Noma Da Kiwo

Yadda Ake Kiwon Kifi a Sauƙaƙe

Wannan kalma ta ‘Fishery’ ta na da mabambantan ma’anoni. Oxford Dictionary (2000), Encarta Dictionary (2009), Merriam-Webster Dictionary (2015), sun kalle ta a matsayin ‘wuri ko muhallin da ake kamun Kifi’.

Saboda haka, za mu iya cewa ke nan wannan kalma ta ‘Fishery’ da farko ta na nufin wani yanki, ko wuri ko muhalli wanda ka iya zama wani yanki na Teku, Kogi, ko Tafki wanda Kifi ke rayuwa a wurin, kuma wurin ya zama bigiren kamun Kifi.

Ke nan, duk wani yanki na Kogi ko Teku da makamantansu da Kifi ba ya rayuwa a wurin ba za a iya kiransa ‘Fishery’ ba.

Sannan kuma, ta na da ma’ana ta kamfanin da ke kamawa ko sayar da Kifi. Wannan kamfani zai iya kasancewa babba ko ƙarami. Duba (Encarta Dictionary, 2009; Oxford Dictionary, 2000; Wikipedia, 2015).

Har wa yau dai kuma ta na da ma’ana ta dukkan wani abu da ya shafi sana’ar Kifi tun daga kiwon Kifi, kamun Kifi, gyaran Kifi, da kuma sayar da kifin, da ma wurare da masa’antun da ake aiwatar da wannan sana’ar. Kai, har ma da dabaru ko hanyoyin kamun kifin sun shigo ciki. Waɗanda suka haɗu a kan haka sun haɗa da (Encarta Dictionary, 2009; Wikipedia 2015).

Sannan kuma akwai ‘Fishery’, a matsayin fannin karatu da ake koyarwa a fannin aikin Gona, wato ‘Agriculture’ da yake koyar da dukkan wani abu da ya shafi harkar Kifi kamawa tun daga sanin shi kifin a kan-kansa, kiwata shi, kama shi, gyaggyara shi, sayar da da shi da sauran dangoginsa.

Wannan fanni na aikin gona (fishery), ya na bada muhimmiyar gudunmowa wajen samar da ayyukan yi, inganta harkar samar da Abinci, da kuma haɓɓaka hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga ga ɗaiɗaikun mutane, Masana’antar da kuma ƙasashe a Duniya.

Mene ne Kiwon Kifi?

To da farko dai, idan muka ce Kiwon Kifi to wannan na nufin hanyar sarrafa ƙananan Kifaye ta hanyar ba su kulawa har su kai mizanin girma, ta yadda za su ci gaba da hayayyafa su ƙara yawa, wanda dama wannan shi ne babban dalilin kiwon nasu.

Yadda Ake Fara Noman Kifi

Wani kududdufin Kiwon Kifi

Noman Kifi dai iri-iri ne, akwai hanyoyi daban-daban saboda dalilan kiwonsa na ƙara yawa a kullum a Duniya.

Akwai dalilai da dama na bunƙasar Noman Kifi saboda a kullum ana samun ƙaruwar adadin mutane mabuƙata Kifi da sauran albarkatun cikin ruwa wadda suke amfani da shi a matsayin Abinci ko kuma sana’a, wadda za su dogara da ita. Bayan haka, mutane na ƙara fahimtar muhimmancin cin Abinci mai ɗauke da Kifi a ciki.

Mutane da dama na Noman Kifi ne a bisa ra’ayinsu, ko dai don a ci ko a sayarwa don samun biyan buƙatar rayuwa ta yau da kullum, ko kuma saboda nishaɗi, wasu kuma su na Noman Kifi ne don ilmantarwa, musamman a manyan Makarantu da wasu Cibiyoyi don koyar da ɗalibai yadda ake kiwon a aikace (Practically).

Matakan Farko na Noman Kifi

  1. A tabbatar an tantance irin Gona, wato inda za a Noma Kifin; Shin a bayan Gida ne ko kuma a Tafki ne, sa’annan ya ya wajen yake ta fuskar yanayin Zafi ko Sanyin wajen?

Sa’annan dole sai an zayyana dalilin da zai sa a fara Noman Kifin wanda ta haka ne za a fi samun cikakken ƙwarin guiwa a harkar.

Bayan haka dole a tantance irin nau’in Kifin da ake so ka kiwata, saboda akwai hanyoyi iri-iri wajen Noman Kifi. Saboda haka, akwai buƙatar sanin wani irin Kifi ake so a Noma, da kuma rubuta tsari da manufofi na kiwon.

Duk mai buƙatar ya fara wannan sana’a, ya na buƙatar amsa waɗannan tambayoyin:

a. Me za a yi da kifin bayan an Noma? Abinci za a yi da shi, sayarwa, ilmantarwa ko kuma kawai don ƙawa (kwalliya)?

b. Shin ana da nufin gina ɗan ƙaramin Tafkin Kifi ne, ko kuma niyyar ita ce; Kafa katafaren Kamfani domin samun riba mai yawa da shahara a wannan fanni?

  1. An tantance irin jinsin Kifin da ake so a Noma? Saboda tafkin Noman Kifin da za a gina ya danganta ne da irin kalar kifin da za a Noma.

Sa’annan kuma akwai buƙatar fahimtar waɗannan:

a. Idan har an tantance irin Kifin da ake so a Noma, to akwai buƙatar tuntuɓar wanda yake Noma irin wannan Kifi domin su ba da ƙarin haske a kan yiwuwarsa da irin ƙarfin da ake da shi.

b. A rubuta kuma a tantance duk kuɗin da ake kashewa akan kowanne irin jinsin Kifi, kuma ya zama wajibi a san cewa, farashin kowane daga ciki ya sha bamban da kowane irin jinsin Kifi da za a Noma.

c. A kuma yi la’akari da irin yanayin da ake so a Noma Kifi. Akwai Kifin da ke buƙatar Ruwa mai sanyi, akwai kuma mai buƙatar ruwan ɗumi, saboda haka, ana buƙatar gujewa duk wani kasha-kashen kuɗi da ke da alaƙa da salon sanyayawa ko dafa ruwa.

Abubuwan da Ake Buƙata Don Buƙatar Kiwon Kifi

Wani yanki mai yawan ruwa marasa ƙafewa.

Kafin a fara Noman Kifi, dole Manomi ya tabbatar ya tanadi waɗannan abubuwan:

  1. Tsaftataccen Ruwa mara yankewa, ko dai ta hanyar amfani da bututun zuba Ruwa ko kuma ta hanyar Rijiyar Burtsatse.
  2. Samar da lafiyayyar hanya wacce za ta sauƙaƙe shiga da fice daga Gonar.
  3. Bayan haka kuma, ya kamata a ajiye Gonar kusa da Kasuwa domin sauƙaƙe shige da fice da iya hanzarta kai Kifi Kasuwa (idan buƙatar hakan ta taso) don kiyaye lalacewarsu.
  4. A tabbatar an yi Gonar a wurin da yake fili ne kuma a kiyayi yin gonar a kan Tuddai.
  5. A tabbatar da sa ido a Gonar wato ta sami cikakken kulawa.
  6. Irin Kifi da za a zuba ya kasance irin da ke da juriyar ƙarancin iska ne kuma irin wanda ke matuƙar buƙata.

Zaɓen Filin Kiwon Kifi Mafi Dacewa

A nemi fili marasa Tudu, kuma a guji wuri mai yawan Tuddai da me daji-daji domin gyaransa zai haifar da ƙaruwar kuɗin noman. A sauƙaƙe, za a iya gina Kududdufin kiwon a bayan Gida don samun sauƙin kulawa.

  1. A nemi wurin da ke da sauƙin shiga da abin hawa don shiga ko fita da Kifin domin hana saurin lalacewa.
  2. Dole kuma ya zama babu matsalar Ruwa a wurin don hana yawan asara.

Shin ko Akwai Ƙalubale a Kiwon Kifi?

Kamar yadda muka sani bisa al’ada kusan kowace irin sana’a ta na cike da ƙalubale da matsaloli masu ɗimbin yawa, dole sai an yi haƙuri gami da juriya musamman a lamari wanda ya shafi Kiwo.

A taƙaice dai, za mu iya cewa haƙuri shi ne makami kuma jigon nasarar Manomi, misali; Makiyayi kullum sai ya fitar da Shanunsa zuwa Kiwo, komai Sanyi, komai Ruwa, kuma komai zafin Rana ba zai huta ba ko da na rana guda dole sai ya fita Kiwo, a haka zai ci gaba da rainonsu ya na basu kulawa shekara da shekaru har su kai ɗaruruwa zuwa dubunnai, ba don komai ba sai don ya jure kuma yi haƙuri da irin ƙalubalen da ya fuskanta.

Haka zalika mai Kiwon Kaji shi ma dole kullum sai ya tsaftace makwancinsu sa’annan ya zuba musu sabon Abinci da Safe, da Rana da Yamma ba tare da gajiyawa ba.

To haka mai Kiwon Kifi wajibi ne sai ya zama mai juriya kafin ya kai ga nasara. Haƙuri da bin komai sannu a hankali shi ne babban makami a sana’ar Noman Kifi.

Idan mutum baƙo ne a wannan fanni, to ya na buƙatar samun fahimta da ƙwarewa a wannan fanni na neman ƙarin haske daga Manoma waɗanda sun daɗe a harkar Kifin.

koda yake, alal haƙiƙa Kiwon Kifi ba ya buƙatar wani kuɗi mai yawa kafin fara shi. Sai dai ya danganta da ƙarfin aljihu da kuma kwatankwacin yadda ake son a aiwatar da shi. Kamar yadda masana a fannin ke ba da shawarar farawa da ƙaramin jari.

Ba komai ya sa masanan ba da wannan shawara ba, sai dai farawa daga mataki na ƙasa zai bayar da damar fahimta tare da ƙwarewa kafin a tsunduma ga mataki na gaba.

Ko an taɓa harkar, mallaka da kuma tafiyar da Gonar Kifi na buƙatar ilimi mai yawa a kan yadda sana’ar take.

Idan kuma niyyar ita ce a mallaki sana’ar, sannan a dinga lura da ɓangaren sha’anin wannan Gona, to hakan ma ya na bukatar aa faɗaɗa ilimi a kan sana’ar, sannan a ɗauki mutum wanda ya fi kuzari a cikin ma’aikatar, domin tafiyar da wannan harka sai an sami mutum tsayayye mai juriya.

Tafkin Kiwon Kifi don Ado

Wasu Hanyoyin Neman Ilimin Kiwon Kifi

a. a nemi aiki a Gonar da ke Noma irin jinsin kifin da ake da niyyar nomawa. Hakan zai taimaka a ƙara faɗaɗa ilimi ta fannin sanin ɗabi’ar kifayen, da kuma sanin tsarin rayuwarsu.

b. A nemi ilimi a kan Intanet da Littattafan da aka buga waɗanda mafi yawancin su na binciken bayanai takaimaimai akan yadda ake noman ire-iren Kifaye.

c. A lazimci kasancewa Ajujuwa a Jami’o’i ko makarantu musamman akan Noman Kifi. Wannan ya na da matuƙar amfani idan aka yi da wuri, saboda zai feɗe Biri har Wutsiya a kan wannan sana’a ɓaki ɗayanta.

Yadda Ake Gina Tafkin Kiwon Kifi

A tabbata an cire sauwoyi da sauran ciyayi da ke wajen.

Bayan an kammala share filin sannan an yi gwaje-gwaje, to sai a fara gina rami ana fitar da ƙasar gefe ta yadda za a fitar da siffar ramin.

Mataki na gaba shi ne; Gwada fasalin tsayi da faɗin tafkin.

A gwada tsayi da faɗin kowacce kusurwa cikin hikima.

A tabbatar an daidaita tudun ramin ka da ya gaza 1.5 metre.

Bayan an kammala ginin tsayi da faɗin ramin sai a zana magudana daga tsakiyar ramin wanda za a riƙa fitar da lalataccen ruwa da sauran datti.

Sassan kammalallen kududdufin Kiwon Kifi na zamani.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Noma Da Kiwo

Noma: Na Duƙe Tsohon Ciniki

Aikin gona shi ne dukkan abin da ya shafi Noma da Kiwo, wanda idan aka faɗaɗa shi zai zama ke