Me ya sa Ranar 26 ga Disamba ake kiranta da ‘Boxing Day?’
Wata al’ada ce da aka yarda da ita ta nuna cewa, sunan ya samo asali ne daga al’adar da masu hannu da shuni ke yi na bada abin da ake kira “Akwatin Kirsimeti” da ke ɗauke da Kuɗi da kuma kyaututtuka ga bayi da Ƴan kasuwa washegarin Kirsimeti.
‘Boxing Day’ Rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti, amma masana tarihi su na ganin, ta samo asali ne a lokacin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria a shekara ta 1827 Miladiyya.
Ranar ba ta da wata alaƙa da wasan Damben Boxing da ake gudanarwa a faɗin Duniya. Sunan ya samo asali ne sakamakon ƙunshe kyauta da masu arziki ke yi a cikin Akwati kafin su bai wa mabuƙata (‘Box’ na nufin Akwati a harshen Hausa).
Boxing Day a al’adance, ita ce Ranar da Bayi kan yi hutun aiki sannan su karɓi kyautuka na musamman daga Iyayen-gijinsu.
Haka nan, a Ranar ce su ma suke zuwa Gida domin bai wa Iyalansu Akwatunan kyautar.
A yankunan Catalonia na Spain da Ireland na Birtaniya, su na yin Bikin Ranar ne da sunan “Saint Stephen’s Day.”
A ƙasashen Turai kuma kamar; Hungary da Jamus da Poland da Netherlands, su na kallon ‘Boxing Day’ a matsayin Ranar Kirsimeti ta biyu.
Tara Kuɗi
Su ma Coci-Coci/Majami’u sun taka rawa wurin ƙirƙirar ‘Boxing Day.’ Sukan karɓi Kuɗi daga masu bauta a tsawon shekara baki ɗaya domin bai wa mabuƙata a lokutan Kirsimeti.
Sannan, sukan ajiye Kuɗin a cikin Akwatuna kafin a buɗe su a Ranar Kirsimeti, sai kuma a bai wa mabuƙata kwana ɗaya bayan Kirsimeti wato ‘Boxing Day.’
Sai dai a yanzu ba a fiye amfani da Akwatunan ba kamar da.
Yaushe ne Boxing Day?
Boxing Day, ita ce Rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti, wadda ke faɗowa ranar 26 ga kowane Disamba. Har ila yau, Rana ce ta hutu a Najeriya da wasu Ƙasashen Duniya.
Bugu da ƙari, idan ta faɗo ranar Asabar, akan mayar da hutunta zuwa Litinin ta gaba. Idan kuma ta faɗo ranar Lahadi, to ranar Talata ne hutun.