Tarihi

Tushen Rikicin Palasɗinawa da Yahudawa

Daga: Muhammad Cisse

Matsalar abin da ya shafi Yahudawa da dangantakarsu da Gabas ta Tsakiya dai wata aba ce mai daɗaɗɗen tarihin gaske, domin kuwa tun kafin haihuwar Annabi Musa Alaihissalam, wato tun zamanin Annabi Ibrahim Alaihissalam. Shi wadda ya yi rayuwa a wannan yanki da yanzu ake kira Palasɗinu da Iraƙi da Siriya da Misra. To, Annabi Ibrahim Alaihissalam, ya na da Ƴaya guda biyu, su ne; Annabi Ishaq, da Annabi Isma’il.

Su Yahudawa su na danganta kansu a matsayin ƴayan Annabi Ishaq, su kuma Palasɗinawa su na danganta kansu a matsayin ƴayan Annabi Ismail. Wannan ya nuna ke nan Yahudawa ma su na da tushe a wannan wuri kamar yadda Larabawa ma suke da shi.

Saboda haka, gaba ɗayansu sun rayu a wannan wuri, rayuwa mai yawan gaske kafin Mulkin Mallaka daban-daban da suka rinƙa faruwa, waɗanda suka zama sanadiyyar fatattakar wannan nan, wannan can, a kai ta dai fuskantar matsaloli. Sai da ta kai a Duniya Yahudawa ba su da matsuguni amma saboda tarihi ya yi halinsa, suka shiga ƙasashe daban-daban na Duniya suka zauna a ciki.

A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, Ƙasar Isra’ila ta shiga ayari ita da Birtaniya da Faransa da kuma ƙawayen su waɗanda suka yaƙi Daular Usmaniyya wadda take da Hedikwata a Turkiyya, wadda kuma take da ƙarfin faɗa aji a ƙasashen Musulmi.

Sakamakon haka sai wannan yanki gaba ɗaya ya zamanto ƙarƙashin Mulkin Mallakar Birtaniya da Faransa da ƙawayen su. Yahudawa kuma a duk in da suke saboda su tsiraru ne, sai suka shiga ƙulle-ƙulle na yadda za su ƙwaci kansu, su kuma mallaki Ƙasar Turawa ta koma hannun su.

Wannan ya sa suka fito da tsari guda biyu; Na farko dai shi ne, tsarin shiga cikin Siyasar Ƙasashen Turawa. Na biyu tsarin kutsawa cikin Tattalin Arziƙinsu. Waɗannan dalilai ya sa a kan dole Turawan suka tafi da su.

Ɗaya daga cikin alƙawarin da aka yi masu saboda gudun mowar da suka bayar har aka ci nasara, shi ne za a sama musu wuri da za su kafa Daular su.

Da farko an yi musu alƙawari za a ba su wuri a Uganda tunda dai Birtaniya ce take Mulkin Mallaka a wannan Ƙasa, sai suka ce a’a, sai dai in da su a addinance, addinin su ya ba su cewar nasu ne, wurin su na alƙawari, wato wannan yanki na Isra’ila ta yanzu. To, haka kuwa aka tsaga wannan wuri, musamman bayan yaƙin Duniya na biyu, lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta zauna da gindinta.

Kasancewar ƙasashen da ke cikin Majalisar a wancan lokaci ba ƴantattu ba ne, aka je aka yi rufa-rufa, aka tsaga yankin Palasɗinu, aka ce to wannan shi ne yankin da ya shafi Yahudawa, kuma su je su zauna a wurin.

A wannan lokaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, idan Yahudawa da Palasɗinawa sun karɓi wannan tsagu da aka yi, in da aka bai wa Yahudawa kashi 55% daga cikin 100% na Palasɗinu, su kuma Palasɗinawan a ka ba su kashi 45% cikin 100%. Sannan kuma aka ce garin Ƙudus saboda mahimmancinsa a dukkanin addinan Musulunci da Kiristanci da kuma Yahudanci, zai kasance ƙarƙashin kulawar ƙasashen Duniya, ba wai ya na ƙarƙashin Palasɗinu ko Isra’ila ba.

A wannan lokaci Isra’ila wadda ita ruwa ne ya ciyo ta, ko me aka miƙa mata za ta karɓa, ballantana a ce an ba ta wannan gagarumar ganima, sai ta ce ta amince. Saboda haka, sai aka yi mata rijista, ta zamanto ɗaya daga cikin ƙasashe mambobi a cikin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Su kuwa Palasɗinawa, suka ce ba su yarda ba, wannan ai cuta ce, a kan me za a tsaga wurinsu a bai wa Yahudawa? Kuma har ma sauran ƙasashen Larabawa suka goya musu baya, suka kuma sha alwashin ƙwato musu ƴancin su, ko da tsiya ko da arziƙi.

To, daga wannan lokaci ne artabu ta fara faruwa, aka ci gaba da rikici da rigingimu har ya zuwa yau (2024).

A wancan lokaci da Palasɗinawa sun yarda sun karɓi wannan kashi 45% a bisa zaluncin da aka yi musu, to da yanzu akwai wani abu mai suna Daular Palasɗinawa ƴantacciya.

Rashin karɓar da suka yi, shi ya sa Isra’ila ta ci gaba da yaƙar su da kuma mamayar sauran yankin na Palasɗinawa, wadda a cikin wannan kashi 45% ɗin, abin da Palasɗinawa suke haƙilon su samu yanzu bai wuce kashi 25% ba, kuma Isra’ilan ta na ƙi ballantana kuma abin da ya shafi Ƙudus ɗin da ta ce, ya zama nata wadda hakan ya sa a kullum ake ci gaba da wannan gwagwarmaya ta Siyasa.

Isra’ila na samun goyon bayan Amurka, su kuma Palasɗinawa ba su da wannan ceto, domin kuwa su kansu Larabawan sun juya musu baya, hasalima dai ta kansu suke yi domin su samu karɓuwa a wajen Amurka, ka da su ɓata mata rai, wadda kuma in dai da haka ne, to ba a san ranar da za a iya kawo ƙarshen wannan matsala ba.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Tarihi

Tarihin Ƙabilar Fulani

Fulani, suna ne na ƙabilar Fulɓe a Hausance. Ƙabila ce wadda take magana da harshen, Fillanci ko Fulatanci, abin da
Tarihi

Yadda Sauyin Yanayi Zai Rusa Wuraren Tarihin Afirka

Tun daga zane-zanen Dutse da ke Kudancin Afirka zuwa Dalar da ke gefen Kogin Nilu, al’ummar da suka gabata sun