Bikin La Tomatina, da ake yi duk shekara a ƙauyen Buñol da ke Valencia na ƙasar Spain na samun halartar dubban mutane daga faɗin Duniya.

Hoto: When in City
Ana amfani da Tumatur maras kyau wajen jifar juna, don tabbatar da cewa ba a yi ɓarnar abinci ba yayin bikin.

Hoto: When in City
La Tomatina, ya kasance shahararren biki musamman ga al’ummar yankin da kuma masu yawon buɗe ido da kan ziyarta daga sassa daban-daban na Duniya.


Har ila yau, an yi hasashen cewar, shi ne bikin al’ada na abinci mafi girma a Duniya. Aƙalla ana amfani da Kilo 150,000 na Tumatur, inda ake samun mahalarta kusan mutum 220,000.



Shi dai wannan biki, ya samo asali ne a shekarar 1940, a lokacin da wasu abokai suka fara jifar junansu da nufin wasa, daga nan ne ya rikiɗe zuwa shahararren bikin al’adar gargajiya a ƙauyen Buñol.

