Masarautar Katsinar Maraɗi, babbar Masarauta ce mai daɗaɗɗen tarihi a Jamhuriyyar Nijar inda darajar Masarautar ta tashi daga Sarki zuwa Sultan.
Daga: Awwal Ahmad Janyau
Mafi yawancin al’ummar Masarautar Maraɗi Hausawa ne da kuma wasu ƙabilu na Nijar kuma ta ƙunshi Musulmi da kuma wasu kaɗan mabiya addinin Kirista.
Masarautar Maraɗi ta yi iyaka da yankin Damagaram daga Gabas da yankin Tawa daga Yamma da yankin Agadez daga Arewa, sannan ta yi iyaka da Najeriya daga Kudu musamman Jihohin Katsina da Zamfara da Sakkwato da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Akan yi wa yankin Maraɗi kirari da gidan al’adun gargajiya na Nijar da Cibiyar ilimi kuma cibiyar ciyar da ƙasa saboda harkokin kasuwanci da noman da ake yi a yankin.
BBC ta tattauna da masana tarihi, Farfesa Ado Mahaman shugaban Jami’ar Tawa a Nijar kuma masanin wanda ya yi rubuce-rubuce da dama kan Maradi da masarautar Katsinan Maradi, da kuma Issoufou Habou Magagi malamin da ke kula da gidan tarihi na Jihar Maraɗi.
Kalmar Maraɗi
Duk da ra’ayin manazarta ya bambanta kan asalin tushen kalmar Maraɗi, amma masana tarihi sun ce sunan Maradi ya samo asali ne zamanin mutumin da ya kafa garin.
Malam Issoufou Magagi mai kula da gidan Tarihi na jihar Maradi ya ce, sunan Maraɗi ya samo asali daga kalmar “Muradi” bayan Ɗanfodiyo ya ci Katsina da yaƙi, lokacin da ta watse.
“Sai Ɗan Ƙasawa ya ce – mu tsaya nan kafin muradinmu ya cika mu je mu karɓe birninmu na Katsina – daga kalmar Muradi aka samu sunan Maraɗi,” in ji shi.
Ya ce, sun ci gaba da zama a wurin duk da niyyar zuwa karɓo Katsina saboda sun samu ƙasa ce mai albarka ta noma da Ruwa da Kiwo da Farauta – “Bayan sun samu ƙasa mai albarka sai suka ci gaba da zama har suka dawwama a wurin.”
Amma a nasa ɓangaren masanin tarihin Masarautar Katsinar Farfesa Ado Mahaman ya ce, sunan Maraɗi ya samo asali ne daga Sarauta na wani yanki a Katsina.
Ya ce, sarautar ta na ƙarƙashin Katsina ne kuma wanda ke riƙe da sarautar shi ake kira “Maraɗi.”
Ya ce, akwai unguwar Maraɗawa da sarkin ke da ikon yankin amma kuma ya na ƙarƙashin Katsina kafin jihadin Usman Ɗanfodiyo.
“Sarauta ce ta Ƙaramar Hukuma da ke ƙarƙashin Sarkin Katsina na gidan Korau.”
Tushen Masarautar Maraɗi da Kafuwarta

Hoto: Issoufou Habou Magagi
Masana tarihi sun ce, Masarautar Maraɗi ta kafu ne tsakanin shekara 1807 – Kuma Farfesa Ado da Malam Issoufou sun ce, Ɗan Ƙasawa ne ya kafa Daular Katsinar Maraɗi.
Farfesa Ado ya ce, gidan sarautar Ɗan Ƙasawa ta samo asali ne a wajajen ƙarni na 17 daga cikin babbar Katsina. Kuma Katsinawa ne ke Sarautar Maraɗi.
“Jikokin Korau ne Maraɗi, su suka kafa garin tun garin ya na ƙarami suka mayar da shi babban birni da ake kira Katsinar Maraɗi,” in ji shi.
Ya kuma ce, Gidan Korau ne suka mayar da yankin Maraɗi Cibiyar kasuwanci a Nijar – suka kuma tallafawa Jamhuriya ta farko har da Turawan Mallaka da kuɗin gudanarwa saboda noman Gyaɗa da suke.
“Da kuɗin Gyaɗa da Kiwo suka taimaka wajen tafiyar da Gwamnati har zuwa lokacin da aka samu arzikin ‘Uranium’ a 1971.”
Me ya sa ake Cewa Sarkin Katsinar Maraɗi?
Kamar yadda bayani ya gabata kan tushen Maraɗi, Masana sun ce waɗanda suka gujewa jihadin Ɗanfodiyo ne suka kafa Masarautar Maraɗi.
Kuma duk da cewa, asalin Maraɗi wani yanki ne na Ƙasar Katsina ta Najeriya, amma Masarautar ta fice ne daga ƙarni na 19.
“Wasu Katsinawan Maraɗi a Nijar har yanzu su na ganin Katsina ta Najeriya yanki ne na Masarautarsu,” in ji Farfesa Ado.
Ya ce, tun da Katsina ta rabu biyu, sai gidan Sarautar Korau ya baro birnin Katsina ya dawo ya kafu a Maraɗi – “Shi ya sa ake cewa Sarkin Katsinar Maraɗi ko Katsina ta Arewa ko katsina ta Faransa.”
Issoufou Magagi ya ce, Korau ne ya kafa Daular Katsina ta biyu, baya ga Daular da Koma yau ya fara kafawa a ƙarni na shida wanda ya fara kafa Daular Katsinawa a shekarar 1665.
“Muhamman Korau wanda shi ne asalin Daular Katsinan Maraɗi ya kafa Daularsa ne a 1348. Sannan Ɗan Ƙasawa ya kafa Daular Katsinan Maraɗi a 1820, wacce ita ce Daular Katsinawa ta uku,” in ji shi.
Farfesa Ado ya kuma ce, Maraɗi ta na ƙarƙashin Masarautar Katsina ne tun kafin Jihadi ba ma kafin zuwan Turawa ba wato kafin shekara ta 1807 lokacin da goguwar Jihadi ta ci Katsina.
Kamar yadda ake cewa, “Katsinawa jikokin Korau – To ƴan Gidan Korau ne suka taso suka dawo Maraɗi.”
Don haka a cewar Farfesa Ado, Maraɗi wani yanki ne na Katsina – Kuma Maraɗi da Aguie da Madarounfa da Tessaoua da Dakoro da Korgom da Kanan Bakache duka yankuna ne na Katsina kafin goguwar Jihadi ta raba su.
Sai dai ya ce, Gidan Sarautar Maraɗi ne ya kafa Daular Katsina a ƙarni na 15 bayan saukar Durɓawa wanda ya ba Birnin Katsina ƙofofinta kamar Ƙofar Ƙwaya da Ƙofar Ƙaura da Ƙofar Guga da Ƙofar Marusa.
“Shi ne ya mayar da Katsina Sarkin Kasuwa, ya ba ta jami’o’inta kamar Jami’ar Ɗanmasani da ta Ɗanmarina da ta Ƴan Doto wadda babbar Jami’a ce a Afirka duk da cewa yanzu babu ta.”
Malam Issoufou Magaji ya ce, ana cewa Katsinar Maraɗi don a bambanta da Katsina ta Najeriya wato Katsina ta ƙaya da Katsina ta Maraɗi ta Nijar da ake kira Katsina ta laka. Amma dukkaninsu Katsinawa ne na Nijar da Najeriya.
Kuma kowa mai cin gashin kansa ne babu wanda ke ƙarƙashin wani. Amma su na hulɗa ta Diflomasiyya da bukukuwa tsakaninsu da kuma kuma hulɗar zaman lafiya.
Sarakunan da Suka yi Mulki a Maraɗi

Elh Mahaman Sani Kure – Buzu Ɗan Zambadi – Sarkin da ya fi daɗewa a Masarautar Maraɗin Katsina. |Hoto: Issoufou Habou Magagi
Sarakuna 23 ne suka yi Mulki a Maraɗi. Kuma Ɗan Ƙasawa ne ya fara yin Sarauta wanda ya fara kafa Masarautar.
Sarakunan Masarautar Katsinan Maraɗi su ne:
- Ɗan Ƙasawa 1807 zuwa 1830
- Rauda Magajin Haladou 1830 zuwa 1836
- Ɗan Mari 1836 zuwa 1843/4
- Binoni 1843/4 zuwa 1848/9
- Ɗan Mahedi 1848/9 zuwa 1851/2
- Ɗan Baura 1851/2 zuwa 1852/3
- Baskore Rauda 1852/3 zuwa 1875
- Barmo Ɗan Kasawa 1875/6 zuwa 1879
- Maza Waje Ɗan Ƙasawa 1879/8 zuwa 1882/3
- Malam Ɗan Ƙasawa 1882/3 zuwa 1883/4
- Salau Ɗan Mahedi 1883/4 zuwa 1887/8
- Gulbi Ɗan Kaka Rauda 1887/8 zuwa 1889/90
- Ɗan Dadi Binoni 1889/90 ya yi ƴan watanni
- Mijinyawa Barmo 1889/90 zuwa 1892
- Naibo Ɗan Baura 1892 zuwa 1894
- Daci Binoni 1897 zuwa 1898
- Kure Malam 1897/8 zuwa 1904
- Mahaman Burja Ɗan Mahedi 1920 ya yi ƴan watanni
- Ali Ɗan Kimale Ɗan Baura 1920 ya yi ƴan watanni
- Ɗan Kulodo Malam 1920 zuwa 1944
- Mahaman Ɗan Baskore Kure 1944 zuwa 1947
- Elh Mahaman Sani Kure – Buzu Ɗan Zambadi
- Daga 1947 zuwa 2004
- Elh Ali Zaki – 2005 har yanzu.
Malam Issoufou Magaji ya ce, Sultan na yanzu, Alhaji Ali Zaki ya hau Karaga Mulki a ranar 1 ga watan Oktoban 2005 kuma ya hau ne bayan rasuwar Malam Sani Kure wanda ake cewa Bouzou Ɗan Zambadi wanda ya hau mulki a 1947 kuma ya rasu a 2004.
“Marigayi Buzu ya shekara 57 a kan Karagar Mulki kuma shi ne wanda ya fi daɗewa a Masarautar Katsinar Maraɗi,” in ji shi.
Zamanin Alhaji Ali Zaki ne Sarautar Katsinar Maraɗi ta koma Sultan tun kafa Masarautar.

Sultan Katsinan Maradi Elh Ali Zaki. |Hoto: Issoufou Habou Magagi
Alaƙar Masarautar Katsinar Maraɗi da Daular Usmaniyya
Masana tarihi sun ce, Masarautar Maraɗi ba ta da danganta da Daular Usmaniyya amma sun yi gwagwarmaya daga baya ne suka shirya dab da zuwan Turawa.
Amma Malam Issoufou ya ce, Daular Maraɗi ta yi alaƙa ta yaƙi da Daular Ɗanfodiyo, “Ko da Ɗanfodio ya zo ya same su suna da addininsu na Musulunci.”
Ya ce, Littattafan tarihi su na nuna cewa, addinin Musulunci ya shigo yankin Maraɗi a ƙarni na 11 ta hanyar kasuwanci da ke yi a yankin Sahara inda Larabawa saman Raƙuma suke fatauci tun daga Hamada su ratso yankin Katsina har zuwa Kano.
“Daga lokacin ne ƙarni na 11 ake sa ran addinin Musulunci ya shigo Daular Maraɗi ta hanyar Labarawan da ke zuwa fatauci.”
Malam Issoufou ya ce, lokacin da Ɗanfodio ya zo shi ya na ganin akwai kuskure kan yadda suke gudanar da addininsu wanda ya haifar da matsala tsakanin Katsinawa da Gobirawa.
“Sun yi zargin cewa, Ɗanfodio ya zo ne kawai da burin faɗaɗa yankin shi – shi ne ya fake da Jihadi,” in ji shi.
Masanin ya ce, lokacin da Usman Ɗanfodio ya tarwatsa Katsina sai ya aza Ummaru Dalaje wanda shi kuma ya tura Mani Asha zuwa yankin da yanzu ake kira Maraɗi.
Ya ce, a lokacin Katsinawan Maraɗi sun zargi wakilin na Ɗanfodio da azabtar da su ta hanyar sa su aikin ƙarfi da cin zarafi.
A tarihin a cewarsa, Magaji Halidou wanda shi ne Sarki a Katsinan Maraɗi ya kashe kansa saboda takaicin tarwatsewar Katsina sakamakon jihadin Ɗanfodio.
Wannan ya tilasta wa Ɗan Ƙasawa yin gudun hijira zuwa Damagaran, daga baya kuma ya turo mayaƙansa su kashe Mani Asha kafin ya zo ya kafa Daula.”
“Ya tura manyan mayaƙansa ne guda shida suka yi masa Juyin Mulki – Suka sare kansa suka aika wa Ɗan ƙasawa cewa, sun kashe shi kafin daga nan kuma ya dawo ya kafa Daularsa a Maraɗi.”
Dangantakar Katsinan Maradi da Gobirawa

Marigayi Sultan na Gobir Elh Abdou Bala Marafa. |Hoto: Issoufou Habou Magagi
Maraɗi ta ƙunshi Masarautu biyu masu ƙarfi a Ƙasar Nijar, waɗanda ke da alaƙa ta maƙwabtaka duk da sun yaƙi juna kafin su haɗe kai su na yaƙar wanda ya kawo masu farmaki.
Farfesa Ado ya ce Katsinawa da Gobirawa maƙwabtaka ce tsakaninsu – Su na cikin gungun manyan Sarakunan Hausawa kamar Zazzau da Kano da Daura a Hausa bakwai.
Kilomita bakwai ne tsakanin Katsinar Maraɗi da yankin Tsibiri na Gobirawa inda Jihar Maraɗi ta kasance mai manyan sarakuna biyu masu girman Sultan.
“Da farko Ɗan Kasawa ne ke mulki a Katsinan Maraɗi -Ali Ɗan Yakouba a Tsibiri kuma dukkanin masarautun biyu yanzu Sultan ne,” in ji Malam Issoufou.
Kuma a cewarsa masarautun biyu al’adunsu da addininsu da sana’arsu duka ɗaya – ba su da wani bambanci al’adu tsakaninsu.
Don haka ke nan akwai danganta ta al’ada da addini da kuma harshe da ta kasuwanci a tsakanin Katsinawa da Gobirawa.
Farfesa Ado ya ce, tun can asali Gobirawa maƙwabtan Katsinawa ne kuma akwai wasannin dangi tsakaninsu, amma a cewarsa dalilin sarautar Gobir ne goguwar jihadi ta taso ta ci su da yaƙi.
Su wa ke Naɗin Sabon Sarki?

A zamanin Ali Zaki sarautar Katsinar Maraɗi ta koma Sultan. |Hoto: Issoufou Habou Magagi
Masana sun ce, Sarkin Katsinar Maraɗi Sarki ne mai cin gashin kansa amma bisa tsarin Masarautar Katsinar Maraɗi mutum huɗu ne ke zaɓar sabon Sarki; Galadima da Ƴanɗakan Katsina da Ƙaura da Durɓi.
Yayin da wasu ke cewa, daga Katsina ta Najeriya ake naɗin Sarkin Katsinar Maraɗi, masana tarihin Masarautar sun ce, babu wata alaƙa tsakanin masu naɗa Sarki a Katsinar Maraɗi ta Nijar da Katsina ta Najeriya. Kowannensu mai cin gashin kansa ne babu wanda ke ƙarƙashin wani. Amma su na hulda ta Diflomasiyya da bukukuwa tsakaninsu da kuma kuma hulɗar zaman lafiya.
Malam Issoufou ya ce, Galadama da Ƴanɗakan Katsina a hannun damar Sarki suke yayin da Ƙaura da Durɓi ke hannun hagun Sarki wadanda mayaƙan Sarki ne.
Sannan kafin zaɓen sabon Sarki, su na la’akari da wasu muhimman abubuwa da suke duba wa idan Sarkin da ake son zaɓa ya cika darajar da ake nema.
Ana duba martabarsa da nasara; Sai an duba wanda zai faɗaɗa Daula da samar da yalwa da wadata da hayyafa ta dabbobi da jarumtaka, duk su na cikin alamomin da ake duba wa kafin naɗa sabon Sarki.
Hakan na nufin daga cikin ƙa’idojin zaɓar Sarki sai wanda zai kawo zaman lafiya da wadata da arziki.
Farfesa Ado Mahaman ya ce, idan masu naɗin Sarkin ba su jitu ba su na kiran Liman ya raba masu gardama. Kuma a cewarsa tun daga shekara ta 1445 suke zaɓar sarkin Katsinar Maraɗi har zuwa yanzu.
Ya ce, dukkanin masu naɗin sabon Sarkin Katsinar Maradi su na wakiltar ko wani ɓangare na Katsinawan Maraɗi daga ɓangaren Bayi da gidan Sarauta da Sojoji da Talakawa.
Sannan Farfesa ya ce, ana zaɓar Sarkin Maraɗi ba bisa kama-karya ba, “Dole sai ɗan tsatson Gidan Korau ake zaɓa, ba a zaɓen wanda ba Ɗan gidansa ba.”
Masanin tarihin ya ce, akwai gwaji da ake yi bayan naɗin sabon Sarki kuma idan bai ci gwajin ba za a fitar da shi a saka wani.
“Gwaji na farko sai ya buga Tambura guda 12 inda ya na tsakar bugawa sai Iya ta tambaye shi wani gari ya bata? Amma idan ya kasa bugawa ya na cikin zanzana za a cire shi a sa wani.”
Za a kuma kai shi gidan Galadiman Katsina har tsawon mako ɗaya inda za a sa shi lalle saboda Sarki mijin Ƙasa ne kuma Uban kasa ne.”
“Sannan akwai gwaji na Mari da ake yi wa Sarki – Mai cin sarautar Mari ne zai kama haɓar Sarki ya na marinsa kaɗan-kaɗan.”
“Ya na cewa, manta da abin ake maka kana ɗan sarki, Manta,” in ji Farfesa Ado.