Al'ada

Hawan Sallah na Kano Ya Shiga Jerin Bukukuwan Tarihi na UNESCO

Hukumar kula da al’adu da illimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta ayyana Hawan Daba na Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, a matsayin guda daga cikin al’adu da ke da mahimmanci a Duniya.

Daga: Salahuddeen Muhammad

A bikin na Hawan Dawaki wanda aka fara tun ƙarni na 15 a Kano, Sarki, wanda shi ne jagoran addini ya na yin hawa tare da mahaya Dawaki fiye da 10,000 da suka haɗa makaɗa da mawaƙa, inda suke kewaya wasu sassan cikin birnin Kano, birni mafi girma a arewacin Nijeriya, wanda mafi yawan mazaunansa Musulmi ne.

Wannan zanen Fenti ne, na Hawan Sallah A Kano, wadda wani Baturen Ƙasar Amurka John Howard Sanden, ya zana a 2001.

Ana gudanar da bikin ne sau biyu a shekera; Lokacin Ƙaramar Sallah da kuma lokacin Babbar Sallah.

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a yayin da yake jagorantar dubun-dubatar al’umma Hawan Daba. |Hoto: Majida Studio

Ana kuma gudanar da bikin da aka fi sani ‘Hawa Daba’ a garuruwan Musulmai da dama a Ƙasar Hausa.

Fitatccen Bikin mai Ƙayatarwa

Hawan na Sallah ya samo asali ne daga Kano, birni na biyu mafi yawan jama’a a Nijeriya, inda sama da mutum miliyan huɗu ke rayuwa a cikinsa, wanda kuma shi ne birni mafi yawan Musulamai a Nijeriya, sannan Sarkin Kano na ɗaya daga jagororin Musulmai mafiya tasiri a ƙasar.

A yayin da Sarki yake zagawa cikin birnin Kano, a yayin Bikin Hawan Daba. |Hoto: Majida Studio

“Daba biki ne mai ƙayatarwa, da mutunci, da alfahari da kuma nishaɗantarwa,” a cewar Hajo Sani, wacce ke wakiltar Nijeriya a hukumar ta UNESCO, a yayin taron Kwamitin Haɗaka don Alkinta Bukukuwan Al’ada karo na 19 da aka gudanar a Asuncion, babban birnin Paraguay.

“Biki ne na al’ada mai ƙarfin gaske wanda yake haɗo ƙabilu da dama, da suka haɗa da Hausawa, da Fulani, da Larabawa, da Nufawa, da Yarabawa da Abzinawa, abin da yake haɗa su, su zama al’umma ɗaya,”kamar yadda ta bayyana.

A yayin bikin, Sarki, wanda ke yin shiga ta ƙasaita shi ne yake jagorantar hawan, inda Dogarai da Hakimai da Dakaru suke yi masa rakiya a duk lokacin hawan.

A yayin da al’umma suke tarbar Sarki a lokacin Bikin Hawan Daba |Hoto: Majida Studio

Haka nan, Sarkin da sauran mahaya su na kewaya wasu sassan Kano, yayin da jama’a suke yi masa gaisuwa da jinjina tare da nuna masa goyon baya, kamar yadda shafin intanet na UNESCO ya bayyana.

Dubun-dubatar al’umma a yayin Bikin Hawan Daba |Hoto: Majida Studio

A bisa al’ada dai, sarkin Kano na daga jagororin Musulmi mafi girma a Nijeriya bayan Sarkin Musulmi, wanda shi ne jagoran Musulmi a Arewacin Nijeriya.

Sarakunan gargajiya da ke da dama a Nijeriya ba su da wani aiki a Kundin Tsarin Mulkin ƙasar, amma su na da muhimmanci wajen alkinta al’adu, abin da ya sa suke da matuƙar tasiri a ƙasar mafi yawan jama’a a Afirka.

Al’umma a yayin da suke isar da gaisuwa ga sarkinsu, a yayin Bikin Hawan Daba. |Hoto: Majida Studio

Samar da Ayyukan yi

“Wata Masana’anta ce da ke samar da ayyukan yi, da bunƙasa tattalin arzikin jama’a da dama,” a cewar Hajo Sani.

“Bikin ya bunƙasa, inda ya zama fitacce har ma ya zama birane da dama a Arewacin Nijeriya har da Abuja na gudanar da shi,” a cewarta.

Hawan na sallah ya shiga cikin manyan bukukuwan al’ada na Nijeriya da ke jerin bukuwan al’ada na UNESCO, da suka haɗa da bikin al’ada na ‘Sukur’ da ake gudanarwa Jihar Adamawa kusa da kan iyakar Nijeriya da Kamaru, da kuma bikin ‘Sacred Grove’ mai tsarki na Osogbo a jihar Osun.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Al'ada

Bikin Guérewol na Ƙabilar Wodaabe a Jamhuriyar Nijar

Bikin Guérewol wata gasa ce ta al’adar neman aure da ake yi a kowace shekara tsakanin al’ummar Wodaabe Fula na
Al'ada

Shin Kayan Lefe Kyakkyawa ko Mummunar Al’ada Ce?

Abdulmutallib A. Abubakar malami a sashen nazarin aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri da ke jihar Barno kuma mai sharhi kan