Turmin Tsakar Gida

Tarrare: Mutumin Da Ya Kasa Daina Cin Abinci, Saboda Ba Ya Ƙoshi

A ƙarshen shekarun 1700s, akwai wani mutum a ƙasar Faransa wanda ke fama da yunwa marar iyaka kuma ya kasa daina cin abinci, amma duk da haka ba shi da yawan ƙiba.

Daga: Salahuddeen Muhammad

Ya na cin Tsuntsaye irinsu Hankaka har da dabbobi masu rai, da mushe da ƴantayi. Haka nan, ya na cin Nama mai yawa.

Ya zagaya Faransa tare da ƙungiyar karuwai da ɓarayi kafin ya zama mai yawace-yawace don yin wasan kwaikwayo. A cikin wannan aikin, ya na haɗiye Kwalabe, Duwatsu, Dabbobi masu rai, da kwandon Tuffa.

Daga nan sai ya koma zuwa birnin Paris inda ya ci gaba a matsayin mai wasan kwaikwayo.

Ba a san ainihin ranar haihuwarsa ba, amma an san shi da suna Tarrare, kamar yadda ake kiransa, an haife shi ne a birnin Lyon, na Ƙasar Faransa, a shekara ta 1772. Ko da ya na Yaro, cin abincinsa ya yi yawa wanda har ya janyo iyayensa suka kore shi a lokacin da yake da shekaru 17, don ba za su iya ciyar da shi ba.

Sunansa ya fito daga wani furucin harshen Faransanci, “Bom-bom-tarrare.”

Shiga Aikin Soja

Tarrare, ya shiga cikin sojojin a lokacin juyin juya hali na Faransa, inda aka ninka masa abinci ninki huɗu fiye da na sauran yan’uwansa sojoji, amma duk da haka abincin ya kasa gamsar da shi. Daga nan ya koma cin duk wani Abinci da Ruwa ya koro a magudanar ruwa da tarkacen shara amma duk da haka ba ya ƙoshi.

An kwantar da shi a asibiti sakamakon kasala, inda aka yi masa gwaje-gwajen Likitanci domin auna yawan cin abincinsa, inda aka gano ya na iya cin abincin da aka tanadar wa mutane 15 a zama guda, ya na cin Kyanwa, Maciji, Ƙadangaru.

Idan ya na wasan kwikwiyo, ya na haɗiye Goro ba tare da ya tauna ba. Duk da irin abincin da ya saba ci ba shi da ƙiba kuma, ba ya nuna alamun taɓin hankali.

Janar Alexandre de Beauharnais ya yanke shawarar barinsa a Aikin Soja, kuma ya ɗauke shi aiki a matsayin masinja ga Sojojin Faransa. A farkon aikinsa, Sojojin Prussian sun kama shi, sun yi masa mummunan rauni, kafin a mayar da shi zuwa Faransa.

An kai shi Asibiti, a Asibitin Likitoci sun kasa sarrafa yadda yake cin abinci; Daga baya ya fice daga asibitin ne domin neman abinci a cikin magudanar ruwa, da tulin shara da shagunan mahauta, ya kuma yi yunƙurin shan jinin wasu majinyata a asibitin a lokacin da suke zubar da jini, da cin gawarwakin da ke ɗakin ajiye a ɗakin Gawa na asibitin. Bayan da ake zarginsa da cinye Gawar wani yaro ɗan shekara ɗaya, an kore shi daga asibiti.

Bayan an tilasta masa ficewa daga Aikin Soja, ba a sake jin ɗuriyarsa ba, sai bayan shekaru huɗu a Versailles a lokacin da ya kamu da cutar Tarin Fuka mai tsanani kuma ya mutu ba da jimawa ba, bayan wani dogon lokaci ya na zawo.

Bayanin kula: Hoton da yake bisa ba hotonsa bane, zane ne. Labarin Gaskiya ne ba Almara ba.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Turmin Tsakar Gida

Musaboni Hosono: Ɗanƙasar Japan Guda Ɗaya Tal da ya Tsira Daga Haɗarin Jirgirn Ruwan Titanic

Wanann shi ne Musaboni Hosono. Ɗan asalin Ƙasar Japan guda ɗaya tal da ya tsira daga haɗarin Jirgirn Ruwan Titanic
Turmin Tsakar Gida

Babbar Magana! An Naɗa Akuya a Matsayin Shugaban Gari

Wata al’umma a ƙauyen Nabankaha na Cote d’Ivoire, ta naɗa Akuya a matsayin shugaban garin. Bugu da ƙari, shi ne