Chabbal Waadi, (wadda aka fi sani da Dutsen Mutuwa), ya na cikin Najeriya kuma, ya na da tsayin mita 2,419 (7,936 ft), sama da matakin Teku, kuma shi ne Tudu mafi girma a ƙasar da ma Afirka ta Yamma gaba ɗaya.

Ya na cikin Jihar Taraba, Arewa maso Gabashin ƙasar, kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Kamaru, a gefen Gandun Dajin Gashaka Gumti, da ke yankin Plateau na Mambilla.

Bugu da ƙari, ya kasance wani yanki na tsaunukan Bamenda, da Alantika, da Mandara na Najeriya da Kamaru.

Chappal Waddi, Tsauni ne mai ban sha’awa kuma masu hawan dutse, da masu bincike da yawon buɗe ido kan ziyarci wurin.

Har ila yau, wani yanki ne mai mahimmanci na al’ummomin da ke kewaye da dutsen, waɗanda akasarinsu makiyaya ne da suka dogara da wurin don ciyar da dabbobinsu.

Mafi yawan lokaci yanayin wurin ya kasance na hunturu, wadda hakan ya sa mutane kan ziyarci wurin daga sassa daban-daban na duniya domin yawon shaƙatawa da ɗebe kewa.
