Rana Kamar Ta Yau

Bikin Ranar Kirsimeti

A Rana mai kamar ta Yau, 25 ga Watan Disamba, a shekara ta 336 AD, Cocin Kirista a Roma ya fara yin Bikin Kirsimeti.

A lokacin Sarkin Roma Constantine aka fara yin Bikin, duk da a zahiri Romawa ne suka ƙirƙira, amma har yanzu ba a samu takamaiman sunan mutumin da aka tabbatar da shi ne ya fara yin bikin ba.

Asalin Kirsimeti

Kirsimeti ya samo asali ne daga al’adun Arna da na Romawa. Romawa su na yin bukukuwa guda biyu a watan Disamba. Na farko shi ne; Bikin Saturnalia, wanda shi ne bikin makonni biyu na girmama Allahn Aikin Gona na Saturn.

A ranar 25 ga Disamba, su na yin bikin Haihuwar Mithra, Allahn Rana. Bukukuwan biyun sun kasance masu ban sha’awa, inda ake sada zumunta, gami da waƙe-waƙe, raye-raye, da kuma shaye-shaye.

Haka kuma a cikin watan Disamba, inda Rana ba ta yin Haske saboda Sanyi, a al’adun Maguzawa (Pagan) su na kunna Wuta da Kyandir don kawar da Duhu. Romawa sun shigar da wannan al’ada cikin bukukuwan nasu.

Yayin da Addinin Kiristanci ya yaɗu a Turai, Limaman Kirista ba su iya hana al’adu da bukukuwan Arna na al’ada ba, tun da ba wanda ya san ranar haihuwar Yesu, sai suka mai da al’adar Arna (Maguzawa) ta zama bikin ranar haihuwarsa. Tun da ba a rubuta ranar da aka haifi Kristi a cikin Littafin Injila (Bible) ba.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Rana Kamar Ta Yau

Yau Shekaru 32 da Fara Tura Saƙo na ‘SMSC’ a Duniya

A Rana Mai Kamar Ta Yau Neil Papworth, Injiniya mai shekaru 22 da ke aiki a Sema Group Telecoms, ya
Rana Kamar Ta Yau

Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya!

Kowace shekara a ranar 9 ga Disamba, ita ce Ranar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya. Ana amfani