Masana ilimin albarkatun ƙasa a Israila sun gano wani masallaci, da ake tunanin na ɗaya daga cikin masallatan da suka fi tsufa a Duniya.
Ƙaramin Masallaci ne da aka gina da duwatsun da aka yi a tun ƙarni na bakwai.
An gano masallacin ne yayin da ake aikin gina wani rukunin gidaje a birnin Rahat da ke kudancin Isra’ila.

Kazalika, alƙiblar masallacin ta karkata ne zuwa birni mai tsarki na Makka.

Masallacin kuma na da nisan kilomita biyu ne daga wani Masallacin irinsa, da ake tunanin an gina su ne lokaci guda, wadda aka gano a shekarar 2019.
