Yaƙi Tsakanin Ƙasar Ingila da Faransa 1337 zuwa 1453, Shekaru 166 ana Gwabzawa.
Daga: Salahuddeen Muhammad
Yaƙin shekaru 100 ya kasance doguwar gwagwarmaya tsakanin Ingila da Faransa a kan gadon sarautar Faransa.
Ya kasance daga 1337 zuwa 1453, don haka ana iya kiran shi da “Yaƙin shekaru 116yrs.”
Yaƙin ya fara ne da nasarori masu ban mamaki da dama daga ɓangaren Birtaniya, kuma sojojin Ingila sun mamaye Faransa tsawon shekaru da dama.
Yaƙin dai da aka yi shekaru ɗaruruwa ana yi, shi ne yaƙin da aka ɗauki tsawon lokaci ana yi ana tsagaitawa tsakanin Ƙasar Ingila da Ƙasar Faransa, tun daga shekarar 1337 zuwa 1453, wato a taƙaice an shafe kusan shekaru 116 ana fafatawa.
Sun shiga rikici ne kan batutuwa da dama, ciki har da taƙaddama kan mallakar yankin Ingilishi a Faransa da kuma halarcin gadon sarautar Faransa.
Yaƙin Agincourt, (Oktoba 25, 1415), ƙaƙƙarfan yaƙi a cikin yaƙin shekaru Ɗari 1337 zuwa 1453 wadda ya haifar da nasarar Ingilishi a kan Faransawa. Sojojin Ingila, ƙarƙashin jagorancin Sarki Henry V, sun yi fice wajen samun nasara duk kuwa da fifikon adadi na abokin hamayyarsu.
An fara wannan yaƙi ne a lokacin da sarkin ingila wadda ake kira da suna Sarki Edward na uku, ya ƙalubalanci gadon sarautar Faransa, kuma ya mamaye yankin Arewa maso Yamma na Ƙasar ta Faransa.
Sarkin da ya gaji Sarki Edward shi ne Sarki Richard na biyu, shi ma ya ci gaba da wannan yaƙi, haka zalika Sarki Henry na huɗu wadda ya tumɓuke Richard daga Sarauta, shi ma ya ci gaba da gwabza yaƙi da Faransawa.
Sarki Henry na biyar shi ne wadda ya zama Sarkin Ingila bayan Sarki Henry na huɗu, shi ne kuma wadda ya ci Faransawa da yaƙi a yaƙin da ake kira da suna “Agincourt’’ in da ya naɗa muƙaddashinsa a ƙasar ta Faransa.
Bayan shekaru da dama, Sarkin Faransa wato Charles na biyar, ya dawo da yaƙi sabo, in da ya koma yaƙar Ingila tare da taimakon ƙasar Scotland, kuma ƙasar ta Faransa daga baya ta samu nasarar yaƙe-yaƙe da dama musamman ma a shekarar 1429, amma dai ba a samu wata cikakkiyar nasara ba sai a shekarar 1436, lokacin da Faransawa suka ƴanto birnin Paris daga ƙarƙashin mulkin Ingila, sannan kuma a shekarar 1453, Faransa ta kori Ingila kwata-kwata daga yankinta.
Yaƙi na biyu da yake rufawa yaƙin Ingila da Faransa baya, shi ne yaƙin Lardin Aceh, ko da yake dai akwai ƴar tababa daga ɓangaren masana tarihi game da tsayin da ake cewa, yaƙin na lardin Aceh ya yi, wato tsakanin al’ummar Aceh na ƙasar Indonesia da kuma al’ummar ƙasar Holland.
Da farko dai, Netherlands ce ta ƙaddamar da yaƙi a kan al’ummar lardin Aceh, a shekara ta 1873, to daga nan ne fa yaƙi ya ci gaba ya na yi ya na lafawa na tsawon shekaru da dama.
Wasu masana tarihi sun ce, yaƙi ya ƙare ne a shekarar 1903, amma dai a hukumance al’ummar ƙasar Netherlands ba su kwashe ya-nasu ya-nasu ba har sai a shekarar 1942. Saboda haka, za a iya cewa yaƙin lardin Aceh ya ɗauki tsawon shekaru 30 ko kuma 69.
To idan muka komo yaƙe-yaƙen da suka faru a ƙarni na Ashirin, babu wani mutum da zai iya cewa ga yaƙin da ya fi tsawo, domin kuwa waɗansu har yanzu ana nan ana ci gaba da su.
Misali yaƙin da ake yi tsakani Yahudawa da Palasɗinawa, yaƙi ne da ya samo asali tun a shekarar 1946, wato bayan yaƙin Duniya na biyu, lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tsaga yankin Palasɗinu, in da aka bai wa Yahudawa kashi 55% da bisa 100 na Palasɗinu, su kuma Palasɗinawa aka ba su kashi 45% bisa 100, saboda haka, sai suka ce ba su yarda ba. To daga nan ne fa yaƙi ya fara har ya zuwa yau, kusan kimanin shekaru 75 ke nan ana cikin wannan hali.
Akwai kuma rikicin ƙasar Sudan na yaƙin basasa wadda aka fara tun a shekarar 1955, in da yanzu haka an ɗauki kusan shekaru 51 ana wannan gumurzu.
Haka zalika ita ma ƙasar Guatemala ta faɗa gararin yaƙin basasa wadda ya ɗauki kusan shekaru 36 tun daga shekarar 1960 zuwa 1996.
Kai! Babu ko shakka, abin baƙin ciki ne idan aka dubi yadda tarihin Duniya ya cika da yaƙe-yaƙe masu tsawo, domin kuwa ba ya ga waɗanda muka bayyana a baya, har ila yau akwai yaƙoƙi irin su yaƙin nan na ƙasar Girka (Greece) mai tarihi wadda ya ɗauki shekaru 27, da kuma yaƙin Vietnam wadda aka yi shekaru 18 ana yi.
Ban da kuma rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinye wa fiye da shekaru 33 a yankin Northern Ireland.
Waɗannan yaƙe-yaƙe dukkaninsu, yaƙe-yaƙe ne masu tsawo ƙwarai da gaske.