Kasuwar Dabino a Saudiyya na bunƙasa, yayin da aka samu ƙaruwar riba da kashi 14% a shekarar da ta gabata (2023).
Wannan dai, ya na nuni da yadda aka samu ci gaba wadda ya kai kashi 152.5% na haɓakar tattalin arziki a fannin, inda ya kai SAR1.462 biliyan, idan aka kwatanta da SAR1.280 a shekarar 2022, a cewar Hukumar Kula da Dabino ta ƙasar (NCPD).
Har ila yau, a ƙarshen shekarar 2023, adadin ƙasashen da ke jigilar Dabino daga Saudiyya sun kai 119.

|Hoto: 📷 KSA Expats/ NCPD
Shugaban NCPD Dr. Mohammed Alnuwairan, ya yaba da nasarar da aka samu ga ƙoƙarin haɗin guiwa tsakanin shugabanni, da kamfanoni da dillalai masu fitar da kaya, da kuma hukumomin gwamnati.
Bugu da ƙari, ya jaddada cewar, cibiyar za ta bunƙasa ƙoƙarinta na haɗin guiwa tsakanin masu samar da Dabino na cikin gida da na waje, da shirya ayyukan kasuwanci, da sauƙaƙe hanyoyin fitar da kayayyaki, da kuma yin aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu a ƙarƙashin wani tsarin bai ɗaya da ke nufin tallafawa ƴan kasuwa.
A cikin 2022, an samar da tan miliyan 9.91 na dabino a Duniya. Dangane da bayanai daga Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya; Masar ita ce kan gaba wajen samar da dabino a Duniya, bayan da ta shuka kusan tan miliyan 1.73 a shekarar 2022 kaɗai. Saudiyya ta kasance ta biyu da tan miliyan 1.61 na Dabino, sai kuma ƙasar Aljeriya mai tan miliyan 1.25.

|Hoto: KSA Expats/ NCPD