Al'ada

Yadda Bikin Bajekolin Fasahohin Ghana Ya Haskaka Yankin Volta

Bikin na kwanaki uku ya nuna al’adun gargajiyar Ghana kana ɓude taron bikin ne daga gaɓar tekun garin Keta, ɗaya daga cikin wuraren yawon buɗe ido a yankin Volta.

An gudanar da bikin bajekolin fasahohi na Ghana wanda ke mai da hankali kan bikin fasahar zane-zane da al’adu da kuma yawon buɗe ido a kwanan nan a yankin Volta na ƙasar.

Bikin na kwanaki uku, wanda aka gudanar daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Nuwamba, an soma shi ne a ranar Juma’a da jawaban ilimantarwa ga ɗaliban fasahar zane-zane na garin Keta da Alonga – manyan wuraren yawon buɗe ido biyu da ke yankin Voita a ƙasar.

Bikin fasahohi na Tsadidi, wanda a yanzu ya kai shekaru uku da aka soma, ya na nufin yawon shaƙatawa a harshen Ewe. Glenn Samm, wani mai ba da labari ta hanyar zane-zane kana mai tallan ƙawa ne ya ƙirkire bikin.

Kimanin masu yawon buɗe ido miliyan 1.1 ne suka ziyarci Ghana a shekarar 2023, a cewar wata kiɗiddiga da aka fitar.

Taken bikin Tsadidi na bana a shekarar 2024 shi ne, “Gwajin Al’adu,” inda aka bajekolin kayayyakin tarihi na yankin Volta.

An baje kayayyaki da tufafin gargajiya da zane-zanen fasahohi akan hanyoyi da dai sauran wasannin al’adu a muzaharar da aka yi. / Hoto: Glenn Samm

Wasannin Al’adu

An ƙarkare bikin na ranar Juma’a ne da zaman shan ɗumin wuta da ba da tatsuniya, sannan aka ɗora da tattakin fasahar zagaye garin Keta a ranar Asabar.

An baje kayayyaki da tufafin gargajiya da zane-zanen fasahohi a kan hanyoyi da dai sauran wasannin al’adu a muzaharar da aka yi.

Bikin ƙarshe da aka gudanar a ranar Lahadi, an yi ciye-ciye a bakin teku inda aka baza abincin gargajiya iri daban-daban tare da kiɗe-ƙiɗe na gargajiya.

Manufar bikin ita ce; A gudanar da shirye-shiryen nishaɗi iri daban-daban tare da mai da hankali kan fasaha. Hoto: Glenn Samm

Ayyukan Nishaɗi

“Biki ya na haɗa mutane wuri ɗaya da kuma masu ba da tallafi zuwa bikin bisa ga mabambantan dalilai, ciki har da shaida irin al’adun gargajiya da ake da su,” kamar yadda Glemn Samm ya bayyana a wata hira da kafar Grapic Showbiz ya yi da shi.

“Kamar dai yadda aka saba, bikin bajekolin fasahar Tsadidi ya na ƙirkirar ayyukan nishaɗi ga mahalarta kana a wannan karon da aka gudanar da bikin an samar da shirye-shiryen nishaɗi daban-daban, inda aka fi mai da hankali kan fasahohi,” in ji shi.

Glenn Samm, wanda ainihin sunansa shi ne Samuel Glenn Semakor, ya lashe lambar yabo ta ‘Fashion Influencer’ na shekara na shirin Pulse Influencer a shekarar 2022.

Salahuddeen Muhammad

Salahuddeen Muhammad

About Author

Ɗanjarida, marubuci, mai manufar bunƙasa harshen Hausa da al'adar da ba ta yi karan-tsaye a addini ba.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai Masu Nasaba

Al'ada

Bikin Guérewol na Ƙabilar Wodaabe a Jamhuriyar Nijar

Bikin Guérewol wata gasa ce ta al’adar neman aure da ake yi a kowace shekara tsakanin al’ummar Wodaabe Fula na
Al'ada

Shin Kayan Lefe Kyakkyawa ko Mummunar Al’ada Ce?

Abdulmutallib A. Abubakar malami a sashen nazarin aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri da ke jihar Barno kuma mai sharhi kan