Daga: Khalid Idris Doya
A ranar Asabar da ta gabata (28/12/2024), an gudanar da babban bikin bajekolin al’adun gargajiya a Masarautar Kaltungo, a Jihar Gombe, inda dubban mutane suka halarta daga cikin Jihar da wajenta.
Bikin ana gudanarwa ne a duk ƙarshen shekara a Masarautar Kaltungo, da ke Jihar Gombe, Arewa maso Gabashin Najeriya.





Shi dai wannan Biki, ya na da muhimmanci, yayin da yake bayar da damar bajekolin al’adu da fasahohi iri daban-daban.


Haka nan, a yayin taron, ana waƙe-waƙe, da kaɗe-kaɗe, da raye-raye, da kuma gabatar da al’adun gargajiya, ciki har da irin Abincin gargajiya da aka gada tun kaka-da-kanni a Masarautar Kaltungo, da sauran Masarautun maƙwabta.



Taron na bana, ya gudana a filin wasanni na tunawa da Obasanjo da ke Kaltungo, inda Manyan Baƙi da Sarakunan Gargajiya daga yankunan Arewa suka halarta.


Haka kuma, tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Farfesa Jerry Gana, ya gabatar da jawabi, yayin da Mr. Meso C. Dickson ya kasance Babban Baƙon taron.

Prof. Jerry Gana, ya na gabatar da jawabi.
Daga ƙarshe, Mai Kaltungo, Injiniya. Sale Muhammad Umar OON, ya gode wa Sarakunan gargajiya da sauran al’umma bisa halarta da kuma amsa gayyatarsa.

Mai Kaltungo, Engr. Sale Muhammad Umar OON, a yayin da yake gabatar da jawabi.
Ya kuma bayyana cewar, ana shirya wannan taron ne domin tallafawa ci gaban al’adu, da kuma ƙarfafa zaman lafiya da ƙaunar juna tsakanin mazauna Masarautar da sauran maƙwabtanta.