Jiya Da Yau

Sarauniya Abla Pokou: Uwar al’ummar Baoule na Côte d’Ivoire

Sarauniya Pokou, ko Awura, Aura, ko Abla Pokou (ta yi sarauta c. 1750 – c. 1760) ita ce Sarauniya kuma ta kafa ƙabilar Baoule a Yammacin Afirka (Ivory Coast), yanzu Côte d’Ivoire,

Ta yi sarauta a kan wani reshe na Daular Ashanti mai ƙarfi, yayin da yake faɗaɗa Yamma. Ƙabila ta al’ummar Akan, mutanen Baoule a Yau su na ɗaya daga cikin manyan kabilu a Côte d’Ivoire, ta zamani.

Abla Pokou, Sarauniya ce ta Akan wadda ta jagoranci jama’arta daga Ƙasar Ghana ta yanzu zuwa Côte d’Ivoire, a 1770, tarihi ya nuna ta sadaukar da ɗanta ga Iskoki domin mutanenta su ƙetara Kogi.

Mene ne Matsayin Abla Pokou a Cikin al’ummar Ashanti?

An haifi Abla Pokou a matsayin Gimbiya a farkon ƙarni na 18. Ƴa ce ga ɗan’uwan Sarki Osei Tutu, wanda da shi aka kafa Daular Ashanti da ta zama Ƙasar Ghana a wannan zamani.

A lokacin da ya rasu rikicin shugabanci ya ɓarke aka kashe Dakon ɗan’uwan Abla Pokou wanda ya na daga cikin masu gadon Sarauta. A bisa tsoron rayuwarta da danginta Abla Pokou ta gudu.

Wane ne ya yi wa Abla Pokou Rakiya a Lokacin da ta Tsere?

Abla Pokou ta gudu tare da dukkan mutanen da suke biyayya ga Dakon wanda kuma ya ƙi amincewa Opokou Ware ya gaji Sarauta. Ta haɗa gagarumar runduna ta kuma jagoranci tawagar zuwa inda a yanzu Ƙasar Côte d’Ivoire ta ke.

Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: The African History

Ta ya ya Abla Pokou ta je Côte d’Ivoire?

Tarihi ya ruwaito cewar, lokacin da suka tsere, Sarauniya Abla Pokou da magoya bayanta sun kasa ci gaba yayin da suka isa kogin Comoe. Comoe dai nan ne kan iyaka tsakanin Ƙasar Ghana ta yanzu da kuma Côte d’Ivoire.

Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: The African History

Kogin ya cika maƙil saboda ruwan sama da ake yi akai-akai, a saboda haka ba za su iya tsallakawa ba. Sarauniya Abla Pokou ta shawarci Bokan da ya yi musu rakiya, sai ya ce aljanun Kogi sun buƙaci a sadaukar da jariri. Sai Abla Pokou ta jefa ɗanta cikin kogin kuma ya ɓace a kogin da ke ƙara yin toroƙo.

Wannan hoton zane ne aka yi kamar yadda aka bayanna a tarihi, amma ba hoton zahiri ba ne. |Hoto: The African History

Duk da haka a cewar wani ƙaulin na tarihi, wani abin mamaki ya faru, Bishiyoyin da ke Gaɓar Kogin sun ranƙwafa suka yi gada. Wani ƙaulin kuma ya ce, manyan Dorinar ruwa ne suka fito suka yi jerin gwano suka yi musu gada yadda Abla Pokou da ƴan rakiyarta za su iya wucewa.

Bayan da suka tsallaka, Abla Pokou ta rusa kuka ta na kuwwa ta na cewa, “Bâ wouli.” Ma’ana; “Jaririn ya mutu.” Wannan kalmar mai yiwuwa ita ce ta samar da sunan Baoule (“Ba wouli”) al’ummar da a yanzu ta ke zaune a Côte d’Ivoire.

Shin Tabbas Abla Pokou ta Sadaukar da Ɗanta a Cikin Kogi?

“Sarauniya Abla Pokou mai yiwuwa ba ta sadaukar da jariri ba,” a cewar farfesa Kouamé René Allou kamar yadda ya shaidawa DW.

“Akwai wasu lokuta a cikin shekara da kogin Comoe kan janye yadda za ka iya taka Duwatsun da ke ƙarƙashin Kogin ka ƙetara.” Mai yiwuwa wannan shi ne abin da Baoule ta yi a cewar wasu majiyoyi.

Ina ne Haƙiƙanin inda Abla Pokou ta Zauna a Lokacin da ta isa Côte d’Ivoire?

Sarauniya Abla Pokou ta zauna a yankin Namounou da ke Bwake kusa da kauyen Akawa. Namounou na nufin “Kula da uwa,” ya kamata mutane su kula da Abla Pokou a wannan wuri.

Abin takaici, an ƙauracewa ƙauyen Namounou bayan da sarauniyar ta rasu. An binne ta a cikin kogin N’draba. Akawa Boni, wanda ya gaje ta ya tashi ya koma Sakassou da zama.

Ya ya ake Tunawa da ita a Yau?

Har yanzu ana tuna Sarauniya Abla Pokou ta hanyar Adabin Baka da kuma Adabin Zube a Ghana da Côte d’Ivoire, sai dai kuma ya na da wuya iya samun hotunan Abla Pokou.

Babu wani gini ko gidan tarihi da aka sanya wa sunanta baya ga wani mutun-mutumin ƙarfe da ke dandalin ‘République’ da ke Abidjan. Sai dai kuma a fagen kayan ƙawa wasu masu tsara kayan kwalliyar sun samar da salo masu yawa ɗauke da sunan shahararriyar sarauniyar Abla Pokou.

Madogara

Shawarwari ta fannin kimiyya ga wannan muƙala an same su ne daga masana tarihi Farfesa Doulaye Konaté, Lily Mafela, Ph.D., and Professor Christopher Ogbogbo.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Jiya Da Yau

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne
Jiya Da Yau

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna

Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen