Ana ci gaba da murnar shahararren ginin Turkiyya na ban mamaki wato ‘Masallacin Ayasofya,’ komawarsa Masallaci.

Kewayen Masallacin Ayasofya. |Hoto: AP News
Wannan kyakkyawan ginin na Santambul, mai ɗimbin tarihi ya karɓi baƙuncin Miliyoyin Musulmai a faɗin Duniya tun daga 2020.

Ayasofya, wanda aka gina a ƙarni na shida, wanda a farko Coci ce ta Daular Byzantine, an adanata da kula da ita tsawon shekaru haka kuma ta samu kyakkyawar kulawa tun daga zamanin Daular Usmaniyya bayan sun mayar da Santambul babban birninsu a 1453.



|Hoto: AP News
Idan aka haɗa tarihin Addinin Musulunci da na Kirista, masana tarihi na kiran wannan gini da “Abin Mamaki na Takwas a Duniya,” wato “Eighth Wonder of the World” a turancin Ingilishi.



|Hoto: AP News
Al’umma daga sassa daban-daban na duniya kan ziyarci Masallacin domin yawon buɗe ido.

Wasu masu yawon buɗe ido, a farfajiyar Masallacin Ayasofya. |Hoto: Yedikapi Tour