Tsumi Da Tanadi

Sharhi: Tattalin Arziki

Tattalin Arziƙi (Economy) ya dogara ne a kan samar da Abinci, Sutura, Ayyuka, Kiwon Lafiya, Ilimi, Gine-Gine da sauransu, da kuma rarraba su, da cinikayyarsu har zuwa ga amfani da su ga al’umma.

Tattalin arziƙi shi ne bunƙasa, aiwatarwa da haɓɓaka ayyukan da ke kawo ci gaban ƙasa, ta hanƴar dogara a kan fitar da amfani daga ayyukan da mutum ke yi don amfanar kansa da kuma kula da su.

Abubuwan da ke haɓaka tattalin arziƙin ƙasa su ne; Mutane, Kasuwanci, Ma’aikatu, da Gwamnati.

Ayyukan tattalin arziƙi ya fara ne tun daga cinikayya, wato a lokacin da mutane biyu suka ƙulla yarjejeniyar cimma ciniki a kan wani abu da ake so, ta hanyar amfani da kuɗi ko wani abu mai daraja kamar Zinari, Azurfa, Tagulla da dai sauransu, duk da yake ana ganin cinikayya ta kuɗi kawai wani ƙaramin abu ne idan ana magana a kan tattalin arziƙin ƙasa.

Tattali arziƙi, na samun zumma ne tun daga samar da ayyuka ko abubuwan da ke amfani da albarkatun ƙasa ko ma’adinai, aikin Ɗan Adam, da sa jari.

Amma haka ya canja sanadiyyar canjin rayuwa, da kuma ci gaban fasahar Ɗan Adam wurin amfani da injina masu sarrafa kansu, ya kawo samun sauƙi da saurin aikata ayyuka, da kuma rage kuɗin da ayyukan kansa, haka nan kuma samun ci gaba wurin ƙirƙirar sabbin abubuwa, sabbin hanyoyin aiki, sabbin hanyoyin gabatar da ayyuka, manƴa-manƴan kasuwanni, kasuwannin da suka tattari abubuwa daban-daban, ana kuma samun ƙarin kuɗin shiga.

Tattalin arziƙi ya na samun nasara ne sanadiyar ayyukan al’adun al’umma, martabarsu, iliminsu, faɗaɗar fasaharsu, tarihinsu, tsarin al’ummarsu, tsarin tafiyar da siyasarsu da dokokinsu, har wayau; Da kuma irin yanayin ƙasar, ma’adinan ƙasa, da yanayin rayuwar halittun ƙasar, waɗannan su ne ke bayar da cikkakiyar samun haɓɓakar arzikin ƙasa, kuma waɗannan abubuwan suke bada wuri da abubuwan da arziki ke ci gaba da su sannan ya tsara su a kan amfanuwar ƙasa da al’ummar ta.

Akwai tattalin arziƙi da ya dogara kacokan a kan kasuwanci, kuma ya na gudana ne a kan cinikayyar ayyuka ko kayayyaki tsakanin mutane, ta hanyar samar da su da kai su kasuwanni domin cinikinsu da kuɗaɗe ko dai wani abin da aka ƙayyade mai daraja.

Akwai tattalin arziƙi da ya dogara a kan bayar da umurni daga ƴan siyasa kai-tsaye da kula da yadda ake samarwa ƴan ƙasa da ayyuka ko kayayyaki da kuma yadda za a saidar da su da rarraba su.

Akwai tattalin arziƙi da ya dogara a kan ma’adinan ƙasa, da sanya al’umma a cikin gudanarwar su.

Ƴancin kowace al’umma ko ƙasa ya dogara ne kacokan a kan bunƙasar Tattalin arziƙi. A yau Ƙasar Sin (China) ita ce ƙasa ta biyu da ta fi kowa yawan al’umma, amma ta samar da tsarin tattalin arziƙi da kowane ɗanƙasa zai sami nagartacciyar rayuwa, da wasu ƙasashe irin Indiya da Amurka da Dubai da Japan da sauran su.

Rashin samar da tsarin Tattalin arziƙi ya haifar da muguwar koma baya ga ƙasashe masu tasowa musamman a nahiyar Afirka, hakan ya faru ne saboda sun kasa tsarkake tsarin siyasar su da killace ma’adanai da inganta wutan lantarki da kawo masu zuba jari.

Inganta sana’o’i aba ce da ke da babbar fa’ida, wannan ya na cikin tarnaƙi da ƙasashe masu tasowa ke fuskanta. Wata babbar matsala ita ce, tashe-tashen hankula da muguwar cin hanci da rashawa da ya baibaye su.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Tsumi Da Tanadi

Dabino na Samun Tagomashi a Saudiyya

Kasuwar Dabino a Saudiyya na bunƙasa, yayin da aka samu ƙaruwar riba da kashi 14% a shekarar da ta gabata
Tsumi Da Tanadi

Mizanin Hauhawar Farashin Kayayyaki a Najeriya ya Ƙaru

Mizanin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙaru zuwa kaso 34.6 a watan Nuwamba, ƙaruwar maki kaso 0.72 daga kaso