanzu Central Saint Martins) a London.
Haka nan, ta dawo gida Legas a shekarar 1960, shekarar da Najeriya ta samu Ƴancin Kai, kuma cikin sauri ta kafa nata wajen sayar da kaya (Boutique) mai suna: ‘Maison Shade.’
Da farko dai, ta sha wahala wajen shawo kan ƴan Najeriya su sayi Yadudduka da Zane na gida, domin mutane su na ganin na al’adun Birtaniya sun fi kyau.
Shade Thomas-Fahm, ta rike Kambu mai ban mamaki na zama, mai zanen kayan ado ta farko a Najeriya. A farkon shekarun 1960, ta tsunduma cikin harkar Zane-zane, inda ta ƙaddamar da sana’arta a lokacin da kayan Najeriya ke kan gaba wajen ƙarko da nagarta. Wannan ƙoƙarin nata, ya buɗe hanya ga masu ƙirƙira waɗanda suka biyo bayanta.

Shade Thomas-Fahm, a ofishinta.
Ƴar Kasuwa mai Hangen Nesa
Shade Thomas-Fahm, ba kawai mai Zane ba ce; ta kasance ƴar kasuwa mai hangen nesa. Ta kafa laƙabin salonta “Shade Styles” a cikin shekarun 1960s, alamar da ta sami karɓuwa cikin sauri kuma ta zama daidai da salo, da ƙima. Ƙirarta ta haɗa da Yadudduka na al’adun Najeriya tare da kayan ado na zamani, sun kuma kasance masu kyau da jan hankali.
Tasirinta a Duniya
Zane-zanen Shade Thomas-Fahm sun wuce cikin Ƙasa Najeriya. Ta kasance ba kawai alamar ƙasa ba amma mai tasiri a Duniya.
An bajekolin abubuwan da ta ƙirƙira a Duniya, wanda ta gabatar ga masu hannu da shuni, da nau’ikan Kaset iri-iri na kayan adon Najeriya.




Zakaran Yaduddukan Najeriya
Ɗaya daga cikin aikin Shade Thomas-Fahm shi ne sadaukar da kai ga masana’antar Najeriya. Ta jajirce wajen yin amfani da masaƙun da ake samar wa a cikin gida, inda ta ɗaukaka su zuwa matakin Duniya.

Shade Thomas ta na aikin kammala wata sutura.
Kyawawan zanenta sun haɗa da, kayan masaƙun Gargajiya na Najeriya kamar: Aso Oke da Ankara, tare da haɗa su da salon zamani.
Kyauta da Yabo
Gudunmowar Shade Thomas-Fahm ga Duniyar Kayan Kwalliya ba ta yi ƙasa a guiwa ba. Ta samu kyautuka da yabo da dama a duk tsawon rayuwarta, ciki har da karramawa daga Cibiyar Nazarin Zamantakewa da Tattalin Arziki ta Najeriya, da Ƙungiyar Mata ta Najeriya, da sauransu.
An yi bikin tasirinta a Gidan Tarihi na Victoria da Albert (V&A) na London a cikin 2022.

Wasu daga cikin ababe tare da bayanai, da aka yi bajekolinsu.
Gado
Shade Thomas-Fahm, ta na ci gaba da zaburar da sabbin tsari na masu Zanen Kaya da masu sha’awar sabbin salo.

Shade Thomas, a babban kantinta da ke samar da sabbin salon zamani.
Sabuwar hanyarta ta salon kwalliya, jajircewarta ga masaƙun Najeriya, da sadaukarwarta ta yau da kullum ga sana’arta sun kasance ababen birgewa da alfahari.
Ta nuna cewa, da haziƙanci, da ƙwazo, mutum ɗaya zai iya barin gado mai ɗorewa.
Thomas-Fahm ta rinjayi yawancin mutanen zamaninta, tun daga shekarun 70s zuwa yau. Wasu daga cikinsu sun haɗa da: Abah Folawiyo, Betti O, Folorunsho Alakija, da Nike Okundaye, waɗanda duk sun yi tasiri sosai a kan salon Najeriya.

Shade Thomas, a yayin da take sanya ido kan ayyukan ma’aikatanta, da suke aiwatarwa.
Ta kasance Shugabar Ƙungiyar Rotary Club na Victoria Island daga 2009 zuwa 2010.

Shade Thomas, cikin ado na kayan gargajiyar Ƙabilar Yarbawa.
A yanzu haka, ta na nan a raye da shekaru 91 a Duniya.
