Gidan tarihi na Dar Gnawa Museum da ke birnin Marrakech na Maroko ya na cike da tarin abubuwa da suka shafi labarai, al’adu, tadoji, da UNESCO ta saka cikin jerin gadon al’ummar Duniya.

Al’ummar Gnawa su na alfahari da yaɗa al’adunsu. / Hoto: Dar Gnawa Museum
Daga: Firmain Eric Mbadinga
Gidan adana kayan tarihi na Dar Gnawa Museum ya na nuna fasahohi da kayan tarihi na al’ummar da ta samo asali daga yankin Afirka Kudu da Sahara, waɗanda a baya Bayi ne da ke Rayuwa a yankin Maghreb tun shekarun Ƙarni na 19.
Wani abin kiɗa mai suna Guembri, wanda ke da Zare kuma yake ba da Sauti daban-daban, abu ne da ke wakiltar salon biki da raye-raye na al’adun Gnawa.
Al’ummar Gnawa waɗanda ke da asali daga Afirka Kudu da Sahara ana samun su a dukka yankin Maghreb, daga Tunisia zuwa Algeria, da kuma Morocco.
Miliyoyin Mata da Maza na wannan al’umma su na alfaharin yaɗa al’adarsu, wadda ta ƙunshi cike da tasirin al’adun ƙabilun Barber, da Larabawa Musulmai.
An kafa gidan tarihin Dar Gnawa Museum a shekarar 1860 a garin Derb jdid na Marrakech, da manufar nuna wa Duniya faɗin al’adun wannan jama’a.
Oussama Elasri, ɗan wannan al’umma ne. Kuma mai kulawa ne kuma mataimakin Daraktan wannan gidan tarihin. Ya na yawan faɗa wa masoya fasaha cewa, Dar Gnawa cike yake da al’adu.

Gidan tarihi na Dar Gnawa Museum da ke birnin Marrakech na Morocco ya na cike da tarin abubuwa da suka shafi labarai, al’adu, Fadoji. |Hoto: TRT Afirka
“Wannan gidan tarihin ya na ba da mahanga zuwa tarihi daɗaɗɗe, da labaran alaƙar Afirka Kudu da Sahara da yankin Maghreb, musamman da Morocco,” cewar Oussama Elasri da yake zantawa da manema labarai.
Tun bayan buɗe ta ranar 1 ga janairun 2024, bayan an mata gyare-gyare, cibiyar ta saka burin adanawa da bayyana tarihin Gnawa.
Gidan tarihin ya na ɗauke da kayayyaki kiɗa, kamar Guembri, da tufafin al’ada da na yau da kullum da mutanen Gnawa ke sanyawa.

An nuna wasu daga cikin kayayyakin tarihin gidan a bikin al’adu na Dakar da aka yi a Nuwamban bara. / Hoto: Dar Gnawa Museum
”Wannan ya nuna faɗin tasirin wannan al’adar tsakanin ɓangarorin Afirka, wanda ke ƙara danƙon zumunci tsakanin ƙasashe,” in ji Oussama Elasri.
Baya ga nune-nune, gidan tarihin ya na shirya nunin Fim, da Kaɗe-Kaɗe, Raye-Raye, da Wasan Kwaikwayo da Bukukuwa, dss.

Masu bincike da Ɗalibai su na ziyarta cibiyar kan batutuwa kamar yadda ake ƙera Guembri, da rawar bori, da alaƙar al’adun Gnawa, da al’adun Afirka.
Cibiyar ta Dar Gnawa ta dace da ci gaban zamani a Morocco kamar yadda Ƙasar da ke ƙarƙashin Sarki Mohamed VI, ta na da kishin raya al’adu.
Ɗaukaka manufofin cibiyar tarihin ya na da tasiri wajen nuna damarmakin ci gaban tattalin arziƙi da Yawon buɗe ido da Morocco ke da shi.
