Wannan shi ne karo na biyar a jere da William Masvinu ke lashe gasar mutumin da ya fi kowa muni ( Mr Ugly) a ƙasar, kuma ya ce nasarar ta ba shi damar yin fice da har yake samun kuɗaɗe daga tallace-tallace.
A cewarsa, ya na alfahari da muninsa, kuma ya na son ya lashe kyautar na matakin ƙasa da ƙasa.

William Masvinu, wadda ya lashe lambar yabo na ‘Mutum mafi muni a Zimbabwe.’ |Hoto: Africa Facts Zone
Bugu da ƙari, masu shirya gasar sun bayyana cewar, su na son mutane masu muni su sami dama irin na kyawawan mutane.

William Masvinu, a lokacin da yake karɓar lambar yabo. |Hoto: Africa Facts Zone
Daga ƙarshe, wadda ya lashe gasar ya na karɓar Dala 500 da Saniya guda.
📷 Africa Facts Zone