Dabbobi

Ɗankunya: Ɗaya Daga Cikin Dabbobi Mafi Muhimmanci a Duniya

Wannan dabbar ita ake kira a Hausa da Batoyi, wasu kuma su na kiranta da Ɗankunya (Pengolin).

Bugu da ƙari, ana kuma samun wannan dabbar a Nahiyar Asiya da kuma yankin Kudu da Hamadar Sahara a Afirka.

An yi imanin cewar, su ne mafi yawan fataucin Dabbobi masu shayarwa a Duniya.

Ana farautar dubun-dubatar Ɗankunya kowace shekara, ana kuma kashe su saboda amfaninsu na magungunan gargajiya da Ƙasar Sin ke yi da kuma cin namansu. Sannan, ana amfani da fatar wajen ƙera Rigunan Silke na harsashin Bindiga (bulletproof).

Akwai nau’ikan Ɗankunya har guda takwas. Ana samun huɗu a Nahiyar Asiya; Sin, da Sunda, da Indiya, da Philippine. Hukumar IUCN ta bayyana na Ƙasar Philippines a matsayin mafi hatsarin gaske.

Dukkan nau’ikan takwas su na fuskantar raguwa saboda yawan haramtacciyar farautarsu da ake yi domin fatauci.

Wasu daga cikin nau’ukan Ɗankunya

Shekaru da dama, nau’in Ɗankunya na yankin Asiya su ne farkon abin da masu farauta da masu fatauci suke kai wa hari.

Amma yanzu da adadinsu ya ragu, masu fasa-ƙauri na ƙara karkata zuwa ga na Nahiyar Afirka.

An tattara cewa, a cikin watan Afrilu na shekarar 2019, Ƙasar Singapore ta kama jigilar tan 14.2 da kuma jigilar tan 14 na ma’aunin Ɗankunya, daga ƙiyasin 72,000 wadda sun fito ne daga Najeriya.

A shekara ta 2016, Ƙasashe 186 da ke cikin yarjejeniyar Cinikayyar Ƙasa da Ƙasa ta Namun Daji (CITES), sun yi yarjejeniyar da ke daidaita cinikin Namun Daji na Ƙasa da Ƙasa, inda suka kaɗa ƙuri’ar haramta cinikayyar dabbar.

Jami’an hukomomi a yayin da suke bincike kan wasu Ɗankunya da aka yi fasa-ƙauri

Ɗankunya, sun kasance masu kaɗaita al’amuransu da rana, wadda galibi sun fi yin walwala da daddare.

Yawancin su na rayuwa ne a doron ƙasa, amma wasu kamar; ‘Pangolin black-bellied‘ su na hawan Bishiyoyi.

Sun kasance da ɗan girma da kuma tsayi fiye da ƙafa huɗu. Su na rufe da kariya, kamar dai farcen ɗan’adam, wadda ake masu laƙabi da “Scaly Anteater.”

Lokacin da aka matsa masu, su na mirginawa kamar ƙwallo, kuma su na iya sakin wani ruwa mai wari daga gindin wutsiyarsu a matsayin hanyar kariya.

Ɗankunya su na da dogon Hanci har ma da harsuna masu tsayi, waɗanda suke amfani da su don ƙwanƙwasa Tururuwa da suke tonowa daga Tudu ko Shuri da faratansu masu ƙarfi. Bugu da ƙari, su na iya rufe Hanci da Kunnayensu don hana Tururuwa ko Ƙwari shiga a lokacin da suke ci.

Ko da yake sun fi kamanceceniya da kuma ɗabi’a irin ta dabbar ‘Anteaters‘ da ‘Armadillos.’ Ɗankunya sun fi kusanci da Maguna, da kuma Karnuka a fannin tarayya.

Ana haihuwar jarirai da kariya (scale) mai taushi wadda bayan kwana biyu ya ke yin tauri, inda suke hawan wutsiyar iyayensu har sai an yaye su a kusan watanni uku. Yayin da kuma suke isa shekarun girma (balaga) a cikin shekaru biyu.

Girmansu ya na kai inci 45, tsayi kuma 4.5, nauyi kuma 4 zuwa fam 72.

Ana amfani da gurzin jikinsu domin yin ababe da dama kamar su; Farcen hannu, Gashi, da Ƙawo. Har ila yau, gurzin jikin Ɗankunya kamar ƙahon Karkanda ne, ba su da tabbataccen amfani a matsayin magani a hukumance, amma duk da haka ana amfani da su a cikin magungunan gargajiya na Ƙasar Sin da Vietnam don taimakawa rage cututtuka irinsu, ciwon Huhu da dss.

Haka nan, idan aka busar ya zama hoda, za a iya juya shi zuwa ƙwayoyin magani na amfani.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Dabbobi

Gwaggon Biri Mafi Tsufa a Duniya ta Cika Shekaru 67

Gwaggon birin da ta fi tsufa a duniya, Fatou, ta cika shekaru 67 a Duniya a yayin da take tsare.
Dabbobi

Rikiɗar Halittun Ruwa Zuwa na Ƙasa

Daga Muhammad Cisse Masana juyin halitta, sun yarda da cewa, halittun ruwa sun rikiɗe sun koma halittun da ke tafiya