Tarihi

Wanne Fir’auna ne ya yi Rayuwa da Annabi Musa?

Daga: Wael Gamal (BBC News Arabic)

Labarin asalin mutanen Masar da kuma tahirinsu ya yi ƙasa ba a jinsa har sai lokacin da aka samu ɓullar Yahudawan gargajiya da ke zaune a Ƙasar Masar, waɗanda aka ambata a littafin Injila, babin ficewar Banu Isra’ila daga Masar, da kuma wasu Ayoyin Al-kur’ani mai girma.

Littattafan addini na baya su ma ba su ambato sunan wannan “Fir’aunan” ba, wanda ya mulki Masar kuma ya yi rayuwa da Annabi Musa Alaihissalam.

Wannan ya janyo wasu malamai da ke da sha’awar bibiyar tarihin mutanen Masar tattara duka bayanan da tarihi ya tanada domin warware dambarwar sanin Fir’aunan da kuma gano shaidun sanin da za su warware taƙaddamar da ke tsakaninsu.

Gawar sarki Ramesses II, (c. 1297-1213 BC).

A 1976, aka kai gawar Sarki Ramses na biyu Filin Jirgin Bourget da ke Paris babban birnin Faransa, a wani Jirgin Sojin Faransa aka kai Gidan Tarihi na Breguet.

An yi wani taron biki akan gawar, wanda tawagar Shugaban Faransa na lokacin da Shugaban sojojinsu da wakilin Masar a Faransa da sauran mutane suka halarta.

An yi kaɗe-kaɗen Soji gabanin a ajiye gawar a Gidan Tarihi, da ke tsakiyar babban birnin Ƙasar, a wani shiri da ake yi na killace gawar da dawo da ita kan ganiyarta da wasu masana kimiyyar Faransa za su yi saboda cutukan da ake tsoron zai shafe su.

Marigayi Shugaban Ƙasar Masar Mohamed Anwar Sadat, lokacin da yake leƙa gawar Sarki Ramses na biyu.

Cikin watanni bakwai na lokacin daga 26 ga watan Satumbar 1976 zuwa 10 ga watan Mayun 1977 birnin Paris ya riƙa karɓar manyan ɓaki “kamar yadda fitacciyar masaniyar kimiyyar nan Madame Christiane de Roche Noblecourt ta bayyana a littafinta na “Ramsey na biyu.

Labarin ya ƙara da cewa an ware wani dogon ɗaki domin gawar ta fir’auna kawai.

Domin gane ƙwayoyin cutar da suka shafi gawar Masaraucin, sannan a samar da wani tsari da za a kiyaye gawar, shugaban Gidan Tarihin ya samar da masu taimaka masa kimanin 120, wadanda duk suka yi alƙawarin za su yi aikin kyauta, cikin har da masu bincike masana kimiyya 63 a mabambantan fannoni.”

Me ya sa aka kai Gawar Ramses na Biyu Birnin Paris?

Madame Alice Saunier-Cité, tare da tawagar shugaban Faransa na lokacin Valéry Giscard d’Estaing, ta na gabatar da bayani yayin bikin gawar ta Fir’auna ko kuma Sarki Ramesses na biyu a “Bourges” da ke Rukunin Gidajen Soji tare da fitacciyar Madame Christiane de Roche Noblecourt daga hagu a tsaye.

Akwai manufofi uku cikin aika Gawar Sarki Ramses na biyu zuwa birnin Paris. Na farko a magance wata cuta da ta kama Ƙafar Gawar, da Dunduniyarta da Kafaɗarta ta dama da ƙasan Cibiyar Gawar.

Na biyu kuma a koyi wani ɓoyayyan sirri na yadda ake ajiye gawarwakin shugabannin Masar, sannan a gano yanayin da Gawar take a yanzu, sannan a gano da waɗanne irin sinadarai ake iya ɓoye gawarwakin.

Na uku kuma shi ne yunƙurin gano musabbabin mutuwar sarkin: Shin mutuwa ce ta gaskiya saboda tsufa ko kuma mutuwa ce dalilin sarƙewar numfashi saboda nutsewa da ya yi a ruwa?

Dakarun tsaron Faransa yayin bikin tarbar gawar Sarki Ramses na biyu a Paris.

Masana kimiyyar na aikin gano ƙwayoyin halitta na ciki da wajen gawar, kamar Ɓargo da Gashi da Ƙirji da kuma gefen haƙarƙarin gawar, sannan a yi wasu gwaje-gwaje masu yawa kan gawar.

Gwamnatin Faransa ta samar da wani Ɗakin Gwaji da aka cika da kayan aikin na zamani a gidan tarihin domin nazari kan gawar Sarki Ramses na biyu.

Tawagar na nazari kan duka wasu sassan gawar, ciki da waje, Ƙwarangwal ɗin gawar da sauran ƙasusuwanta, ta hanyar ɗaukar hotonta sannan suka raba gawar zuwa kashi shida da za su yi nazari a kai.

Raɗaɗi da Ɓacin Rai Kan Sarki Ramses II

Hoton gawar lokacin da za a duba yadda za a farfaɗo da jikin gawarsa a Paris.

Wani bincike kan ƙwayoyin cutuka da aka yi a ɓangaren Ƙafa da Dunduniyar gawar da kuma Kafaɗarta ta dama, ya nuna wasu ƙwayoyin halitta sun kama gawar saboda sauyin da aka samu na yanayi tun lokacin da aka gano gawar a Deir el-Bahari – Wanda masanin kimiyya Faransa Gaston Maspero ya gano a 1881, sannan kuma aka warware naɗin da aka yi wa gawar a ranar 1 ga watan Janairun 1886.

Binciken masana kimiyyar ya nuna yadda ƙashin sama da ƙasan haɓa ke murmushewa sakamakon taruwar ruwa a wajen. Hoton masana kimiyya ya nuna yadda aka samu zaman ruwa na zama da shekaru a ɓangaren haƙora.

Sai dai binciken bai nuna an taɓa yi wa sarkin aikin haƙori ba lokacin ya na raye.

Bincike ya nuna kumburi a wajen haƙarƙarin gawar da bayan hannunta, jijiyoyin cinya da ƙafa, ƙashin ƙugun gawar duka ya lalace ga kuma murmushewar gashin kai da yake fama da ita.

Kumburin da aka gano bayan mutuwarsa an ce ya samo asali ne shekaru gabanin ya mutu a ƙarshen shekarun rayuwarsa.

Duk waɗannan na nuna cewa lafiyar fir’aunan ta taɓarɓare, inda ya riƙa fama da cutar sanyin ƙashi a shekaru ashirin na ƙarshen rayuwarsa, kamar yadda nazarin Nabelcore ya nuna.

Fir’aunan da ya fi Kowanne a Tarihin Masar

Sarki Ramses na biyu ana masa kallon fir’auna mafi ɗaukaka a tarihin Masar, kuma ɗaya daga cikin mafiya ɗaukaka tsakanin sarakunan Duniya.

Ya na ɗaya daga cikin sarakuna ƙalilan da suka yi mulkin dogon zamani, inda ake cewa ya kai shekaru 67 ya na jagoranci.

Ya na da ƴaƴa da dama kimanin 52 Maza ne 32 kuma mata ne, kuma shi ne mijin fitacciyar macen nan Sarauniya Nefertari.

Ya sa mutane sun gina mutum-mutumi da hannu a lokacin mulkinsa masu nauyin ton dubu, yanzu su na nan a wajen bautar Ramesseum bayan faɗuwar da suka yi a baya saboda girgizar ƙasa.

Majami’ar Abu Simble da Sarki Ramses na biyu ya gina a nesa da kudancin Masar.

Sarki Ramses na biyu ya ɗare kujerar iko ne bayan mutuwar mahaifinsa, Sarki Seti na ɗaya. Wasu rubutu da aka gani a majami’ar mahaifinsa a Abydos sun nuna Sarki Seti na ɗaya ya bai wa ɗansa Sarki Ramses na biyu iko mai yawa tun ya na kan mulki.

Shin Ramses na biyu shi ne Fir’aunan da aka Faɗa a Littafin Injila da Al-Ƙur’ani?

Sarki Ramses na biyu shi ne sarki guda da ya bar bajintarsa a ko’ina cikin Masar.

Malaman tarihin da ke bibiyar tarihin Masar sun ta bayyana mabambantan ra’ayi kan wannan batu.

Wasu daga cikinsu, ba tare da kafa hujja da wata shaida ta masana kufai ko tarihi ba, sun yi amannar cewa banu Isra’ila wadda aka ambata a cikin ayoyin Injila da kuma Alƙur’ani ta faru ne a zamanin sarakunan Huksus waɗanda suka mulki Masar.

Wasu ra’ayoyin kuma sun ce, sun rayu ne yayin Daular Masar ta 18, kamar yadda malaman tarihin Masar suka bayyana, musamman lokacin sarki Thutmose na uku.

Wasu sun ce, an yi Banu Isra’ila lokacin Sarki Amenhotep na biyu. Yayin da ra’ayi na huɗu suka ce sun yi amannar ya faru ne lokacin Sarki Amenhotep na uku.

Wasu masu tarihin sun wuce gaba inda suka ce ƙissar banu Isra’ila ta faru ne bayan mutuwar Sarki Amanhoteo na huɗu “Akhenaten,” amma ra’ayin da ya fi zama mafi karɓuwa a tsakanin mutane shi ne labarin Banu Isra’ila ya faru ne lokacin Sarki Ramses na biyu, kuma shi ne ra’ayin da masu shirya fim na duniya da sauran marubuta suka fi nunawa, irin shi aka nuna a shahararren fim ɗin nan “The Ten Commandments,” wanda aka shirya a 1956 wanda Cecil B. Demille ya ba da umarni, a cikin fim ɗin akwai ɗan Amurkan nan Charlotte Heston (a matsayin Annabi Musa) da kuma Yul Brynner (a matsayin Fir’auna).

Yul Brynner a matsayin Sarki Ramesses na biyu a 1956 a fim ɗin “The Ten Commandments.”

Wata marubuciya Noblecore ta ce, “Ko shakka babu zai fi dacewa a ce wannan Kissa ta faru ne tsakanin mulkin Fir’aunoni tsakanin shekara ta 10 zuwa ta 18, kamar yadda bincikenta ya nuna.

“Saboda babu wasu takardun shaida daga Masar da suka yi nuni kan shekarun da lamarin ya faru.

“Idan har muka dage sai mun fito da matsalolin Kissar domin mu bayyana lokacin da lamarin ya faru ba za mu iya ba, saboda akwai abubuwan da tarihi bai bayyana ba.

Sunan Musa (yana nufin haihuwa) tabbas asalinsa na Misrawa ne, kuma ya yi daidai da alamun gaɓa ta biyu da ta uku ta sunan Ramesses.”

Malamar nan ta tarihi ta Faransa ta ware wata babu guda na gudun hijirar Banu Isra’ila aka bugata a littafin da Nobelcore ta wallafa, inda suka ce Ƙissar ta faru a ƙarnin mulkinsu na 18 kafin haihuwar Annabi Isa.

Ta na cewa: “Musa ya samu kariya ta musamman daga Fir’auna, kuma Sarki Horemheb wanda rikicin Banu Isra’ila ya dabaibaye.

Lokacin da Musa ya kammala karatunsa sai ya koma cikin danginsa.

A wannan lokacin Sarki Seti na ɗaya ya gina wata madatsar ruwa a Delta, sannan ya gina fadarsa a Qantir wadda ta zama mazaunin Ramses na biyu.

Hoton zanen da ke nuna dakarun Fir’auna na nutsewa a ruwa lokacin hijirar Banu Isra’ila.

Musa ya cewa, Fira’auna ya zo su yi tafiya ta tsawon kwana uku a cikin sahara a matsayin sadaukarwa. Fir’auna ya ƙi amsa kiran sai rikici ya ɓarke.

Tsaba da Ƙasa

Wani ƙaton zanen Sarki Ramses na biyu a jikin bangon majami’ar Abu Simbel da ke Kudancin Masar.

Wani bincikenta Nobelcore ta tattauna kan wani abu da aka gano ya kuma ja hankalin wasu mutane, wanda gawar Ramesses na biyu an samu wata shaida jikinta da za ta taimaka wajen tabbatar da abin da masana tarihi suka yi hasashe cewa, ajiye gawar na tsawon lokaci ya faru ne a yankin arewacin babban birnin.

Ta ce “Mun san cewa an alkince gawar Ramesses na biyu ne a Arewacin babban birnin Masar. Ɓurɓushin ƙasar da aka samu mai kama da taɓo ta tabbatar mana da bayanan da muka tattara, wadda ta yi daidai da inda aka naɗe shi yankin Delta da ke nesa da kogin Nilu.

Ana iya ganin fuskar gawar Fir’auna da wani ɓurɓushi na gashinsa.

A cikin wani rahotonta kan tsabar ƙasa da aka gani kan gawar, wanda ta yi wa suna da “Gawar Ramses na biyu,” Yar ƙasar Farasa Josette Tournec ta nuna cewa, sun yi kama da ƙasar da ke birnin Luxor na Masar, kuma ƙasar ta shiga jikin gawar ne lokacin da ake yunƙurin sauya mata sabon wuri a Deir el-Bahari a ƙarni na 20 na Daularsu.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Tarihi

Tarihin Ƙabilar Fulani

Fulani, suna ne na ƙabilar Fulɓe a Hausance. Ƙabila ce wadda take magana da harshen, Fillanci ko Fulatanci, abin da
Tarihi

Yadda Sauyin Yanayi Zai Rusa Wuraren Tarihin Afirka

Tun daga zane-zanen Dutse da ke Kudancin Afirka zuwa Dalar da ke gefen Kogin Nilu, al’ummar da suka gabata sun