Mizanin hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙaru zuwa kaso 34.6 a watan Nuwamba, ƙaruwar maki kaso 0.72 daga kaso 33.88 da aka gani a watan Oktoba.
Hukumar ƙididdiga ta ƙasar NBS, ta ce idan aka kwatanta adadin a shekara-shekara, hauhawar farashin ya ƙaru da maki kaso 6.4 kan kaso 28.2 da aka samu a watan Nuwamban 2023.
Idan aka kwatanta da wata-wata, adadin a watan Nuwamban 2024 shi ne kaso 2.638, wanda ya yi ƙasa da maki kaso 0.002, idan aka kwatanta da kaso 2.64 da aka gani a Octoban 2024.
Hukumar NBS ta alaƙanta ƙaruwar da hauhawar farashi a muhimman ɓangarori ciki har da na abinci da kayayyakin sha da Gidaje da Ruwa da Lantarki da Gas da Tufafi da Sufuri da Ilimi da Kiwon Lafiya da sauran kayayyaki da hidimomi.