Daga Muhammad Cisse
Masana juyin halitta, sun yarda da cewa, halittun ruwa sun rikiɗe sun koma halittun da ke tafiya a doron ƙasa tun shekaru Miliyan 500 da suka gabata, zamanin da ake kira da suna; Zamanin Cambrian a turance.
A cewarsu wannan wani zamani ne da babu wasu halittu daga Duwatsu sai halittun da ke cikin ruwa, ma’ana; Halittu a wancan lokacin sun fara wanzuwa ne a siffar Kifi.
To, amma gaskiyar batu shi ne cewar, kamar yadda ya kasance halittu a Zamanin Cambrian ba su da magabata, haka ma babu wata alaƙa da take nuna rikiɗarsu, lokaci bayan lokaci, tsakanin halittun ƙasa da Kifi. Ya na da kyau a fahimta cewa, babu wasu siffofi da suka dangantasu.
Dabbobi masu ƙafafuwa su na da tsarin halittar jiki, haka Kifi ya na da nasa. In da ace wannan da’awa ta rikiɗar halittun ruwa zuwa halittun doron ƙasa gaskiya ce, ya kamata a ce “Juyin halitta” ya ɗauki Biliyoyin matakai wanda zai cika, kuma ya kamata a ga Biliyoyin tsaka-tsakin halittun da ke nuna haka.
Masanan sun yi shekaru 140 su na yin haka, don tono ɓurɓushin halittar da ke nuna waɗannan ƙa’ida tasu. Sun gano Miliyoyin ƙasusuwan ɓurɓushin halittun ƙasa da Kifaye; amma har yanzu ba su samu ko ɗaya da yake nuna tsaka-tsakin halitta ba, (wato wata halitta da za ta kasance rabi kifi, rabi dabba) har yau ba su samo hakan ba.
Masanin binciken ɓurɓushin halittu, Gerald T. Todd ya amsa wannan batu a cikin littafinsa mai taken “Evolution of the Lung and the origin of Bony fishes.”
Masana ilimin juyin halitta, sun bayar da misalan Kifaye guda uku, a lokacin da halittar Kifin take ƙoƙarin rikiɗa zuwa halittar da ke taka doron ƙasa. To, amma dukkanin ɓangarori uku na Kifaye da aka samu a daftarin ɓurɓushin halittu, sun bayyana a kusan lokaci ɗaya. Sun sha bamban ta kowace fuska, kuma ga shi su na da girman jiki.
Ta ina suka fara wanzuwa, kuma ta ƙaƙa suka samo manyan gaɓɓai, kuma mene ne ya sa ba a gano asalinsu, ko tsaka-tsakin siffarsu ba?
Tatsuniyar juyin halitta ta na da’awar cewa dai; Kifi ya faro ne daga ƙwaro mai ƙasusuwa izuwa Dabba mai ƙafafuwa. Amma babu gamsashshiyar hujja akan haka. Babu ma ko da ɓurɓushin halittar da ta taɓa wanzuwa.
Dangane da halittar da ka iya kasancewa tsaka-tsaki, wato rabi Kifi rabin Dabba, kafin ta zama dabba gaba daya? To, a nan ma dai, masana ilimin juyin halitta ba su da ta cewa, domin sun ba da kai bori ya hau.
Wani shahararren masanin juyin halitta mai faɗa aji, Robert L. Carrol, ya gasgata batun cewa, ba su da wannan amsa, kuma Mawallafin Littafin ‘Vertebrate Paleontology and Evolution,’ inda yake cewa: “Ba mu da tsaka-tsakin ɓurɓushin halitta tsakanin magabacin Kifi da kuma farkon halittar Dabba mai ƙafafuwa.”
Babu wata hujja a kan ɗaya daga halittun Ruwa waɗanda za a yi zatonsu a wata magabaciyar halitta guda.
Ko da dai akwai wani nau’i na Kifi da ake kira ‘Coelacanth,’ wanda bayan kimanin shekaru Hamsin da suka shuɗe ne, masanan suka yi zaton cewa wannan halitta ta wanzu.
Wannan Kifi da ake kira ‘Coelacanth,’ wanda aka yi ƙiyasin shekarunsa miliyan 410, an gabatar da ɓurɓushinsa a matsayin tsaka-tsakin sifa da ke ɗauke da ƙasusuwa irin na da, da ƙwaƙwalwa irin ta yanzu, da kuma kayan hanji da jijiyoyi wanda za su iya aiki a ban-ƙasa, har da kuma gaɓoɓin da ka iya taimakawa wajen yin tafiya.
Waɗannan bayanai sun samu karɓuwa a matsayin wata hujja wadda ba za a iya juyar da ita ba a tsakanin masana kimiyya, har izuwa shekera ta 1930.
An gabatar da Kifi ‘Coelacanth’ a matsayin tsaka-tsakin sifa ta gaskiya wadda ta tabbatar da hujjar rikiɗar halittun ruwa zuwa halittun doron ƙasa.
To amma, bayan shekaru 8 da samuwar waccan hujjar, a ranar 22 ga watan Disamba, 1938, bincike mai ban sha’awa ya gano dangin Kifi Coelacanth a Tekun Indiya, wanda da, aka gabatar da shi a matsayin tsaka-tsakin sifa waɗanda suka gushe shekaru Miliyan 70 da suka shuɗe. Gano rayayyiyar wannan halitta da aka yi ya jefa masana cikin damuwa, cike da mamaki.
Masanin ɓurɓushin halitta J.L.B. Smith ya ce, ba zai zama ya yi mamaki ba idan da zai ga rayayyen halittar Dinosaur. A shekarun da suka gabata, an kama Kifi Coelacanth guda 200 a wurare daban-daban a faɗin Duniya.
Rayayyun Coelacanth sun nuna ƙarara irin nisan Dam a sama juyin halitta suka yi wajen ƙirƙirar tatsuniyoyinsu, saɓanin da’awarsu. Coelacanth ta tabbata ba shi da Huhun da ballantana babbar Ƙwaƙwalwa. Gaɓar da masanan suka gabatar a matsayin huhun da, an gano cewar ba komai bane illa ƙunzumin yawu ne. bayan haka, an gabatar da Coelacanth ne a matsayin ”Dabba mai ƙoƙarin yin rarrafe ta fito daga ruwa zuwa ban ƙasa,” a haƙiƙani kuwa Kifi ne da ke zaune can ƙarƙashin Teku kuma bai taɓa saman ruwa da aƙalla mita 180 ba.
Dalilan da suka sa, masa ilimin Kimiyya na wannan zamani (waɗanda ba sa tare da ƙa’idar juyin halitta) suka bayar, game da dalilan da suka sa rikiɗar halittun ruwa zuwa halittun doron ƙasa ba za ta yi wu ba, su ne;
- Nauyin jikinsu: Halittun da ke rayuwa a cikin ruwa ba su da matsalar ɗaukar nauyin jikinsu. Haka kuma, halittun da ke rayuwa a ban-ƙasa yawancinsu su na ɗaukar kashi (40%) arba’in cikin dari na kuzarin da ka iya ɗaukar jikin nasu zuwa ko’ina, saboda haka ka ga halittun da ke neman rikiɗa zuwa ƙasa sai sun samo sababbin gaɓoɓi da ƙasusuwan da za su iya ɗaukar nauyin kuzarin da zai sa rayuwarsu ta daidaita, wanda kuma mawuyaci ne maye gurbi da ke tattare da asu ya samar da hakan.
- Jure zafi: a ƙasa, hucin Zafi ko Sanyi na saurin canjawa da bazuwa mai faɗi. Halittun ƙasa na ɗauke da ƙwayoyi a jikinsu da za su iya jure ƙarfin yanayin. haka kuma, a ruwa, hucin Zafi ko Sanyi ba ya saurin canjawa kuma ba ya faɗaɗa. Saboda haka, halittar da ke rayuwar a irin wannan yanayi na cikin ruwa su na buƙatar sinadarai na kariya daga yanayin da ke canjawa a ban-ƙasa, dai-dai gwargwado. Abu ne da ya saɓa wa hankali a yi da’awar Kifi na ɗauke da waɗannan sinadarai ta hanyar bazuwar maye gurbi a yayin da suka hau doron-ƙasa.
- Amfani da ruwa: Ruwa har da jiƙaƙƙiyar iska abubuwa ne da halittun da ke rayuwa a doron-ƙasa, suke amfani da su da riritawa saboda ƙarancin hanyar samun ruwa akan ƙasa. Misali, sai an halicci fata yadda za ta riƙa fitar da ruwa zuwa wani miƙidari tare da kiyayewa daga fitarsa. Saboda haka, halittun ƙasa za su samu gaɓar jin ƙishirwa, wadda halittun ruwa ba su da ita. Bayan haka, fitar jikin dabbobin ruwa ba daidai yake da dabbobin da ba a ruwa suke ba.
- Ƙoda: Halittun Ruwa na da sassauƙar hanyar fitar da datti daga jikinsu, musamman sinadarin ‘Ammonia,’ ta hanyar tace su tun da mazauninsu cike yake da ruwa. A ƙasa kuwa, sai an taƙaita amfani da ruwa. Wannan shi ne ya sa waɗannan halittu suke da tsarin Ƙoda. Madalla, da samuwar Ƙoda, sinadarin ‘Ammonia’ na taruwa ne a nan kuma ya canja zuwa sinadarin ‘Urea’ (fitsari) da kuma ƙarancin ruwan da take amfani da shi yayin fitarwa. ƙari a kan haka, ana buƙatar sababbin gaɓɓan da za su samar wa da Ƙoda ta riƙa aiki sosai. A taƙaice, idan a nan son rikiɗar Halittar Ruwa zuwa ta ƙasa ta yi wu daidai da minti guda a wajen ruwa ba. Idan ana son rayuwarsu a ban-ƙasa, to sai sun samu kyakkywan Huhu, shi ma a gan shi kwatsam!
Saboda haka, abu ne mawuyaci a ce dukkan waɗannan canje-canje za su afku a tsarin halittarsu a lokaci guda kuma kwatsam!
Magana ta ƙarshe dai ita ce, dukkanin wata halitta da ke faɗin Duniya da abin da yake cikinta, Allah mahaliccin kowa da komai ne Ya halicce ta, shi ne kuma yake da iko akan komai, idan Ya yi nufin halittar wani abu, sai ya ce da shi kasance, kuma ya kasance.
Abdullahi Malumfashi
04/12/2024Gaskiya an zalunci jama’a