Jiya Da Yau

Alh. Bashir Ottoman Tofa: Masanin Kimiyyar Sararin Samaniya

A shafin Facebook kaɗai an yi amfani da sunan Bashir Tofa fiye da sau 33,000, ciki har da neman ƙarin bayanin kansa da gidansa da batun rasuwar tasa.

Masallacin gidan Marigayi Alh. Bashir Ottoman Tofa |Hoto: Instagram

Can a shafin matambayi ba ya ɓata na Google kuwa, sunan Bashir Tofa ne abu na uku da aka fi dubawa, inda ake nemi bayani a kansa fiye da sau 20,000.

Mutane da dama sun san Bashir Tofa ne a matsayin gogaggen ɗansiyasa kuma ɗaya daga cikin Dattawa masu faɗa a ji a Arewacin Najeriya.

Alh. Bashir Ottoman Tofa, a yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron ƙara wa juna sani, a Jihar Kano. |Hoto: Kano Focus

Sai dai marigayin ya na da wasu abubuwan da ba lallai kowa ne ya san su ba, kuma ya yi shuhura a waɗannan fannoni.

MASANIN KIMIYYAR SARARIN SAMANIYA

Malam Bashir Tofa, gogaggen masanin kimiyyar sararin samaniya ne, wanda ya dinga bincike da rubuce-rubuce a kan wannan ɓangare.

Ba a bincike da rubutun kawai ya tsaya ba, masanin ya dinga ƙoƙarin bayyana kimiyyar sararin samaniyar a tsarin Al-ƙur’ani tare da fito da al’ajuban da ke tattare da hakan.

A wani littafinsa mai taken “Kimiyyar Sararin Samaniya,” akwai wajen da ya ɗauki mai karatu ya zagaya da shi a sararin samaniya, tun daga Unguwar Rana, wato ‘Solar System’ har Birninmu na ‘Milky Way Galaxy da ma wajen birnin zuwa’ Virgo Supercluster.’

Wannan zagaye na ƙirƙira da ya yi da mai karatu bisa la’akari da abin da bincike ya gama ganowa dangane da Sararin Samaniya da halittun cikinta.

Zai yi matuƙar wahala ka karanta littafin nan na Kimiyyar Sararin Samaniya da ke cike da bayanai kan tsarinta da dokokinta da halittun cikinta ba tare da ka ƙara miƙa wuya ga Allah SWT ba, da kuma ƙaruwar Tauhidi.

MARUBUCI

Malam Bashir Tofa, Marubuci ne sosai, kuma yawanci rubuce-rubucensa da Hausa ya yi su, sai dai akwai na turancin ma.

Ya rubuta littattfai tun daga abin da ya shafi addinin Musulunci da na ban dariya da ban mamaki da labarin Aljanu.

“Ya yi rubutu a harkar addini sosai,” in ji Alhaji Ahmad Aminu, wani amininsa tun na ƙuruciya.

Daga cikin littatafansa akwai:

  • Kimiyyar Sararin Samaniya
  • Kimiyya da Al’ajuban Alƙur’ani
  • Tunaninka Kamanninka
  • Rayuwa Bayan Mutuwa
  • Takaitaccen Tarihim Islam
  • Mu SHa Dariya
  • Gajerun Labarai
  • Amarzadan a Birnin Aljanu
  • Amarzadan Da Zoben Farsiyas
  • Fatuhu Dan Aljan
  • Mutane da Gurare a Islam
  • Muna ta Dariya, da sauransu.

NASABA

Kamar yadda yake a sunan marigayin, ɗan garin Tofa ne a Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin ƙasar. Sai dai aminin nasa Alhaji Aminu ya ce asalin kakanninsa Barebari ne “Amma shi da iyayensa duk haifaffun kuma mazauna ƙasar Kano ne a garin Tofa.

“Kakan kakansa Ɗan Adalan Tofa ne, sannan wani ɗan Baffansa ma mai suna Tsoho Tofa ya riƙe muƙamin, kafin daga baya sarautar ta bar gidansu.”

Wannan dalili ne ya sa aka yi masa tsagen Barebari a fuska kamar yadda aminin nasa ya ce.

Ya ƙara da cewa “Da yawa daga cikin ƴan gidansu kamar yayarsa da ƙanwarsa mai bin sa da wasu ƙannensa da ma wasu daga cikin ƴaansu duk an yi musu zanen.”

KARATU

Alhaji Bashir ya yi karatunsa na Firamare a Shahuci Firamare, sannan ya je ƙaramar Sakandare ta Gwale daga can ya tafi babbar sakandare a Kwalejin Rumfa duk a garin Kano.

Amininsa ya ce, daga nan ne sai ya tafi Ingila ya yi karatun Digiri na ɗaya da na biyu a fannin Tattalin Arzikin Kasuwanci.

“Ya zauna a Ingila tsawon lokaci, har ma a lokacin mukan je ofishin BBC wajen abokanmu ma’aikatan sahsne Huasa ƴan Najeriya don yin zumunci. To daga baya mu ma (har da shi marigayin), muka dinga yin aikin wucin gadi na ɗan lokaci a BBC Hausa ɗin.

Kazalika Alhaji Bashir ya yi karatun addini sosai tun yana ɗan shekara bakwai kama daga kan Alƙu’ani da Hadisai da Shari’a har kan Nahawu a cewar aminin nasa.

AYYUKA

Ya kasance ɗan kasuwa, ɗan kuma kasuwan mai da masana’antu.

Ya yi aiki da kamfanin Inshora na “Royal Exchange” daga 1967 zuwa 1968. Daga 1970 zuwa 1973.

Ya kasance shugaban Kamfanin International Petro-Energy Company (IPEC) And Abba Othman and Sons Ltd.

Har ila yau, ya kuma kasance mamba a kwamitin gudanarwa a Impex Ventures, Century Merchant Bank And General Metal Products Ltd.

SIYASA

Alh. Bashir Ottoman Tofa, ya shiga harkar siyasa a shekarar 1976 lokacin ya na Kansila a Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa, a shekarar 1977 aka zaɓe shi ɗan Majalisar Wakilai.

A lokacin Jamhuriya ta biyu ta Najeriya, Tofa a lokuta daban-daban ya kasance sakataren jam’iyyar NPN reshen Kano, daga baya ya zama sakataren kuɗi na jam’iyyar, kuma ya kasance mamba na kwamitin juyin juya hali na ƙasa.

A lokacin Jamhuriya ta uku, ya na cikin ƙungiyar masu sassaucin ra’ayi wadda ta misalta zuwa ga yarjejeniyar “Liberal” lokacin da ba a yi mata rajista a matsayin jam’iyyar siyasa ba, Tofa ya shiga NRC a 1990.

A shekarar 1993, lokacin da gwamnatin Babangida ta gabatar da tsarin zaɓin A4, aka zaɓi Tofa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar NRC.

A lokacin zaɓen fidda-gwani na jam’iyyar, ya doke Pere Ajunwa, da Joe Nwodo da kuma Dalhatu Tafida, in da ya samu tikitin zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NRC.

Ya kasance abokin Halilu Aƙilu, babban jami’in tsaro a lokacin. Abokin takararsa a zaɓen shi ne Sylvester Ugoh, ɗan ƙabilar Ibo (Igbo) kuma tsohon gwamnan rusasshiyar babban bankin ƙasar Biafra.

Watau; Dukkan su biyun sun kasance ƴaƴan rusasshiyar jam’iyyar NPN ce.

Da alamu dai Tofa, ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasar da abokin takararsa Moshood Kashimawo Olawale Abiola, wadda ya kasance abokin shugaba Babangida, kuma ɗan ƙabilar Yarbawa daga kudu maso yammacin Najeriya, amma gwamnatin Babangida ba ta fitar da sakamakon zaɓen ba.

An tilastawa Babangida ya sauka daga mulki a watan Agustan shekera ta 1993, bayan zanga-zangar neman sakamakon zaɓen.

IYALANSA

Marigayin wanda ya rasu yana da shekara 74, ya bar mace ɗaya da ƴaƴa shida, mata uku da maza uku. Sannan ya bar tarin ƴan uwa.

Aminin nasa ya kuma bayyana shi a matsayin mutum mai matuƙar son tsafta da ƙawa, “shi ya sa ma ko yaushe za a ga gidansa kamar sabon gini ake yi, amma ba haka ba ne yawan gyara ne kawai da yake sa wa a yi.”

Marigayi Alh. Bashir Ottoman Tofa, a gidansa ta na watsawa Ɗawisu Hatsi. |Hoto: Vanguard News

RASUWA

Kowane rai sai ya ɗanɗani mutuwa!” Kamar yadda Allah Ya fada a Al-ƙur’ani mai girma.

A ranar Litinin uku ga watan Janairun sabuwar shekarar 2022 ne Allah Ya karɓi rayuwar Alhaji Bashir Othman Tofa, tsohon ɗantakarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar NRC a shekarar 1993.

An yi jana’izar tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya Bashir Othman Tofa a gidansa da ke unguwar Gandun Albasa a birnin Kano na Najeriya. |Hoto: BBC Hausa

Rasuwar tasa ta ɗimauta da yawan mutanen Najeriya, saboda irin rashin gwarzo da suke cewa ƙasar ta yi.

Ɗimbin mutane suka halarci jana’izar ciki har da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero. |Hoto: BBC Hausa

Mutane da dama tun daga kan shugaban ƙasar Muhammadu Buhari (na wancan lokacin) har zuwa masu amfani da kafafen sadarwa sun yi ta miƙa saƙon alhini da ta’aziyyar wannan “Gwarzo.”

An binne shi ne a tsakanin kabarin mahaifinsa da na mahaifiyarsa. |Hoto: BBC Hausa

Mutane da dama sun bayyana marigayin a matsayin mutum mai son ci gaban Najeriya da taimakon jama’a. |Hoto: BBC Hausa

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Jiya Da Yau

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne
Jiya Da Yau

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna

Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen