Adabi

Rubutu da Karatun Hausa na Ganin Tasku a Zamanin Yau

Manyan ƴan bokon da suka fi yi wa rubutun na Hausa illa su ne ƴan jarida, musamman masu rubutun tallace-tallace.

Daga; Ɗanladi Haruna

Kasancewar Hausa Harshe ne mai sauƙin fahimta gami da basirar da Allah Ya yi wa ƙabilar wajen aro wata kalmar daga wani yaren, su mayar da ita tamkar ƴar asali a cikin yaren, ya sa harshen yake bunƙasa a dukkan faɗin Duniya.

A lokacin da Duniya ke kwance, duk inda Bahaushe ya je yakan fita zakka, kuma idan sun kai su dubu sai ya samu kulawa ta musamman daga masu ‘Jan kunne’ ko Larabawa.

Har yanzu ma kuwa masu fita ƙasashen wajen na shaida mana irin ɗaukakar da suke samu alfarmar yarensu da al’adunsu da addininsu.

To amma fa bunƙasar Hausar na samun naƙasu ta wajen abubuwa da dama. Ɗaya daga cikinsu shi ne yadda rubutun Hausa ke cikin tsaka mai wuya.

“Idan na ce rubutun Hausa, ina nufin rubutun da aka juyar da haruffan boko zuwa Harshen Hausa, ban san yadda Ajami yake ba, watau rubutun Hausa cikin haruffan Larabci, wataƙila shi ma akwai irin waɗannan matsaloli da zan zayyano.”

Yanzu ya zamana cewa, duk wanda yake iya fahimtar yaren ko da ta fuskar saye da sayarwa ne, sai kurum ya hau kankanbar rubutawa, musamman irin wanda ke taƙama da ilmin Boko, ba tare da la’akari da ƙa’idojin da masana harshen suka shimfiɗa ba.

Manyan ƴan bokon da suka fi yi wa rubutun na Hausa illa su ne ƴan jarida, musamman masu rubutun tallace-tallace.

Na ci karo da wani ƙaton Allon Talla a cikin birnin Kano an rubuta: “Mu na a Geyyara da Sayarawa.” Wai fa nufinsu “Muna gyara da sayarwa.” Wani allon kuma na ga an rubuta: “San u o zuwa.” Wai su na nufin: “Sannu da zuwa.”

Haƙiƙa wannan ta’addanci ne ake yi wa Harshen Hausa, maimakon a ɗauki ƙwararren mai fassara kamar yadda ake ɗauka a wasu yarukan, amma ganin ƙyashi da azarɓaɓi da rashin girmama ƙabilar ya sa ake amfani da fassarar da aka ga dama.

Na biyun masu ta’addaci ga rubutun Harshen Hausar, su ne masu Gidajen Rediyo da Talabijin, musamman masu karanta labaru cikin Turanci da Hausa.

Kasancewa ta mai sauraren labaran Gidajen Rediyon da ke birnin Kano, kwanaki cikin sanarwar da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta fitar game da binciken da ta gudanar a gidan tsohon mai ba wa Shugaban Ƙasa shawara ta fuskar tsaro, a labaran na Ingilishi sai suka ce: “…High calibre Rifles, several Magazines and Military related Gears were found…”

A labaran Hausar kuma sai suka ce: “An samu manyan makamai tare da Mujallar sojoji a gidansa.”

Gidan Rediyo na biyu kuma suka ce: “A gidan an samu wata Mujalla da ke koyar da aikin Sojoji tare da wasu manyan Bindigogi.”

Gidan Rediyo na uku kuma suka ce: “Tare da wata Mujalla Soja na koyar da yaƙi a cikinta.”

Gaba ɗaya fa sun kasa fahimtar cewa, kalmar ‘magazine’ da aka faɗa a sanarwar, ba ta na nufin Mujalla ba, ta na nufin Jigidar Albarusai, ko wani babban akwati mai ɗauke da Albarusai musamman na bindigar nan mai sarrafa kanta (Machine Gun).

Wannan ma babbar taɓargaza ce, kuma haƙiƙa ana cutar da Harshen Hausa bisa wannan mummunar fassara da ake yi cikin garaje.

Kuma ya zama kamar raina aikin manyan Farfesoshi ne da ke hidimtawa Harshen a kullum, ba Dare ba Rana.

Masu rubutu a zaurukan sada zumunci, musamman Facebook da WhatsApp da sauransu, su na gigita ƙa’idojin rubutun Hausa.

Nan ne za ka ga rubutu babu waƙafi balle Aya, babu fasali balle kama, babu fasaha balle ƙa’ida. Nan ne za ka ga rubutu daga sama zuwa ƙasa, ko daga ƙasa zuwa sama kamar na ƴan Ƙasar Sin (China).

Kuma wai su masu rubutun har buri suke a yi musu tsokaci, ko me za a ce da su? Oho! Ni kam ba na ko kallon rubutun nasu, domin ina gudun ka da kwamacalar da ke ciki ta sa ni amai.

Da a ce ina da iko, duk wanda na samu da irin wannan baragadar rubutun, sai na ci tararsa gwargwadon ɓarnar da ya aikata.

Makarantun Firamare da Sakandare, musamman masu zaman kansu, na taka muhimmiyar rawa wajen lalata rubutun Hausa.

Da yawa saboda tsumulmula ta rashin ɗaukar ƙwararrun malamai kamar yadda suke yi a wasu fannonin, sai su ɗauki Ngozi ko Chinyere ko Samuel a matsayin waɗanda za su koyar da Yaren Hausawa rubutun Hausa.

Wannan wata mahangurɓa ce da ba ta haifar da da mai ido. A ganina ma ita ce ummulhaba’isin faruwar taɓargazojin da na ambata a sama.

Don haka, ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su miƙe tsaye su ƙara azama wajen kare martabar rubutun Hausa. A sanya doka mai tsanani ga duk wanda aka ga ya na rubuta gurɓataccen rubutun Hausa a Allunan Talla, sannan a inganta hukumomin fassara ta yadda ba kowanne karabiti ne ke da lasisin fassara Hausa ba, sai wanda ya ke ƙwararre.

Ɗalibai kuwa, a ƙara himma wajen naƙaltar hawa da saukar rubutun Hausa, ko da ba ita ce abin da kake koyo a makaranta ba, za ta zame maka abin tinƙaho duk inda ka je a faɗin Duniya.

Ƙasashen da suka ci gaba dukansu da rubutun harshen ƙasarsu suke alfahari. Saboda haka ne ire-irenmu da ba Hausar muke karantawa a makaranta ba, amma saboda ita ce ta haife mu gaba da baya, ya sa muke nuna kishinmu game da ita.

Malamai kuma ya dace su ƙara nutsawa fagen bincike da ƙirƙiro sabbin hanyoyin nazari da samar da tabbatattun ƙa’idojin rubutu.

Ya kuma dace su shigo harkar zamani, musamman Intanet domin su kankare kura-kurai da gangancin da ake yi wa harshen Hausa.

Gwamnati kuwa da yake ita ce sha kundum, rubutun Hausa na buƙatar agaji ta hanyar ɗaukar nauyin malamai domin gudanar da bincike-bincike gami da ƙarfafa dokokin da suka jiɓinci rubutun Hausa tare da inganta hanyoyin koyon rubutun, ta yadda zai zama ya tafi asin-da-asin tare da harshen ta fuskar furuci.

Taskar Nasaba

Taskar Nasaba

About Author

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Adabi

Matakan Rubuta Ƙagaggun Labarai

Idan aka ce matakan rubuta ƙagaggun labarai, ana nufin hanyoyi ko dabaru ko wasu tubala ko kuma wasu abubuwa da