Daga: Salahuddeen Muhammad
Kaburan Waliyai da ɗimbin Littattafan tarihi a Timbuktu sun ɗaukaka sunan birnin da ke arewacin Ƙasar Mali.
Tombouctou ko kuma Timbuktu, birni ne a ƙasar Mali da ke cikin wurare masu daɗɗaɗen tarihi na Duniya, saboda haka ne ma a shekara ta 1988, Cibiyar kula da al’adu da kayan tarihi, ilimi da kimiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta jera shi a sahun wurare mafi tasiri na Duniya.
Daga Timbuktu zuwa Bamako babban birnin ƙasar Mali, akwai kimanin kilomita 1,000.

Tarihi ya nuna cewar, Abzinawa suka girka wannan gari a cikin ƙarni na 11, yanzu muna ƙarni na 21, ke nan Timbuktu ya samu ƙarni 10 da girkuwa.
Idan muka yi lissafi duk cikin ƙarni akwai shekaru 100, wato a taƙaice yanzu Timbuktu ya samu shekaru 2,000 ke nan da aka kafa shi.
Timbuktu, birni ne wadda masu ilimi suka ziyarta da daɗewa, tun farko-farkon shigowar addinin Musulunci a wannan yanki. Saboda haka, aka raɗawa garin suna “Birnin Waliyai 333.”
Wato a yanzu haka, akwai ƙaburbura na manyan mutane wadda suka ɗaukaka addinin Musulunci a yankin gaba ɗaya, wadda kuma da dama daga cikinsu suka yi wafati a Timbuktu.
Daga wannan ƙaburbura wadda mutane suka fi karramawa su ne; Kabarin Sidi Mahmoud, wadda ke Arewacin garin, sannan sai Kabarin Sidi Moukhtar, da Kabarin Alpha Moya, da kuma na Cheick el-Kabir.
Mutanen Ƙasar Mali da ma na ƙasashen ƙetare su na zuwa takanas domin su kai ziyara a wannnan kaburra, da ma wasu sauran daga cikin birnin Timbuktu, saboda haka ne ƙungiyar Ansar Dine wadda ta mamaye Arewacin Mali ta rusa wannan kaburra wadda ta ce, babu abin bautawa sai Allah, kuma ziyarce-ziyarcen da mutane ke yi a wannan ƙaburra ya saɓawa addinin Musulunci.
Daga jimlar ƙaburburan waliyan (333) da suka yi wafati a Timbuktu, akwai 16 wadda aka katange domin ƙara karrama su.
Bayan wannan kaburra na waliyai, Timbuktu na da wasu Masallatai guda uku masu dogon tarihi, akwai Masallacin Sidi Yahaya, wadda sarki Kanken Musa ya gina a shekarar 1325 AD, da Masallacin Djingareyber, wadda aka kammala ginawa a shekara ta 1328 AD, sai kuma Masallacin Sankore da wata mata ta gina a ƙarni na 11.



A Ɓangaren Rubuce-Rubuce, Garin Timbuktu Ya Yi Shura a Duniya

Timbuktu na da Littafai wadda masana suka rubuta tun lokacin da aka kafa garin, wasu kuma tun ma kafin Musulunci, ya bayyana a yankin.
Kafin Timbuktu ya faɗa hannun ƙungiyoyi masu tsatstsauran kishin addinin Islama akwai aƙalla Littattafai 18,000, wadda ke ajiye a wata cibiyar bincike mai suna ‘Institut de Hautes Etudes et de Recherches Islamiques Ahmed Baba.’

Shi Ahmad Baba, ya na ɗaya daga manyan marubuta na Bamako, wadda gwamnatin Mali ta kafa a shekarar 1973, Afirka ta Kudu ta bada babbar gudunmowa wajen sabunta ginin wannan Cibiya.
Afrika ta Kudu ta zuba tsabar kuɗin CFA Miliyan Dubu Biyu da rabi wajen gina cibiyar, sannan akwai wasu ƙarin dubbunan Littafai a cikin gidajen ɗaiɗaikun mutane, wadda suka gada iyaye da kakanni.

Mafi yawan daga wannan Littatafai an rubuta su da Larabci da Fillanci ko kuma da Hausa. Su na bayani game da Musulunci, kimiyya, al’adu, zamatankewar ɗan’Adamtaka, da dai sauran ɓangarori na ilimi.
Daga cikin wannan Littattafai akwai; Tarikh el-Fettah wadda Mahmud Kati ya rubuta, akwai kuma Tarikh es-Sudan wadda Abderrahmani es Saadi, ya rubuta a ƙarni na 17.

Duk wannan Littatafai sun shahara wajen tarihin Sudan, wato yankin ƙasashen da za a iya dangatawa yanzu kusan Afirka baƙar fata, mussamman yankin Afrika ta Yamma na yanzu.
Akwai Turawan Mulkin Mallaka da dama wadda suka ziyarci birnin Timbuktu, kuma suka yi mamaki game da tasirin wannan birni, mussamman ta ɓangaren rubuce-rubuce da kuma tsarin shugabanci, daga cikin wannan turawa akwai wani mai suna René Caillé, ɗanƙasar Faransa wadda ya je Timbuktu a shekarar 1828, bayan shi sai Heinrich Barth ɗanƙasar Jamus, wadda ya share watani shida a Timbuktu, daga 1853 zuwa 1854.
Waɗannan turawa su suka fara yaɗa tasirin Timbuktu a ƙasashen Turai. A lokacin, an samu masu ilimi da dama na Turai da suka nuna shakku ga bayanai da suka bayar game da Timbuktu.
Sai a shekarar 1894 da Turawan Mulkin Mallaka na Faransa suka kama garin, a lokacin suka tabbatar da sahihancin labaran sannan suka gasgata bayanan da suka samu daga Turawan farko da suka ziyarci Timbuktu.