Jiya Da Yau

Gimbiya Yennenga: Kakar Al’ummar Mossi na Burkina Faso

Daga: Richard Tiéné (ATB/MNA)

Gimbiya Yennenga, ta kasance jaruma a fagen yaƙi kuma ƙwararriya wajen hawa Doki. Ta bar tarihi mai ɗorewa a Burkina Faso.

Yaushe Aka Haifi Gimbiya Yennenga?

Masana tarihi ba su cimma daidaito ba a game da haƙiƙanin ranar da aka haifi Gimbiya Yennenga, sai dai da dama sun yi imani da cewa, an haife ta ne a tsakanin ƙarni na 11 zuwa ƙarni na 15.

Ita ce ƴar gaban goshi ta Sarki Naba Nedega. Ya yi mulkin Masarautar Dagomba wadda a yanzu take cikin Ƙasar Ghana

Mene ne Abu na Musamman Game da Gimbiya Yennenga?

A tarihi na baka, Gimbiyar ta fi son Doki fiye da sauran dabbobi tun ta na yarinya. Bayan shafe tsawon lokaci sau da dama ta na yunƙuri, Yennega ta sami shawo kan mahaifinta ya ƙyale ta, ta hau Doki.

Wannan wata dama ce da aka keɓe wa Maza kawai a Masarautar. Gimbiyar ta nuna cewa, ba ma kawai ta na da hazaƙa wajen hawa Doki bane kaɗai, jaruma ce a fagen yaƙi.

Ta haifi ɗanta ne sakamakon soyayya da ta ƙullu tsakaninta da wani maharbi a daji.

Sun raɗa wa ɗan suna Ouedraogo (stallion) domin karrama wannan Doki da ya yi sanadiyyar haɗuwarsu.

Ƙabilar Ouedraogo su ne kakannin al’ummar Mossi, ƙabila mafi girma a Burkina Faso.

Sarƙaƙiya a Game da Labarinta

Yanayin da Yennenga ta ɓace a daji ya kasance tamkar al’mara, an riƙa bada labarai masu karo da juna. Labari mafi shahara shi ne cewa, Gimbiyar ta gudu ta bar ƙauyensu domin guje wa mahaifinta wanda ya ƙi yarda ƴar da yake so ta yi Aure.

A game da asalin masoyinta kuwa, wasu majiyoyi sun ce Maharbi ne daga Ƙasar Mali. Wannan bayani shi ne dalilin da ya sa al’ummar Mossi suke da tushe daga Mali.

Wani Tarihi ta Bari a Baya?

A cikin mawaƙa ƴan Burkina waɗanda suka yi mubaya’a ga Gimbiyar har da Yili Nooma. A gare ta, Yennenga Mace ce jajirtacciya kuma wace ba ta da tsoro. jarumar yaƙi wadda a cikin mata ake so a yi koyi da ita. Sanya sunan Gimbiyar a faifan waƙarta ta farko, wata hanya ce ta nuna cewa, a yau su ne Yennenga a wannan zamani.

An ci gaba da raya tarihin Yennenga ta hanyar “Dokin Zinare na Yennenga” wanda ake bayarwa ga zakarun da suka lashe gasar Fina-finai ta FESPACO da ake gudanarwa duk bayan shekaru biyu.

A yanzu haka ma, ana gina wani sabon birni da aka sanya wa suna Yennenga da kuma ASFA Yennenga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ajin farko na gasar Lig ta Ƙasa. Haka ma, sunan ‘stallion’ da aka raɗa wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa a Burkina Faso, karramawa ce aka yi ga dokin da Gimbiyar ta fi ƙauna.

Madogara

Shawarwari a kan wannan maƙala sun samu ne daga Farfesa Doulaye Konaté, da Dr. Lily Mafela da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Jiya Da Yau

Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, wadda ya rubuta fiye da Littattafai 400 na addinin Musulunci. Malamin, wadda jigo ne
Jiya Da Yau

Taytu Betul: Shahararriyar Sarauniyar Sarakuna

Taytu Betul ta kasance sarauniyar Habasha daga 1889 zuwa 1913 kuma matar sarki Menelik na biyu. Jarumi mai tasiri wajen