Wannan Maƙala ce da ta yi bincike tare da jin ta bakin masana kan yankin da kuma wasu mutane da suka taɓa keta wannan Hamada mai matuƙar girma.
Gabatarwa
Hamadar Sahara ita ce waje na uku mafi girma a Duniya da mutane ba sa rayuwa a cikinsa, ba ya ga Antarctica da kuma Arctic. Sai dai ita Sahara, ita ce waje mafi tsananin zafi a ban ƙasa, yayin da ‘Antarctica’ da kuma ‘Arctic’ kuwa suka kasance masu tsananin sanyi.
Girmanta ya kai nisan kilomita Miliyan 9.4, kusan kashi ɗaya bisa na uku na girman nahiyar Afirka, wato ke nan kusan girman ƙasar Amurka da ta haɗa da Alaska da Hawaii.
Sahara ta ɗauki kusan kashi 30% cikin 100% na dukkanin ƙasashen da ke Afirka. Kuma Sahara ta na tsakiya ne a Afirka, kuma wuri ne da ke samun ƙarancin ruwa.

Wasu masu yawon buɗe ido a yayin da Al’muru ta gabato a Hamadar Sahara |Hoto: BBC
Muhimman Bayanai Kan Sahara
- Yanki Mafi Tsananin Zafi a Duniya
- Shekarun samuwarta; Miliyan 100.
- Yawan ƙasashen da Sahara ta ratsa; 11.
- Girmanta; Kilomita Miliyan 9.4.
- Ma’aunin zafi na celsius; 47-50.
Bayani: Farfesa Maharazu Yusuf Bebeji BUK
Asalin Sahara

Asalin sunan Sahara ya samo asali ne daga harshen Larabci wato ‘Sahra.’ Sahara ta ƙunshi mafi yawancin yankin Arewacin Afirka da ke kan iyaka da yankin Sahel da kuma ƙasashen Kudu da Sahara.
Ƙasashen Sahara sun haɗa da; Aljeriya da Chadi da Masar da Libiya da Mali da Sudan da Tunisiya da Murtaniya da Nijar da kuma ƙasar Yammacin Sahara.
Wani masanin yanayin ƙasa Farfesa Maharazu Yusuf Bebeji, na Jami’ar Bayero, Kano, ya ce bincike ya nuna cewa, a da can shekaru aru-aru wannan yankin ba Hamada ba ce.
Ya ce, wasu masu bincike sun samu wasu abubuwa da suke nuna cewa, da can ita Sahara wuri ne da ke da danshi da Koguna, amma samuwar yawaitar mutane a Afirka ne ya sa ruwa ya janye a wajen.
“Masana sun ce, wannan ya faru ne fiye da shekaru Miliyan ɗari,” in ji shi.
Ya ce, masu bincike sun ce, an samu Kwale-Kwale a sahara sannan an haƙo manya-manyan halittu kamar ‘Dinasours’ da aka tsinto a Sahara, wanda ke nuna a can shekaru miliyoyin da suka gabata babu Sahara.
Farfesa Maharazu ya ce, “Kuma ‘Dinasour’ ba ya rayuwa sai wuri mai dausayi, kuma an same shi ne a yankin Agadez.” na ƙasar Jamhuriyar Nijar.

Yawanci gine-ginen ƙasa ne a yankunan daji na Sahara. |Hoto: Getty Images
Shin Asalin Sahara, Teku ce ta Ƙafe?
Masanin ya ce, Sahara ba Teku ba ce ta ƙafe, domin Sahara da muke da ita ta na da tudu, kuma ya fi girman Najeriya wadda ke nuna cewa ba Teku ba ne.
Akwai wani ɓangare wadda ya yi ƙasa da ake zaton cewa an samu Tafkuna kamar Tafkin Chadi da ake tunanin sun ajiye Ruwa.
Sai dai ya ce, faruwarta, shi ne wurin da ke samun ƙarancin ruwa.
“Wuri ne da Iska ke tashi, ba a samun ruwan sama, sai gefenta ne ake samun sau ɗaya tak a shekara. Wani lokaci a wata ɗaya tak.”
Amma masanin ya ce, akwai lokacin da take da dausayi, kuma kamar yadda in da ba Sahara ba yake da dausayi akwai kuma lokacin da yanayin yake komawa na Sahara.
Shin Tun Asali Akwai Sahara?
Farfesan ya ce, da can akwai Sahara, shekaru aru-aru tun kafin zuwan mutane.
“Shi ɗan’adam ba a daɗe da samunsa ba a Duniya” in ji masanin.
Ya ce, kamar wasu garuruwan Arewacin Najeriya, a shekaru aru-aru can baya Sahara ne.
Bincike ya nuna cewar, daga baya ne yankin ya samu daga Sahara kamar yadda ake gurgusar da Teku.

Sahara a lokacin da ta koma dausayi. |Hoto| BBC
Ƙasashen da Sahara ta Ratsa Sosai a Ƙasashen Nahiyar Afirka
- Kashi 30% girman yankin da Sahara ta mamaye
- Kashi 95% yawan Hamadar da ke Masar (Egypt).
- Kashi 60% yawan Hamadar da ke Aljeriya (Algeria).
- Kashi 60% yawan Hamadar da ke Jamhuriyar Nijar (Niger Republic).
Bayani: Farfesa Maharazu Yusuf Bebeji BUK.
Shin Hamadar Sahara da Ƙasashe Nawa ta Haɗa Iyaka, Sannan Yankin Wace Ƙasa ce ta fi Yawa?
Ilimin yanayin ƙasa ya nuna cewa, yankin Sahara ya yi iyaka da Tekun Atlantika daga Yamma, da Kogin Maliya daga Gabas, da Bahar Rum daga Arewa sannan daga Kudu ta yi iyaka da yankunan da ke da Ciyayi amma ba Bishiyoyi da yawa wato; Sahel Savana.
Wannan ƙasurgumin waje ya ratsa ƙasashe 15 na Afirka da suka haɗa da Aljeriya da Chadi da Masar da Libiya da Mali da Mauritaniya da Moroko da Nijar da Yammacin Sahara da Sudan da kuma Tunisiya.
Kuma daga cikinsu an bayyana cewa, ƙasar Masar ce ta fi yawan Sahara. Wato ita ce ta fi yawan girman Hamadar Sahara.
“Kashi 95% na Masar kusan Hamada ce, sai Aljeriya da kuma Nijar, wacce kashi suttin cikin ɗari na ƙasar Hamada ce.” in ji Farfesa Maharazu.

Waɗanne Irin Halittu da kuma Tsirrai ke iya Rayuwa a Hamada?
Masana sun ce, akwai Halittu da ake gani a Hamada, waɗanda ake ganin Allah Ya ba su kariya da za su iya rayuwa ba tare da Ruwa ba.
Halittun su na da abin da za su iya ajiye Ruwa, irinsu Gawo da Kafto waɗanda za su iya zama tsawon lokaci ba tare da sun damu da Ruwa ba.
A ɓangaren tsirrai akwai Dabino da ke da saiwa mai zurfi, ana samun sa ne a Hamada.
A ɓangaren Dabbobi, akwai Raƙumi wanda ake kira “Jirgin Hamada” da kan ɗauki kwanaki kamar mako ɗaya ko kwana 10 ba tare da ya sha Ruwa ba.

Ana yawan ganin Raƙumi wanda ake kira “Jirgin Hamada” da kan ɗauki kwanaki kamar mako ɗaya ko kwana 10 ba tare da ya sha ruwa ba. |Hoto: Getty Images
Akwai Ƙadangaru, da suke juriyar wahala, da za su iya ɗaukar lokaci ba su nemi Ruwa ba. Masana sun ce, dangin Ƙadangare da Macizai za su iya jure wa ƙarancin ruwa a Hamada.
Farfesa Maharazu ya ce, duk da cewa akwai wurare masu zurfi da za a iya samun Ruwa a Sahara, amma halittun su na da wata halitta da Ubangiji ke kare su da zafin Rana na Hamada.
Ya ce, kamar yadda ake samun halittun Ruwa, haka akwai halittun da ba za su iya rayuwa ba sai a wannan yanayi na Sahara. “Haka Allah Ya yi su.”
Wani mutum ɗanƙasar Nijar Abu Ila, da ya taɓa ratsa Sahara don zuwa Libiya ya ce, ya ga Tsuntsaye nau’i uku, amma bai ga Tsirrai ko Bishiyoyi ko Gini ba.
Yanayin Sahara
Hamada ta na da nau’i biyu, ta na da ƙarancin Ruwa da kuma Zafi. Farfesa Maharazu ya ce, a lokacin Rana, Zafi a Sahara yakan kai ma’aunin ‘celcius’ arba’in da bakwai zuwa hamsin (47-50).
Da Dare kuma yanayin zai koma na Sanyi, In da ma’aunin zai sauka ya dawo zuwa 15°.
Ya ce, halittun duk da ke rayuwa, Allah zai ba su juriyar Zafi da kuma sanyin Hamada.

Dubban ƴan ci-rani ne ke tafiya Turai daga Afirka inda su kan bi ta Agadez, kuma su na tafiyar kwana 40 a Sahara. |Hoto: Getty Images
Samun Ruwan Sama a Sahara
Abu Ila ya ce, a kwanakin da suka yi su na tafiya “An yi ruwan sama jefi-jefi.”
Masana sun kasa Hamadar Sahara kashi biyu – akwai Aric inda ake samun ruwan sama, waɗanda za su iya yin Noma. Akwai kuma inda ba a samun ruwa, da ake kira ‘Hypa Aric’ a Turance, kamar yankin Arlit zuwa Aljeriya, inda ake iya shafe shekara ba a yi Ruwa ba.
Farfesa Maharazu ya ce, akwai wani wuri a yankin Masar da aka ce an yi shekaru sama da arba’in ba a yi Ruwa ba. Haka kuma ya ce, a wuraren Kudancin Agadez ana iya shuka saboda sukan samu Ruwa.
Sai dai Abu Ila ya ce, a tafiyar da ya yi a cikin Sahara bai ga ko da tsiro ɗaya da ke nuna alamar ana iya Shuka a wurin ba.”

Abin Da Ke Kawo Sanyi da Zafi?
Masanin yanayi Farfesa Maharazu ya ce, yawancin Makamashi da muke samu daga hasken Rana ne. Kuma Hamada babu Bishiyoyi, sai Rairayi kuma a haka Rana takan zo ta faɗi.
Ya ce, ba kamar yankin da ba Hamada ba inda Itatuwa da Bishiyoyi ke riƙe zafin da Rana ta buga, amma a Hamada babu.
Dalilin Da Ya Sa Sahara Ke Yin Sanyi
Farfesa ya ce, Gajimare yakan riƙe zafin da Duniya ta ɗumama da shi daga hasken Rana, amma Hamada tun da babu wannan gajemaren, to a buɗe sama take.
“Idan tiririn ya bugi ƙasa nan da nan sai ya huce ya yi sama sai wuri ya yi Sanyi,” in ji shi.
Ana Samun Ruwan Sha a Sahara?
Abu Ila ya ce, a tafiyar da suka yi cikin Sahara dai da guzurin ruwan shan su suka tafi, kuma rijiya biyu kawai suka gani a cikin Sahara.
“Rijiyoyin kuwa su ne wacce ake cewa ‘metal’ wacce take a jikin gini kuma ba Ruwa a cikinta, sai kuma Ashugur ita kuma akwai ruwa a cikinta,” in ji Abu Ila.

Masana sun ce, an haƙo manya-manyan halittu kamar Dinasours da aka tsinto a Sahara a can baya. |Hoto: Getty Images
Ta Ya Ya Hamada Ke Kwararowa?
Masu bincke sun tabbatar da cewa, lallai Hamada ta na gurgusowa, saboda sauyin yanayi. Yawan ruwan da ake samu ya ragu, wanda hakan ke nuna gurgusowar Hamada.
Al’umma ta yawaita, an mayar da wurare wurin Noma da Kiwo, wanda ke haifar da kwararowarta.
Nijar ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fuskantar barazanar kwararorwar Hamada, ta fi ɗaukar matakan kariya.
An ɓullo da wani tsari na sassaben zamani, inda ake koyawa Manoma yadda ake sassabe ba tare da ƙwalƙwale komi ba, sai dai a yi sama-sama domin daƙile Kwararowar Hamada.
Ya Zurfin Yashin Hamada?
Masana sun ce, akwai Hamada mai Tsakuwa da Duwatsu, akwai kuma mai Ƙasa.
Kuma a cewar Farfesa Maharazu, Hamada mai tsakuwa ta na da zurfi, amma ya danganta da yawan ƙasar da Iska ta tara.
Ya ce, yawanci Iska ce ta ke tara ƙasa a Sahara. Kuma yawanci zurfin yakan kai mita 10 zuwa mita 20.
“Mun yi wani bincike a Arewacin Ƙaramar Hukumar Yusufari ta Jihar Yoben Najeriya, akwai wadda za ka samu ta kai zurfin mita 50 zuwa 100,” in ji masanin.

Garin Arawan ke nan da ke Arewacin Timbuktu na Mali kafin Sahara ta gurgusa ta rufe wajen, a shekarar 2002. |Hoto: Getty Images
Akwai Arzikin da Ake Samu a Sahara?
Masana sun ce, akwai arziƙi sosai a yankin Hamadar Sahara a Afirka.
Kuma masanan sun ce, rashin Ruwa ba zai hana samun arziƙi ba ko da ƙura da iska sun ruguza ko sun lulluɓe Duwatsu tsawon shekaru. Amma ba zai hana a samu Ma’adinai ba, domin an samu Man Fetur a Nijar da Iskar Gas.
Akwai kuma Zinariya da ake haƙo wa a yankin Agadez da kuma arziƙin Uranium.
Akwai kuma ma’aidanai da dama a yankin Aljeriya da Nijar da Masar.