Wata ƴar ƙasar Maroko mai sa Hijabi da aka samar da ita da Ƙirƙirarriyar Fasaha ta yi nasarar lashe Gasar Kyau ta Miss AI ta farko a Duniya.

Macen Ƙirƙirarriyar Fasaha, wadda ta lashe Gasar Kyau ta Duniya. |Hoto: MM News
Kenza Layli, mai faɗa a ji a shafukan sada zumunta kan salon rayuwa, ta yi nasarar ne a zazzafar gasar inda ta doke sama da ƴan takara 1,500 da suka fafata waɗanda su ma duk da AI aka samar da su, lamarin da ya sa ta karɓi kambin da kuma babbar kyauta ta dala 20,000.

Wani launin Hoto na Macen Ƙirƙirarriyar Fasaha da aka wallafa. |Hoto: MM News