Daga: Safiyah Ma, Sulaiman, CGTN Hausa
A bana, an shaida matsalolin da tsarin gudanar da shugabanci na Duniya ya fuskanta bisa hadarori daban-daban, inda wannan ya zama wani ƙalubale ga haɗin guiwar Ƙasashe masu tasowa na Duniya.
Wani masani daga Thailand, Thanayod Lopattananont, ya bayyana cewa, matsalar rashin daidaiton ci gaba ta samo asali ne daga yadda Ƙasashe masu sukuni suka mamaye tsarin Duniya. Don haka, Ƙasashe masu tasowa ba za su dogara ga hanyar zamanantarwa da Ƙasashe masu sukuni suka bi ba, amma kuma su na binciken tsarin ci gaban da ya dace da halayensu, kamar zamanantarwa irin na Ƙasar Sin, da kuma ajandar Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta 2063.
Domin inganta harkokin tsarin gudanar da shugabancin Duniya, Ƙasar Sin ta gabatar da shawarar gina al’umma mai makomar baiɗaya ga ɗaukacin Bil’adama, da shawarar Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya da sauransu.
Waɗannan tsare-tsare sun tabbatar da kyakkyawar alƙibla ta nan gaba da kuma inganta ci gaba a tare tsakanin Ƙasashen Duniya.
A nasa ɓangaren, Babban Editan Rukunin Jaridun Zanzibar Ramadhan Makame Suleiman, ya yi nuni da cewar, aiwatar da shawarar Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya, ya sa ƙaimi ga bunƙasar ciniki tsakanin Ƙasashen Afirka da kuma tsakanin Afirka da Sin, da samar da guraben ayyukan yi da dama, da kuma inganta haɓakar Tattalin Arziki a Afirka.
Ƙasashe masu tasowa da masu saurin ci gaba sun himmatu wajen wargaza tsare-tsare da za su kawo cikas ga ci gaba mai ɗorewa. Su na kuma goyon bayan manufar “Haɗin kai shi ne karfin kowa” kuma su na ƙoƙarin buɗe sabon ɓangare don gudanar da haɗin guiwa a tsakaninsu.