Harkar yawon shaƙatawa ta kasance ɗaya daga cikin ginshiƙan tattalin arzikin ƙasar, wadda ta ɗauki kimanin kaso 12% na adadin GDP na ƙasar, tare da samar da guraben aikin yi ga al’ummar ƙasar kimanin miliyan uku.

Alƙaluman da ma’aikatar kula da harkokin yawon shaƙatawa da kayayyakin tarihi ta ƙasar ta fitar a kwanan bayan nan sun shaida cewa, a shekarar da ta gabata (2023), masu yawon shaƙatawa kimanin miliyan 14.9 ne suka ziyarci ƙasar.


Har ila yau, wannan sabuwar ƙididdiga ta karya tarihin masu ziyara miliyan 14.7 da aka yi rajista a shekarar 2010.

📷 Egypt Tours Plus