Gwaggon birin da ta fi tsufa a duniya, Fatou, ta cika shekaru 67 a Duniya a yayin da take tsare.

Asali daga Yammacin Afirka aka ɗauke ta zuwa Faransa a shekarar 1959, amma daga baya aka sayar da ita ga wani Gidan Namun Daji na Berlin da ke Jamus, inda take zama a can tun wancan lokacin.

Kamar yadda Kundin Bajinta na Duniya, (Guinness World Records) ya bayyana. An yi amannar cewa, aƙalla shekarunta biyu kacal a Duniya a lokacin da aka kai ta Gidan Ajiyar Namun Dajin a watan Mayu, na shekarar 1959.
