Ahmed Baba ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai na Afirka a karni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari‘a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane.
Ahmad Baba al-Massufi al-Timbuktu, cikakken suna; Abu al-Abbas Ahmad ibn Ahmad al-Takruri Al-Massufi al-Timbukti (Oktoba 26, 1556 – 1627), marubuci ne na Daular Songhai ta tsakiya, masani, kuma ɗan siyasa a yankin. sannan aka fi sa ni da Sudan ta Yamma.
A cikin rayuwarsa, ya rubuta Littattafai fiye da 40 kuma ana sanya shi a matsayin babban malamin Timbuktu.
Lokacin da Ahmed Baba Ya Rayu
An haifi Ahmed Baba a shekarar 1556. Wasu majiyoyi sun ce, a Araouane, kimanin kilomita 250 Arewa maso Yammacin Timbuktu, birnin da ke Arewacin Mali.
Akwai kuma yiwuwar an haife shi a Timbuktu lokacin birnin na bunƙasa a matsayin Cibiyar binciken addinin Islama da harkokin kasuwanci na yankin Sahara.
Baba ya yi karatu a birnin Timbuktu a wani Masallaci da ya yi suna. Bayan ya nuna adawa da mamaye birnin Timbuktu a shekarar 1591 da sarkin Maroko, Ahmed Al-Mansur ya yi, an tasa ƙeyar Baba zuwa Maroko.
Lokacin zamansa na shekaru 12, ya ci gaba da harkokin addinin Islama. Ahmed Baba ya koma birnin Timbuktu a shekarar 1608, in da ya rasu a shekarar 1627.
Abin da Aka San Ahmed Baba da Shi
Lokacin rayuwarsa an san shi da rubuta yarjeniyoyi na shar’ia da ke da dangantaka da addinin Islama ta hanyar rayuwar Musulmai da addininsu.
Yau sunan Ahmed Baba na da dangantaka da tunanin lokacin da birnin Timbuktu yake tsakiyar tashe.
Mene ne Tunanin Ahmed Baba?
Ahmed Baba ya yi ƙoƙarin ganin mutanen da suka fito daga ƙabilu daban-daban sun rayu da juna a birnin Timbuktu a lokacin. Ya na ganin ilimi zai kawo ƙarshen bambancin ƙabilanci.
Ƴan Maroko da suka kama Baba duk da sun yi masa ɗaurin talala, sun ɗauke shi a matsayin malami na gani na faɗa.
Ce-ce-ku-cen Da Ke Kewaye da Ahmed Baba
Game da batun bauta, Ahmed Baba ya rubuta cewa Musulmai ba za su zama bayi ba, ko daga ina suka fito bisa asalin mutum ko launin fata.
A lokacin bayi sun kasance rukuni mai muhimmanci na ciniki a birnin Timbuktu. Ya fahimci dokokin addinin Islama a lokacin ta hanyar da ake gani mai cike da gagarumin sauyi, saboda nuna duk masu imani a matsayin su na da matsayi guda a wajen Allah. Amma, Ahmed Baba bai yi tir da cinikin bayi ba, bisa rubutun, ya ce ya dace a yi cinikin bayi waɗanda da ba Musulmai ba.
A shekara ta 1615 Ahmad ya tattauna tare da sauran malaman musulmi kan batun bauta, domin kare Musulmi daga bautar da su.
Ahmad Baba ya yi ƙoƙari ya kawo ƙarshen bauta Saboda launin fata, kuma ya soki ƙungiyar masu bautar da Baƙar fata ta Afirka, musamman ya soki wasu Musulmai da su ka ɗauki labarin La’anar Ham, da ke cikin littafin Farawa.
Duk da haka, Ahmad Baba ba mai ba da shawara ba ne don kawo karshen cinikin bayi gabaɗaya ba. Maimakon haka, a cikin rubuta Mi’raj al Su’ud ila nayl hukm mujallab al-Sud, ya yi ƙoƙari ne kawai don gyara kasuwancin bayi a yankin Sahara da nufin hana musulmi bautar da sauran Musulmi.
A cewar William Phillips, al-Timbukti da gaske ya bayar da shawarar bautar da ta dogara da nassosin addini maimakon bautar kabilanci, in da musulmi a kowace ƙabila ke da kariya daga bautar da su.
Wane Abu ne Ya Janyo Ake Ƙaunar Baba Har Yanzu?
Ahmed Baba ya shahara saboda sanin da yake da shi da kuma basira, ya nuna bajinta kan adawa da mamaya daga Maroko waɗanda suka kame garinsa na Timbuktu.
Wane Abu Ahmed Baba Ya Bari?
Babbar makarantar koyar da addinin Islama da bincike da ke birnin Timbuktu, ta na ɗauke da rubuce-rubuce kimanin 30,000 kuma na zama daya daga cikin matattara mafi muhimmanci ta Islama da ke ƙunshe da Littattafai da kayayyakin tahirin wadda aka saka sunan Ahmed Baba sannan wani ɓangare na Duniyar Mercury. An ɗauki Ahmed Baba a matsayin gwarzo a Ƙasar Mali yanzu haka.
Madogara
Shawarwari a kan wannan maƙala sun samu ne daga Farfesa Doulaye Konaté, da Dr. Lily Mafela da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo.