Ita dai wannan dabbar ana mata laƙabi da sunaye mabambanta kamar; Polecat Afrika, Zoril, Zorille, Zorilla, Cape Polecat, da kuma African Skunk.
Sukan kai tsayin santimita 29-39 (inci 12-16), da farar Jela mai tsayin 21-31 dogo ne kuma Baƙi, amma akwai farare masu ratsin Fari da Baƙi. su na rayuwa tsawon watanni 160.
Saboda yanayin rayuwarsu, da yawan mutane ba su taɓa ganin wannan dabbar ba, amma sunanta ya shahara.
Da Hausa ana kiransa da Bodari da turanci kuma Zorilla ko Skunk. Akwai sama da jinsi 10 na wannan dabba da ke rayuwa a Duniya.
Su na cin Abinci da yawa daga dangin ƙwari, Nama, da ƴaƴan Itatuwa, Ƙwai da mushe. Saboda ba su jin dafin Maciji, su na cin sa da yawa kuma su na son Zuma sosai, hakan tasa suke ziyartar inda suke.

Duk wanda yasan tarihin Ƙasar Hausa yasan cewa, ana danganta wannan Dabba da tusa amma ba haka abin yake ba. Dangin Dabbobi irin su Zaki da Damisa su na yin fitsari na wani sinadari da ke nuna cewa, nan wajen mallakar su ne, (territory marking) a turance.
Kamar yanayin haka, shi Bodari ya na fitsarin sinadarin ‘sulphur’ ne, lokacin ya fuskanci barazana daga abokan gaba domin kare kansa. Wannan sinadarin shi ne mai matsanancin wari wanda ana iya jinsa har fiye da tsawon kilomita biyar.
Wannan sinadarin ya na da ƙaiƙayi, da raɗaɗi, kuma ya na haddasa makanta na ɗan wani lokaci, haka ma ya sa ko manyan Dabbobi a Dawa suke ba shi girma idan sun yi gamo don zaman lafiya.
Bodari, Dabba ne mai son yawo da Dare ko Sassafe, ko lokacin da duhu ya fara shiga.

Ya na da matuƙar ƙarfin Hanci, amma ba ya gani sosai. Idan kai ma’abocin tafiya ne da safe wataƙila ka taɓa ganin mushensa Mota ta take shi saboda rashin ganinsa sosai.
Lokacin kiwo yawanci su na yi ne a cikin Bazara, kuma matansu su na haihuwar ƴaƴa biyu zuwa biyar.
JIBRIN IBRAHIM GOMA
18/12/2024Nayi matukar farinciki da labari na Bodari
Salahuddeen Muhammad
18/12/2024Madalla, muna godiya da kasancewaku tare da mu. Haka nan, muna marhaba da ra’ayoyinku a koyaushe.