Al'ada

Yadda Bikin Kamun Kifi da Al’adun Gargajiya na Ƙabilar Nwonyo Ya Gudana

Shi dai wannan biki ya na gudana ne a Jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya, wadda ƙabilar Nwonyo ke gudanarwa domin ɗabbaƙa al’adunta.

Haka nan, bikin ya kasance abin sha’awa saboda baje-kolin al’adu daga ƙabilu daban-daban da suke halarta, kuma haƙiƙa wuri ne ga masu yawon buɗe ido.



Bugu da ƙari, bikin ya samu halartar mutane daga sassa daban-daban na ƙasar da kuma wasu ƙasashen Afirka. Haka kuma, an yi baje-kolin al’adu daga ƙabilu daban-daban, inda aka yi; Tseren Kwale-Kwale, wasan ninƙaya da kamun Kifi, da dai sauransu.



Har ila yau, a ɓangaren Su an kafa tarihin kama Kifi mai nauyin kilogiram 170 wadda Malam Hudu Yakubu ya lashe. Kifi na biyu mafi girma ya kai kilogiram 150, yayin da wadda ya yi nasara a matsayi na uku ya na da nauyin kilogiram 120.

Kifi mafi girma da aka kama a gasar ta bana, mai nauyin kilogram 170. |Hoto: Agbus Kefas Media

Har wa yau, bikin ya kasance ƙarƙashin jagorancin Gen. TY Ɗanjuma (Rtd.) da Gwamnan jihar Dr. Agbu Kefas, da kuma Mai Girma Gwamnan Jihar Adamawa Umaru Fintiri, a matsayin Babban Baƙo na Musamman.



“Gwamnatinmu ta himmatu wajen samar da adalci, jituwa da haɗin kai don ci gaban al’umma. Wannan biki shaida ce ga kyawawan tsarinmu a kan zaman lafiya.” In ji, Gwamna Agbu Kefas.

Daga ƙarshe, Jakadan jamhuriyar Namibiya a Najeriya, Humphrey Joseph, ya yaba da yadda bikin ya gudana. Ya kuma yi alƙawarin ƙara tsawaita shirye-shiryen Namibiya don yin aiki tare da jihar don haɓaka Yawon Buɗe Ido.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Al'ada

Bikin Guérewol na Ƙabilar Wodaabe a Jamhuriyar Nijar

Bikin Guérewol wata gasa ce ta al’adar neman aure da ake yi a kowace shekara tsakanin al’ummar Wodaabe Fula na
Al'ada

Shin Kayan Lefe Kyakkyawa ko Mummunar Al’ada Ce?

Abdulmutallib A. Abubakar malami a sashen nazarin aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri da ke jihar Barno kuma mai sharhi kan