Wata ƙwararriyar mai zane-zanen fasaha ƴar ƙasar Azerbaijan mai shekaru 33, mai suna Tünzale Memmedzade, ta kasance mutum na farko a duniya da ta fara rubuta Al-kur’ani mai girma gaba ɗaya a jikin siliki.
Memmezade, ta fara aikin ne bayan ta samu labarin cewar, a baya ba a taɓa rubuta Al-kur’ani da siliki ba.

Littafin Al-kur’ani (mai girma) da Siliki. |Hoto: Life in Saudi Arabia
Wannan aiki dai, ta kammala shi ne a cikin shekaru uku kacal, kuma shi ne irinsa na farko a duniya da aka taɓa gani.

Tünzale Memmedzade, a yayin da take gabatar da kammalallen aikinta na rubuta Al-kur’ani da Siliki, irin sa na farko a Duniya. |Hoto: Life in Saudi Arabia
Har ila yau, ƙirƙira da fasahar zane-zane ta kasance abar tunatarwa a al’adar fasaha ta Musulunci, kuma ta na samun bunƙasa a sassan Duniya.

Tünzale Memmedzade, riƙe da Al-kur’ani wadda ta rubuta da Siliki. |Hoto: Life in Saudi Arabia