A Rana mai kamar ta yau 23 ga Disambar 1953, Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero, ya rasu, wanda shi ne na uku da Turawa suka naɗa Sarauta, inda ya yi mulkin Kano na tsawon shekaru 27.
Kamar yadda tarihi ya bayyana, shi ne Ciroman Kano na farko da ya zama Sarki kuma na farko cikin sarakuna da ya fara aikin Hajji, wanda ta dalilin haka ne ma ake kiransa da ‘Sarki Alhaji.’
Bugu da ƙari, a zamaninsa aka gina Kwalejin Rumfa (Rumfa College), wadda a lokacin ake kiranta da Makarantar Midil ‘Middle School.’
Har ila yau, masana tarihi sun tabbatar da cewar; a lokacin mulkinsa ya samar da ci gaba daban-daban wadda suka bunƙasa Kano.