Tarihi

Bugun Littafin Al-kur’ani na Farko a Duniya

Bugun littafin Al-kur’ani Mai Tsarki na farko a Duniya wadda aka buga da injin bugu ba rubutun hannu ba.

Paganino & Alessandro Paganini, wani kamfanin ɗab’i da ke birnin Venice, a ƙasar Italiya, sun fitar da Al-kur’ani na farko da aka buga da Larabci, wadda kwafi guda ne kawai ya tsira.

Bugun kwafin littafin Al-kur’ani na Larabci tilo guda da ya tsira. |Hoto: Madain project

Tsakanin ranar tara ga watan Agusta, na shekara ta 1537, da kuma tara ga watan Agustan 1538, masu buga takardu na Venetian Paganino & Alessandro Paganini, suka fitar da bugun Al-kur’anin na farko da Larabci.

Wataƙila, an yi niyyar fitar da shi zuwa Daular Usmaniyya ta Turkiyya tsawon ƙarnuka, ana tsammanin wannan bugun amma ya ɓace, kuma jita-jitar ita ce Paparoma ne ya ƙone cikakken bugun.

A cikin shekarar 1987, Farfesa Angela Nuovo, ta sami kwafi guda ɗaya a cikin ɗakin karatu na Franciscan Friars na Isola di San Michele a birnin Venice na ƙasar Italiya.

Kwafin bugun Al-kur’anin da aka gano a ɗakin karatu na Franciscan Friars na Isola di San Michele a birnin Venice na ƙasar Italiya. |Hoto: Madain project

Kwafin ya ƙunshi bayanin mallakar Teseo Ambrogio degli Albonesi, wadda ya mutu jim kaɗan bayan shekarar 1540, da tambarin Arcangelo Mancasula, (Vicar of the Holy Office, Holy Inquisition) na Cremona, wadda aka yi amfani da shi bayan ƴan shekaru.

Bayan haka, Albonesi, masanin ilimin Gabas ta Tsakiya daga Pavia, shi ne kawai mutumin da aka sani ya sarrafa bugun Al-kur’anin na farko da aka buga a cikin Larabci, kuma ya ambace shi a cikin gabatarwarsa a harshen Armeniya a 1539.

Hoto: Madain Project

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Tarihi

Tarihin Ƙabilar Fulani

Fulani, suna ne na ƙabilar Fulɓe a Hausance. Ƙabila ce wadda take magana da harshen, Fillanci ko Fulatanci, abin da
Tarihi

Yadda Sauyin Yanayi Zai Rusa Wuraren Tarihin Afirka

Tun daga zane-zanen Dutse da ke Kudancin Afirka zuwa Dalar da ke gefen Kogin Nilu, al’ummar da suka gabata sun