Tsumi Da Tanadi

Samun Dala Tiriliyan Ɗaya Babbar Nasara ce ga Tattalin Arzikin Ƙasa – SEC

Daga: Bello Hamza da Sulaiman da Salahuddeen Muhammad

Darakta Janar na Hukumar da ke Kula da Hannayen Jari ta Najeriya (SEC), Dakta Emomotimi Agama, ya jaddada cewa, samun nasarar da Ƙasar ta yi na Naira Tiriliyan Ɗaya a Tattalin Azrkin Ƙasa, ba wai kawai ta samu haka ba ne, amma wani abu ne, da ya zama babbar nasara da kuma jajircewar Ƙasar.

Dakta Agama, ya sanar da haka ne, a jawabin da ya yi a wajen taron gabatar a taron Hukumar na 2024.

Taken Ƙasidar da ya gabatar a wajen taron, “Gudunmowar da Kasuwar Zuba Hannayen Jari ke takawa wajen bunƙasa Tattalin Azikin Dala Tiriliyan Ɗaya na Najeriya.”

Agama, wanda John Briggs Shugaban Sashe na Hukumar da ke Shiyyar Jihar Legas ya wakilce shi, inda ya sanar da cewa, kasuwar ta ci gaba da kasancewa, a matsayin wata jigo da ke ƙara haɓaka Tattalin Arzikin Ƙasar, ta hanyar ƙara tura kuɗaɗe na masu sayayya da suke buƙatar kuɗaɗen domin yin amfani da su.

A cewarsa, a ɗaukacin faɗin Duniya Ƙasashe sun samu bunƙasar tattalin arzikinsu ne, ta hanyar ayyukan Masana’antar, fasahar Ƙere-Ƙere da sauransu, musamman duba da yadda suka dogara a kan kasuwannin, su na zuba hannun jari tare da kuma zuba kuɗaɗen yadda ya kamata.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Tsumi Da Tanadi

Sharhi: Tattalin Arziki

Tattalin Arziƙi (Economy) ya dogara ne a kan samar da Abinci, Sutura, Ayyuka, Kiwon Lafiya, Ilimi, Gine-Gine da sauransu, da
Tsumi Da Tanadi

Dabino na Samun Tagomashi a Saudiyya

Kasuwar Dabino a Saudiyya na bunƙasa, yayin da aka samu ƙaruwar riba da kashi 14% a shekarar da ta gabata